Yadda sabon tsarin Gasar Zakarun Turai zai kasance daga baɗi

Ƙungiyoyi 36 ne za su shiga gasar a matsayin lig guda ɗaya.

Yadda sabon tsarin Gasar Zakarun Turai zai kasance daga baɗi

Shugaban UEFA; Alexander Ceferin

A ranar Litinin da ta gabata ce Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai, UEFA ta sanar da sabon tsarin da Gasar Kofin zakarun Turai za ta koma kai daga kakar wasa mai zuwa.

Muhimmin sauyin da dukkan masu ruwa da tsaki suka aminta da shi a cewar shugaban UEFA, Aleksander Čeferin shi ne ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi yanzu.

A halin yanzu matakin rukuni na gasar Zakarun Turai ya ƙunshi ƙungiyoyi 32 da aka raba cikin rukunnai takwas, inda kowanne rukuni ke kunshe da ƙungiyoyi huɗu.

Daga kakar wasa ta 2024/25, kungiyoyi 36 ne za su shiga Gasar Kofin Zakarun Turai (tsohon matakin rukuni), wanda zai ba wa wasu kungiyoyi huɗu damar fafatawa da kungiyoyin da suka fi fice a Turai.

Ƙungiyoyi 36 ne za su shiga gasar a matsayin lig guda ɗaya wadda dukkanin kungiyoyin za su kasance a teburi ɗaya.

A ƙarkashin sabon tsarin, ƙungiyoyi za su buga wasanni takwas a sabon matakin gasar (tsohon matakin rukuni). Za su fafata da ƙungiyoyi daban-daban guda takwas, inda za su buga rabin waɗannan wasannin a gida, rabinsu kuma a waje.

Domin tantance ƙungiyoyin da za su fafata da juna, da farko za a sanya kungiyoyin a cikin tukwane guda huɗu.

Sannan za a fitar da kowace kungiya domin ta yi wasa da abokan hamayya biyu daga kowacce tukunya, inda za a yi wasa ɗaya da kungiya daga kowace tukunya a gida, daya kuma a waje.

Kungiyoyi takwas na farko a teburin za su tsallaka zuwa zagaye na 16 kai tsaye, yayin da kungiyoyin da suka kare a matsayi na 9 zuwa na 24 za su fafata a cike gurbi don samun damar ketarawa zuwa zagaye na ƴan 16 na karshe a gasar.

Ƙungiyoyin da suka kare a matsayi na 25 zuwa kasa za a fitar da su, ba tare da samun damar shiga gasar Europa League ba.