Yadda sabuwar waƙar Rarara ta tayar da ƙura
Mutane da dama sun fusata game da waƙar da Rarara ya saki.
Fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu Rarara, ya sake tayar da ƙura, bayan ya fitar da wata sabuwar waƙarsa a kan tsadar rayuwa da Gwamnatin Tinubu, inda a ciki ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙari.
Hakan ya fusata matasa, inda suka fara kai ƙarar shafinsa na Facebook, wanda wasu suka bayyana cewa an rufe shafin ne saboda fustar matasan.
- Dalilin da ba zan tsoma baki kan rikicin Masarautar Kano ba — Shekarau
- Hotunan yadda aka gudanar da addu’o’i kan matsin rayuwa a Kano
Aminiya ta duba shafin, inda ta lura ko dai an rufe ko kuma an goge shi, sai dai Aminiya ba ta da tabbacin ko mahukuntan Facebook ne suka goge shafin ko kuma shi ne da kansa ya goge.
Sai dai ta ziyarci shafin Instagram na mawaƙin, inda ta ga ya sa hoton wani sabon shafin Facebook mai suna Rarara Gallery, sannan ya rubuta cewa, “Wannan shi ne sabon shafin Facebook ɗina mai suna Rarara Gallery.”
A ƙasan rubutun, wasu matasan sun ci gaba da rubuta cewa shi ma za mu ‘nome shi’ wato shi ma ɗin za su tabbatar an goge shi.
A waƙar da tayar da ƙurar dai mawaƙin ya yi amfani da wasu baitoci da wasu suke ganin kamar cin fuska ce ga Arewa kasancewar ya yaba da ƙoƙarin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
A cikin waƙar, ya yi amfani da wasu baitoci kamar haka:
“Tinumbu ya gama mana aiki ba batun ɓoyo”.
“Ƙananan hukumomi ruhinsu ya dawo”.
‘’Yanzu talauci gyaram, yunwa gyaram,
kana security daram-damdam, ’yanci daram”.
‘’Sannu farin cikin ƙasa Tinubu, sai godiya, baba makanike wajen gyara lamba ɗaya”.
Sabuwar waƙar ta fito ne kwanaki kaɗan bayan mahaifiyarsa ta dawo daga hannun masu garkuwa.
Haka kuma ya fitar da waƙar ce kwanaki kaɗan kafin a fara zangazangar da matasa suka shirya sakamakon tsadar rayuwa da yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke fama da su, wanda hakan ya sa wasu suke ganin bai kamata ya ce an samu tsaro ba, alhalin har mahaifyarsa an sace.
Sai dai Malam Balarabe Kabeer, wanda masanin Hausa ne, kuma marubuci sannan jarumin fim na Hausayayiwani sharhi a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana a ciki cewa ba a fahimci kalmomin da mawaƙin ya yi amfani da su ba ne.
A rubutun, wanda ya yi taken ‘Rarara da maganganunsa da ya yi waɗanda suka ta da ƙura.Ya ce, “Itafa Hausa tana da sarƙaƙƙiya musamman ga mutumin da ya tsinci dami a kala a yaren, ba tare da huri, maimai ko sassarya ba, dama kuma a baya bai yi sassabe ko baɗen taki ba.
Ma’ana dai ya ji yaren ne a gari saɓanin waɗanda suka horu a hannun iyaye da kakanni ko kuma masu abun da suka sha ruwa da iska gami da hana idanu bacci don laƙanta.
Bari mu fara zuba fasahar mawaƙin kafin mu dawo mu yi fashin baƙi a kai.
“Talauci gyaram, yunwa gyaram, ƙarin sikuriti daram dam dam, ’yanci daram, sannu farin cikin ƙasa,Tunibu sai godiya baba bakanike wajen gyara lamba ɗaya, Murna talakkawa murna talakkawa. Ƙananan hukumomi ruhinsu ya dawo.
Bola Tinibu ya sai mana ’yanci talakkawa, yanzu arziƙi zai riƙa yawo gidan kowa.
Na ce murna talakkawa murna talakkawa, ƙananan hukumomi ruhinsu ya dawo Bola Tinubu ya sai mana ’yanci talakawa da arziki zai riƙa yawo gidan kowa. Murna talakawa murna talakkawa.”
Ya ƙara da cewa, “To ku biyo ni don na yi maku fashin baƙi ku gane saƙon da mawaƙin ke so ya isar a cikin maganganunsa. Na san kalmomin farko ne mafi yawan mutane ke ce-ce-ku-ce a kansu ga su kamar haka:
1.Talauci Gyaram.
- Yunwa Gyaram.
- Ƙarin Sikuriti Daram Dam
- Yanci Daram.
“Zan ɗauke su bi da bi mu yi bayani don warware zare da abawa.
Gyaram: Ita gyaram a harshen Hausa duk inda ka ji ta to tana korewa ne, idan kuma an yi amfani da amsa amo na ita kalmar to duk inda ta zo tana magana ne a kan rufewa ko an rufe koko a rufe.
Daram: Ita kuwa kalmar daram to ana magana ne a zaman
abu ko ma mene ne. Da yawan lokuta Hausawa na magana cewar abin ya zauna daram ko zaune yake daram da gindinsa, kuma akan yi amfani da ita sosai a lokacin da aka ajiye wani abu ko aka tsayar da shi ya yi daidai yadda ake buƙata, sai a ce ya zauna daram, har ma a wasu lokutan akan ce ya zauna daram Mahadi ka ture.”
Shi ma fitaccen malamin Hausa Farfesa Ibrahim Malumfashi ya ce, “Rararan dai! Ba zan ce komi ba, domin na san za a ce ina ɗaure wa ƙarya gindi! Sai dai na ji daɗin ganin cewa akwai ɗalibai masu hikima da fahimta ko ba a ajin jami’a ba! Godiya mai tarin yawa Balarabe Kabeer! Rarara mawaƙi ne na musamman!”
Ba wannan ba ne karon farko da mawaƙin yake ta da ƙura, musamman a kafafen sadarwa. Idan ba a manta ba, ya fito ya zargi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da lalata ƙasar kafin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi mulki.
A wajan wani taron manema labarai da mawaƙin ya kira, inda ya zargi tsohon shugaban da lalata kowane fanni na Nijeriya kafin ya miƙa ta ga magajinsa, wato Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mawaƙin ya kuma nuna nadamarsa ta goyon bayan Buharin a baya, inda ya ce ya yi da-na-sanin yin hakan.
Ya kuma ce hatta wata uku na farkon mulki Tinubu, sun fi shekara takwas na mulkin Buhari.
Sannan a lokacin ya ta da ƙura, inda ya ce duk da gudunmuwar da ya ba wa Shugaba Tinubu, ba a nemi shawararsa kafin a naɗa ministoci ba, inda ya ƙara da cewa, aƙalla idan ma ba a ba shi kujerar minista ba, to kamata ya yi a ce an yi kasafinsu da shi.