Yadda sana’ar wanzanci ke neman vacewa
Sana’ar wanzanci sana’ar gargajiya ce da ke cike da abubuwa na al’ajabi. An fi samunsu a Arewacin Najeriya, inda suke yin aski da kaciya da kuma ba da magunguna iri-iri. Amma saboda canjawar zamani yanzu wanzamai sun fara shiga cikin matsala da rashin tabbas sakamakon fara bacewar sana’arsu. Wanzamai mafi yawanci gadon sana’ar suke yi […]
Sana’ar wanzanci sana’ar gargajiya ce da ke cike da abubuwa na al’ajabi. An fi samunsu a Arewacin Najeriya, inda suke yin aski da kaciya da kuma ba da magunguna iri-iri. Amma saboda canjawar zamani yanzu wanzamai sun fara shiga cikin matsala da rashin tabbas sakamakon fara bacewar sana’arsu.
Wanzamai mafi yawanci gadon sana’ar suke yi daga iyayensu maza, amma wani lokacin, ana samun wasu daga waje da suke sha’awar koyon sana’ar don su samu hanyar cin abici. Amma bincike ya nuna cewa sana’ar ba abar da mutum zai koya cikin kauki da sauri ba ce.
Wakiliyar Aminiya da zagaya domin nemo wanzami, inda ta sha wahalar gaske kafin ta tsinkayi wanzami a cikin Abuja. Daga bisani ta hangi wani rataye da jakar fata a kafadansa da zabira da sauran kayan aiki, inda ta ga alamun cewa wanzami ne.
Bayan gaisuwa, wanzami sai ya gabatar da kansa da Abdulmalik Abdullahi, sannan ya bayyana cewa yanzu sana’ar wanzanci ba kamar yadda take da ba.
“Idan kika kwatanta da lokacin da na shiga sana’ar nan, gaskiya yanzu ba mu samun abokanan hulda yadda muke samu a da. Mutane yanzu gani suke al’adunmu ba su da tsabta. Saboda haka, sun fi so su je shagunan aski ko kuma asibitoci don yin kaciya. Amma ba su san cewa tun da iyayenmu suka koya mana wannan sana’ar ba, sun nuna mana yadda za mu tsabtace kayan aikinmu da yadda za mu kashe cututtuka da za mu iya ba. Duk wanda za mu yi wa aski, sai mun sa sinadarin sifirit a askar tukuna sannan mu sa wuta mu dan kona askar. Babana ya yi wanzancin nan, amma cikin ’ya’yansa uku, ni kadai na gaji sana’ar. Duk lokacin da zai yi aski, ko kaciya, ko hada magani, sai in tsaya in sa masa ido, ina kallon duk abin da yake yi. Amma duk da haka, ko da ya rasu, hannuna bai riga ya yi wari ba. Amma yanzu kam, Alhamdulillah. Na iya komai a sana’ar.”
Bayan wannan bayanin, sai Abdulmalik ya bude jakarsa, inda ya nuna wa wakilyarmu kayan aikin da ke ciki kamar aska da kaho da ake jan jini da shi, da magungunan gargajiya da dutse da sabulu da sinadarin sifirit da abin kyasta wuta wato lighter, da sauransu. Daga nan, sai ya cigaba da cewa, “Yanzu matasa ba su da sha’awar gadon sana’ar. Saboda haka mun fara rage yawa. Iyayayenmu da muka gada sana’ar daga wajensu, sun mutu wasu kuma sun tsufa. Mu kuma ’ya’yanmu ba su da sha’awar su gada. Amma duk da haka, akwai matasa ba laifi da ke ladabi wajen wanzamai don su koya sana’ar.”
Ya kara da cewa shekara 15 ke nan yana yin wannan sana’ar, amma duk da haka, wannan lokaci kadan ne idan ka kwatanta da wadanda suka yi shekara 70 ko sama da haka, “Na zo Abuja daga Katsina shekara 8 da suka wuce don tunanin cewa kila zan fi samun kudi. Da na zo gaskiya a lokacin haka din na sama, amma ba yanzu ba. Da ace banda ’yan uwanmu Hausawa, wasu ma suna nemanmu, da kila sana’ar ba ta bace haka ba. Amma duk da haka, ba sana’ar da zan so yi idan ba wannan ba, don na fi kwarewa a ita.
“Amma gaskiya riba babu yawa yanzu. Aski Naira 100 zuwa Naira 150 nake karba. Idan na yi kasuwa sosai, ina iya samun Naira 2500 zuwa Naira 3000.Watarana ba na samun komai. Yanzu sana’ar ba ta da tabbas kuma idan ka auna wahalar da muka sha wajen koyo, gaskiya abin akwai takaici.”
Abdullahi ya kara da bayani a kan yadda suke hada magunguna, “Muna amfani da ganye, da ’ya’yan itatuwa da yawa. Amma mafi yawacinsu ba a samu a nan Abuja, sai dai can Arewa. Shi karatunsa daban ne.”
Wakiliyarmu ta kara zagayawa inda ta sake tsinkiyar wani wanzamin, mai suna Muhammad Alkali wanda shi ne Sarkin Aska wato Shugaban Wanzamai da ke Utako daJabi a Abuja a cikin wata inuwa. Nan ta ga wani wanzami mai suna Muhammad, yana ma wani mai suna Ahmed aski. Ahmed din ya fada wa wakiiyarmu cewa ya yi shekara goma yana zuwa wajen don ya yi aski.
Sarkin Aska Alhaji Alkali ya fada mana cewa shi gadon sana’ar ya yi kuma ya yi shekara 60 yana yi. Amma duk cikin shekarun nan, sana’ar ba ta taba yin samun koma baya ba kamar yanzu.
“Ni kadai ne wanzamin da ke kamu a nan yankin. Kuma duk da aikin da muke yi, wani lokacin muna tashi daga nan ba tare da ko kwabo ba. Har kayan aski na zamani muka siya don kada a barmu a baya, amma duk da haka a banza. Da can har layi ake yi don aski a nan. Abin da bakin ciki gaskiya.”
Ahmed da wakiliyarmu ta iske ana masa aski ya bayyana cewa “Idan dai ina Abuja, to dole sai na zo nan nake samun a yi min aski. Mutanen nan ma sun zama kamar ’yan uwa a gareni.”
Wani mai suna Sham’una Lukman ya bayyana cewa Sarkin Aska har cikin dakinsa yake zuwa a gidansa ya masa askida, amma yanzu, saboda tsoron cututtuka, yana shakka, “Ina jin labarai inda mutane suka rasa rayuwarsu bayan kaciya don zubar jini kuma cutar AIDS na cikin cututtukar da mutum ke iya kamawa. Don haka, na siya abin aski na zamani wato clipper da nake amfani da shi idan zan je shagon aski ko kuma idan zan yi wa yarana a gida. Yana da amfani mutum ya san wadannan abububuwan. Rashin ilimi na cutar da wasunmu.”
Da Aminiya ta tuntubi masana a bangaren kiwon lafiya a game da sana’ar wanzanci, Dokta Fatima Kaigama da ke aiki a Asibitin Garki da ke Abuja ta yi bayyani sosai game da cutar da mutum ke iya samu a wajen wanzamai.
“A zamanin yanzu, mutane sun waye kuma sun samu ilimi a kan cututtuka iri-iri. Amma ya kamata a kara tuna wa mutane cewa aska na tattare da kwayar cutar sepsis. Kuma idan aka samu matsala wajen kaciya, yana iya jawo rasa rai don zubar jini. Cutar HIB da Hafatitis B da C (cutar hanta) suna cikin manyan cututtukan da ake iya samu. Maganin gargajiya kuma na iya ja maka ciwon koda.
Duk da wanzamai na kokarin ganin sun tsabtace kayan aikinsu, ya kamata a kara ilimantar da su. A wurare inda babu ingantattun asibitoci, harkar kiwon lafiya da warkar da wasu cututtuka na iya gagara, kuma hakan na iya sa wa a rasa rai.
Amma duk da yadda ake barin sana’ar, lallai sana’ar wanzanci na da sauran lokaci kafin ya bace.