Yadda sansanin Boko Haram na dajin Sambisa ya kasance – Shaidu
Rahoton farko da ya fito daga babban sansanin Boko Haram a dajin Sambisa da ke Jihar Borno bayan kai masa gagarumin hari da sojoji suka yi, ya nuna hoton yadda aka samu mace-mace da rugurguza wurin.Rahoton ya kuma nuna yadda ’ya’yan kungiyar suke zaune a wani tsararren matsuguni a tsakiyar wannan dokar daji.Rahoton wanda sashin […]
Rahoton farko da ya fito daga babban sansanin Boko Haram a dajin Sambisa da ke Jihar Borno bayan kai masa gagarumin hari da sojoji suka yi, ya nuna hoton yadda aka samu mace-mace da rugurguza wurin.
Rahoton ya kuma nuna yadda ’ya’yan kungiyar suke zaune a wani tsararren matsuguni a tsakiyar wannan dokar daji.
Rahoton wanda sashin Hausa na gidan rediyon BBC Landan ya bayar a ranar Litinin da ta gabata, ya ginu ne kan tattaunawar da aka yi da shaidun da suka yi da’awar cewa su ne rukunin farko na mutanen da suka fara isa sansanin bayan da sojojin suka ruguza shi.
Shaidun sun bayyana dalla-dallar yadda muhallin yake dauke da gidaje da asibiti da bohul-bohul wadanda yanzu aka lalata su bayan harin na sojojin.
Wani ganau wanda aka ki bayyana sunansa saboda dalilan tsaro ya bayyana yadda ya iske wurin kamar haka:
“Hakika na je dajin Sambisa, kuma na ga dimbin motocin da aka kona. Su ’yan Boko Haram, suna da gidaje da dakuna da bohul-bohul da abinci da asibiti. Na ga dimbin gawarwaki – na maza da mata. Amma a zahiri matattun maza sun fi mata yawa. Wasu an dagargaza kafafunsu wasu sun kone,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Tabbas sun tara makamai a wurin. Kuma mun samu wani mutum da aka raunata da ba zai iya gudu ba. Ya shaida mana cewa shugabansu ya gaya musu cewa gwargwaya ta kare don haka su ajiye makamansu su koma gida. Ya ce mana wasu daga cikin mutanen da aka sace sun yi kokari sun gudu. Kuma ya ce wasu daga cikin matan da aka kashe ’ya’yan kungiyar ne suka kamo su, yayin da wasu suka biyo mazajensu da aka kamo zuwa dajin.”