Yadda sabon filin wasan Santiago ya zama matsala ga Real Madrid
Real Madrid ta sake fasalin filin wasanta na Santiago Bernabeu mai dimbim tarihi, sai dai hakan na neman zame mata matsala,
Sabon filin wasan Santiago Bernabéu yana nema ya zame wa kulob din Real Madrid ƙarfen ƙafa.
Real Madrid ta sake fasalin filin wasanta na Santiago Bernabeu mai dimbim tarihi, sai dai hakan na neman zame mata matsala, sakamakon yadda mazauna unguwar da filin wasan yake suke ta zanga-zanga a kan irin surutan da ke fitowa daga filin wasan, musamman na bukukuwan kade-kade da raye-raye da wasu aikace-aikace da ake ci gaba da yi a filin.
Yanzu an fara daukar hayar filin ana yin tarukan raye-raye da kade-kade daga farkon shekarar nan, bayan da aka kammala aikin zamanantar da filin wasan, inda aka saka masa rufi wanda ake iya janyewa da sababbin fitulu masu haske da ma dandalin filin wasan da ake iya janyewa dungurumgum, ya koma tamkar babu komai.
Maƙasudin haka shi ne a mayar da filin, wanda aka ƙaddamar a shekarar 1947 a matsayin filin ƙwallo, ya koma filin gudanar da sabgogin nishadi daga farko zuwa ƙarshen shekara.
Tuni manyan mawaƙa suka fara baje fasaharsu a filin. Sai dai mazauna kusa da filin har fara ƙorarafi a kan wadanda suke sabgogin a Santiago Bernabeu.