Yadda Sallar bana ta zo a baibai ga Musulmin Nijeriya
Wannan matsala ba laifin gwamnati kaɗai ba ce. Mu da kanmu muke ƙara janyo wa kanmu matsalolin.
A yanzu da ake cikin goma ta dokin Sallah za a iya cewa shirye-shiryen Sallar yana haduwa da tasgaro sakamakon halin da al’ummar kasar nan suka samu kansu a ciki na matsin tattalin arziki wanda ake ganin ya faru ne dalilin cire tallafin man fetur da gwamnati da kuma faɗuwar darajar Naira sakamakon hade kasuwar canjin kudaden kasashen waje.
A ziyarar da Aminiya ta kai kasuwannin Kantin Kwari da Sabon Gari da Kofar Wambai a Kano ta iske cewa ciniki ba kamar na shekarun baya ba.
Duk da cewa akwai mutane da ke shiga kasuwannin sai dai Aminiya ta lura ba su sayen wasu kayan a-zo-a-gani kamar na shekarun baya.
Alhaji Yusuf Madatai mai sayar da tufafi a Kasuwar Kantin Kwari ya shaida wa Aminiya cewa a bana akwai karancin masu sayen kaya. “Kamar yadda kike gani ba za a ce ba mutane a kasuwa ba, amma abin da ke faruwa shi ne mutane ba su iya sayen kayan kamar yadda aka saba.
“Kwastomomina masu sayen kaya da yawa a yanzu sun koma sayen kaɗan, wannan ya haɗa da masu sari suna sayarwa a unguwanni da masu sayen na amfanin kansu.
“Ko a bara za ki samu mutum ɗaya ya sayi atamfa sama da turmi 50 ga iyalansa da wanda zai raba wa dangi, amma a bana da ƙyar mutum ke iya sayen na iyalinsa.
“Kin san kayan sun yi tsada sosai wanda mu ma wallahi ba mu jin daɗin yadda abubuwan suke, domin a saya a sayar shi ne riba ba tarin kaya a shago ba.
“Ga kayan nan mun zo mun zube su amma ba a sayensu,” in ji shi.
Wani mai sayar da shaddoji a Kasuwr Kwari mai suna Abdullahi Nhu ya shaida wa Aminiya cewa bana babu harka a wajen mutane don haka ba ciniki kamar yadda aka saba.
Ya ce, “Kamar yau da ya rage saura kwanaki kaɗan Sallah, a da wallahi ba za ki iya samun shigowa cikin shagon nan cikin sauki ba, saboda yawan mutane da za ki iske suna jiran wasu su fita su ma su shiga amma yanzu ga shi nan babu mutane.
“A da a rana ban da masu sarin kaya, muna iya sayar da turmi 500 a rana. Amma yanzu da kyar muke iya sayar da turmi 50 zuwa 60.
“To mai sayen turmi biyar ya koma ɗaya, ai wannan yanayi sai dai mu ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Wani magidanci da Aminiya ta zanta da shi Malam Ali Sanusi ya ce “Na fi shekara 13 ina yi wa dangi da ’ya’yan ’yan uwana rabon kayan Sallah, amma wallahi a bana na kasa saya musu saboda tsadar rayuwa da aka shiga.
“To kuɗin da a baya kake samun atamfa uku da shi a yanzu sai dai ka sayi ɗaya. Ga shi kuma kai a matsayin ma’aikacin gwamnati albashin nan dai shi ne ba a kara wa mutum ko kwabo ba.
“Shi ya sa a bana na dauki wannan matakin don dole. Wallahi ko ’ya’yana da nake yi musu ɗinki iri biyu a bana kowa ɗaya ya samu. Takalmi ma na kasa saya musu.
“A yanzu abin da ya dame ni shi ne in samu kudin dinki da na abincin Ranar Sallah.”’
Haka halin yake ga masu sayar da takalma a Kasuwar Sabon Gari, kamar yadda Abdulkarim Shitu ya ce “To mun gode wa Allah ana shigowa ana saye sai dai ba kamar a baya ba.
“Kin ga yawan matan nan da yara da ke kasuwar nan yawanci sun kasa sayen kayan.
“Da a ce yawan mutanen da ke kasuwar nan za su iya sayen kayan ai da mun ji daɗi. Mu ma ba laifinmu ba ne tashin Dalar nan ya kawo tsadar kayan.”
Wata mata da Aminiya ta zanta da ita mai suna Rukayya Usman ta ce “Kin gan ni tun safe nake yawo da yara a kasuwa amma na kasa samun takalmi daidai kuɗina.
“Duk takalman da nake gani sun haure sama. Ga yara na kwaso na zo da su kasuwa na rasa yadda zan yi da su.
“Kin san dai yara ba za su gane halin da ake ciki ba. Yanzu a ce takamin na goyo babu na kasa da Naira dubu 10, ai an shiga wani yanayi.
“Takalmin da muka saya a bara a kan Naira dubu biyar a bana ya zama Naira dubu 10 zuwa dubu 12.”
A ɓangaren teloli ma haka lamarin yake domin sun nuna cewa yawan dinki ya ragu sosai.
Wani tela mai suna Nasiru Umar ya shaida wa Aminiya cewa a bana dinki sai hakuri.
“Kin ga dai shagon nan a da za ki zo ki samu ba masaka tsinke saboda yawan kaya, amma yanzu babu kayan sai dan abin da ba a rasa ba.
A hakan ma yanzu da Sallah ta matso ne aka fara kawowa sosai domin farkon azumin ba a kawo kaya.
“Za ki samu masu kawo iri uku zuwa huɗu yanzu sun koma biyu wasu ma ɗaya.
“Ga kaya sun yi tsada shi kuma dinkin ya yi tsada. Domin duk kayan dinkin da ake yin ado da su a atamfa ko shadda ko leshi shi ma farashinsa ya haure. Abubuwan ne wallahi sai a hankali,” in ji shi.
Yara da su ne suka fi murnar zuwan Sallah sun bayyana damuwarsu game da yadda Sallar za ta kasance a bana.
Abubakar Muhammad ya ce “Duk da ina so Sallah ta zo, amma gwiwata ta yi sanyi saboda mahaifina kayan Sallah ɗaya ya ɗinka min, ya ce ba ya da kuɗi kuma ya ce ba zai ci bashi don yi mana kayan Sallah ba.
“A yanzu ko takalmi bai saya mana ba, bai saya mana hula ba. Tuni Ummarmu ta ɗauko tsofafin hulunamu ta bayar aka wanke mana, takalmi ma ta ce za ta bayar a wanke mana.
“Su ma takalman ta ce sai ana jajibarin Salalh za ta bayar a wanke mana.”
A Jihar Yobe, Aminiya ta gana da wani magidanci Malam Sunusi Mai Kayan Miya a Kasuwar Damaturu wanda ya ce, “Ai a bana baya ma tunanin ɗinka kayan Sallah ga iyalansa domin a yanzu da ƙyar yake samun abin da za su ci.”
Ya ce “in dai ba wani ikon Allah ba, to, bai ga wata hanyar da zai bi don saya wa iyalai kayan Sallah ba.”
Shi kuwa Malam Muhammad Bello wani tsohon ma’aikacin gwamnati cewa ya yi, “Ai babu abin da za mu ce wa Allah sai dai godiya domin al’amura sun tsaya cik.
“Ta kai a yanzu batun yin kayan Sallah ga iyalai ma ba shi ne a raina ba abin da ke raina shi ne yadda za a samu abincin Sallah shi ma sai in dama ta samu, Allah ya kyauta.”
A Ibadan fadar Jihar Oyo, Musulmi sun fara shara da gyaran filayen Idi daban-daban da dubban Musulmi suka saba yin Sallar Idi bayan kammala azumin watan Ramadan na bana.
Aminiya ta gano cewa Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere ya kafa kwamitin tsabtace Babban Filin Sallar Idi na Agodi-Gate inda yanzu haka aka fara sare ciyayi da kawar da shara domin samar da tsabtataccen wurin da za a yi Sallar Idi mai raka’a biyu.
Shi ma Sheikh Sa’ad Abubakar, Babban Limamin Hausawa mazauna Ibadan ya bayar da umarnin a fara aikin sare ciyayi a filin da suke yin Sallar Idi a harabar Gidan Gwamnati a Ibadan.
Shi kuwa Babban Limamin Izala a Jihar Oyo, Sheikh Sani Haruna cewa ya yi duk da yake filin da suka saba yin Sallar Idi na harabar Filin Wasanni na Lekan Salami ba ya da buƙatar sassabe saboda a shafe yake da kankare, amma akwai buƙatar share shi kafin isowar wannan rana.
Haka lamarin yake a sauran filayen Sallar Idi a unguwannin birnin Ibadan.
A waje ɗaya kuma, Aminiya ta gano cewa yawan Musulmi masu rububin shiga kasuwanni don sayen suturun Sallah ga iyali, ya ragu.
Hakan ya biyo bayan halin tsadar rayuwa a kasa baki daya ne.
Wani mazaunin Ibadan Alhaji Isa Ibrahim Saleh ya shaida wa Aminiya cewa “Akwai ’ya’yana 6 maza uku mata 3 a tare da ni, amma duka babu wanda ya yi min magana a kan kayan Sallah domin su ma sun fahimci halin tsadar rayuwa da ake ciki.
“Wannan matsala ba laifin gwamnati kaɗai ba ce. Mu da kanmu muke ƙara janyo wa kanmu matsalolin,” in ji shi.