AddiniKananan LabaraiKiwon Lafiya• Created May 22, 2020 17:30
Yadda sallar Juma’a ta gudana a wasu masallatan Kano
An gudanar da sallar Juma’a ta farko a jihar Kano bayan hana tarukan ibada a wani mataki na kare yaduwar annobar coronavirus. Gwanan jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bai wa al’umar jihar Kano damar yin sallar Juma’a da na Idi da ake sa ran yin a ranar Lahadi , 24 ga watan Mayu.
An gudanar da sallar Juma’a ta farko a jihar Kano bayan hana tarukan ibada a wani mataki na kare yaduwar annobar coronavirus.
Gwanan jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bai wa al’umar jihar Kano damar yin sallar Juma’a da na Idi da ake sa ran yin a ranar Lahadi , 24 ga watan Mayu.
Gwamnan Kano, Abudullahi Umar Ganduje a sa’ilin da ya shiga masallaci ta na’uarar kashe kwayar cuta
Sashe na masallata a harabar masallacin Juma’a a Kano
Sashen masallata a masallacin gidan gwamnatin jihar Kano
Wani Sashe na masallata a lokacin sallar Juma’a a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje a lokacin da ya ke gudanar da sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnatin jihar
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a lokacin hawan Juma’a
Nan ma wani sashe ne na masallata a masallacin Shehu karami da ke Kano
Sashe na masallata a masallacin Shehu Karami da ke Kano (Tsohon hoto).
Shehu Malam Karami a lokacin da ya ke gabatar da hudubar juma’a a Kano
Masallata ne a lokacin sallar Juma’a a masallacin Gidan Gwamnatin Jihar Kano
Wani sahse na masallata a wani masallacin Juma’a a Kano da ba a bada tazara ba
Nan ma masallata ne a wani masallaci Juma’a a Kano da basu bada tazara a tsakanin su ba
Sashi na fadawan sarkin Kano a lokacin sallar Juma’a