Yadda sarakuna suka burge ’yan kallo a Hawan Dabar cikar Kaduna shekara 100
A ranar Asabar 16 ga Disamban bana ne birnin Kaduna fadar Jihar Kaduna ya cika shekara 100 cif da kafawa, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar ta shirya gagarumin bikin da ya kunshi Hawan Daba don murnar wannan rana. Dubban jama’a daga sassan kasar nan sun halarci bikin wanda manyan sarakunan Arewa suka yi hawan […]

A ranar Asabar 16 ga Disamban bana ne birnin Kaduna fadar Jihar Kaduna ya cika shekara 100 cif da kafawa, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar ta shirya gagarumin bikin da ya kunshi Hawan Daba don murnar wannan rana. Dubban jama’a daga sassan kasar nan sun halarci bikin wanda manyan sarakunan Arewa suka yi hawan da ya burge jama’a. Bikin Hwan Daban wanda ya gudana a filin wasa na Murtala Mohammed da ke cikin garin Kaduna ya samu halartar gwamnoni da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo da ministco da manyan jami’an Gwamnatin Tarayya da na jihohi da kuma ’yan kasuwa.
Daga cikin sarakunan da suka halarci hawan da aka yi sun hada da Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi II da Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da kuma Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai.
Sauran sun hada da masu martaba Sarakunan Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu da takwaransa na Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar da na Jama’are Alhaji Muhammadu Wabi da Sarkin Keffi Alhaji Shehu Chindo Yamusa da na Hadeja Alhaji Adamu Abubakar Maje.
Gwamnonin da suka samu halarta Hawan Dabar su ne Alhaji kashin Shettima na Jihar Borno da Alhaji Aminu Masari na Jihar Katsina, sai mataimakan gwamnonin jihohin Gombe da Zamfara da Bauchi.
Baya ga al’ummar Hausawa da Fulani da Barebare akwai kabilun da suka fito daga jihohin Filato da Kwara da Neja da suka baza kolin nunin al’adunsu.
Sarakunan da suka burge jama’a a yayin Hawan Dabar sun hada da sarakunan Kano da Zazzau da Gombe da Bauchi da Hadeja da Keffi da Jama’are da Bauchi inda dimbin jama’ar da suka halarci bikin suka rika tafi da shewa da kuma yi musu jinjina.
Ayarin mahaya da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya jagoranta ta burge jama’a sosai domin baya ga yawan dawaki da suka mara masa baya ya hawa ne da wani rakumi.
Haka Mai martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu ýAbubakar da Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi sun yi matukar burge ’yan kallo musamman irin yadda suka rika yin wasa da dawaki a filin.
Akalla dawaki da rakuma dubu biyu ne aka yi Hawan Dabar da su kamar yadda wadanda suka shirya Dabar suka bayyana.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya bayyana hawan a matsayin wacce ba a taba yin irinta ba a tarihin Arewacin kasar nan. Ya kuma bayyana cewa Jihar Kaduna ta shirya bikin ne domin tunawa ta gwagwarmayar da shugabannin baya irin su Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Malam Sa’adu Zungur da Sa Kashim Ibrahim da sauransu suka bayar wajen gina birnin bayan Turawa sun bar kasar nan.
Ya ce ko shakka babu Jihar Kaduna ýjiha ce da ke da matukar tarihi a Arewacin kasar nan musamman kasancewar ta taba zama cibiyar tsohuwar Jihar Arewa.
Gwamna El-Rufa’i ya kuma yaba wa sarakunan da suka samu halartar wannan Hawan Daba inda ya ce dukansu sun shiga tarihi domin ko bade ko ba jima nan da shekara dari masu zuwa za a tuna da gudunmawar da suka bayar wajen ganin Hawan Dabar ya gudana cikin nasara.
A jawabin Shugaban Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna kan shirya bikin, inda ya ce Jihar Kaduna tana da matukar tarihi a kasar nan.
Ya bayyana bukatar ganin Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye wajen magance matsalar rashin tsaro da kuma aikin yi a tsakanin matasan yankin Arewa da kasa baki daya.
Ya ce yanzu haka Gwamnatin Tarayya ta magance barazanar matsalar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas wadda a baya take barazana ga kasar nan baki daya.
Wakilin Shugaban kasa kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammed Musa Bello ya ce Allah ne Ya kaddara za a hade Arewa da Kudu domin samar da Najeriya a 1914. Ya kara da cewa Jihar Kaduna ce ta raini sauran jihohi 19 na Arewa har aka samu ci gaban yankin da kuma kasa baki daya. “Jihar Kaduna ce ta raini sauran jihohi 19 na yankin Arewa. Hakan yana nuna muhimmancinta wajen ci gaban Arewa da kuma kasa baki daya,” inji shi.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ya bukaci al’ummar kasar nan ne da su ci gaba da zama lafiya da junansu. Ya ce kasancewar Najeriya kasa daya al’umma daya alheri ne maimakon rarrabuwarta.
A jawabinsa Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris kuma Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Kaduna, kira ya kara yi ga al’ummar kasar nan kan su tashi tsaye wajen fahimtar juna domin a zauna lafiya.
“Akwai alheri a zamanmu na al’umma daya a maimakon rarrabuwar kawuna da ake fama da shi. Zaman lafiya shi ke kawo ci gaba a cikin jama’a da kuma kasa,” inji shi.
Ya kuma yaba wa sarakunan da suka samu yin hawa a wajen ciki har da shi kansa wanda ya bayyana a matsayin zai kara dankon zumunta da fahimtar juna a tsakanin jihohi da jama’ar Arewacin kasar nan.