Yadda Sallar Layya za ta kasance a Najeriya da Saudiyya
Lahadi 16 ga watan nan na yuni, 2024 za a yi Sallar Layya a Najeriya da Saudiyya
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana Lahadi 16 ga watan nan na yuni, 2024 a matsavin ranar Sallar Layya a Najeriya.
Sarkin Musulumin ya kuma ya sanar cewa Juma’a 7 ga watan na yuni shi ne ranar 1 ga wayan Dhul-Hajji.
A ranar Alhamis Sarkin Musulumi kuma Shugaban Majalisar Kolin Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya sanar da ganin jinjirin wayan na Dhul-Hajji, 1445 Hijiriyya.
Sanarwar dauke da sa hannun Sakataren Kwamitin Gwanin Wata na Kasa, Malam Yahaya Muhammad Boyi na zuwa ne bayan makamanciyarta ta ranar Talata da Sarkin Musulmi ya umarci Musulmin kasrar su fara neman sabon watan Dhul-Hajji ranar Alhamisi.
Ganin watan na Najeriya ya zo daidai da na kasar Saudiyya inda za maniyyata ke shirin fara gudanar da aikin Hajji daga ranar Juma’a 14 ga Dhul-Hajii.
Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar cewa a wannan shekarar Musulimi kimanin miliyan uku ne za su sauke faralin aikin Hajji a kasar.
Zuwa ranar Litinin, 10 Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ke sa ran kammala kwashe maniyyatan kasar zuwa Saudiyya domin sauke farali.
Juma’a 15 ga yuni, 2024, shi ne 8 ga Dhul-Hajji, ranar da alhazai za su bar birnin Makkah zuwa Mina, inda za su kwana sannan su wuce filin Arafa washegari.
Halartar tsayuwar Arafa ita ce babban rukunin aikin Hajji, kuma duk mahajjacin da bai samu ba, ba shi da aikin Hajji.
Ranar Arafat za ta kasance Asabar 15 ga watan yuni, inda bayan halartar tsayuwar Arafa, Alhazai za su je filin Muzdalifa su kwana.
Washegari, Lahadi 16 ga wata — ranar Babbar Sallah ga mazauna gida — alhazai za su bar Muzdalifa su koma Mina, inda za su yi jifan farko, yanka hadaza, aski da kuma Dawafin Dawafin Ifada a Makkah sannan su koma Mina kafin dare.
Duk alhajin da ya yi uku nan — jifan farko, yanka hadaza, aski — zai iya cire ihiraminsa, da kuma yin duk abin da aka haramta wa mahajjata, amma banda jima’i.
Kazalika alhaji na iya jinkirta Dawafin Ifada sai idan ya dawo Makkah bayan kammala jifa gaba daya. Amma yin Dawafin Ifada a Ranar Hadaya shi ne mafi falala.
Bayan ranar jifan farko alhazai na da zabin ci gaba da zama da kuma jifa a Mina na karin kwanaki biyu ko uku, kafin su bar Mina su koma Makkah, inda kafin su koma garuruwansu za su yi Dawafin bankwana.