Yadda sarautar Wawan Sarki take a kasar Hausa
Aminiya ta zanta da Wawan Sarkin Zazzau Amadu Umar domin jin asalinsa da yadda ya samu sarautar Wawan Sarki da kuma aikin Wawan Sarki a fada ga abin da yake cewa,, “Kana ganina wawa ina ganinka sakarai.” Mene ne tarihinka da matsayin sarautarka ta Wawan Sarki a fada? To ni dai asalina Bafulatani ne […]
Aminiya ta zanta da Wawan Sarkin Zazzau Amadu Umar domin jin asalinsa da yadda ya samu sarautar Wawan Sarki da kuma aikin Wawan Sarki a fada ga abin da yake cewa,, “Kana ganina wawa ina ganinka sakarai.”
Mene ne tarihinka da matsayin sarautarka ta Wawan Sarki a fada?
To ni dai asalina Bafulatani ne kuma Allah Ya kawo ni garin Zariya kuma na kwashe shekaru da dama a birnin Zariya, ba zan iya tuna iya shekarun da na yi a Zariya ba sai dai na kwashe shekaru kamar arba’in da wani abu, kuma ni ne Wawan Sarkin Zazzau. Kana ganina wawa ina ganinka sakarai, na kai shekara kusan 30 a wannan sarautar ta Wawan Sarki. Aikina shi ne, in ba da dariya da kuma nishadantar da Sarki da sauran mukarraban Sarki da bakin Sarki ka ji aikina ke nan a fada. Kuma na yi karatun addini da na boko sai dai ba mai yawa ba sosai.
Ka gaji sarautar ce ko kawai ka shiga ne?
A’a ba gado na yi ba ni dai Allah ne kawai Ya nufe ni da yi. Domin dama akwai wannan sarautar ta Wawan Sarki a masarautun Hausa, musamman a fadar Mai martaba Sarkin Zazzau tana daya daga cikin sarautu masu girma da kuma tarihi. To sai Allah Ya yi wa mai rike da sarautar ta Wawan Sarki rasuwa domin ni ban ma san shi ba, kuma ba a samu wanda ya ci gaba da sarautar ba. Ina zaune tare da mutanen arziki sai wani daga cikin masoya Sarki ya ga yadda nake hulda da jama’a. Sai ya ce ina ba shi sha’awa domin ya ga ba na fushi kuma ga shi na cika raha da ban- dariya. Don haka zan dace da Sarautar Wawan Sarki idan ina bukata zai kai ni. Sarautar tana bukatar wanda ba ya fushi kuma tana bukatar mai son jama’a don haka idan ina bukata sai ya kai ni in maye wanda ya rasu.
To bayan ya kai ni fada sai aka rika shiga da ni ofishi-ofishi ina ganin manyan mutane kuma aka amince da ni aka hada ni da Sarkin Busa aka ce ya kai ni gaban Mai martaba Sarki ana gabatar da ni a gabansa sai ya amince da ni ya ce zan iya. To da na tashi yin godiya sai na dafa kunnuwana, na rika kwarara ihu ina murna. Sarki ya amince da ni jama’ar da ke wurin suka barke da dariya. To daga nan, na fara kuma na san na karbu a Majalisar Sarki. Ka ji yadda na fara aiki a fada a matsayin Wawan Sarki.
To daga wancan lokaci har zuwa yanzu ina zaune a fada nan nake ci nan nake sha tare da yin duk wata hidima ta rayuwar yau da kullum.
Kai ma kana hawa ne kamar yadda sauran hakimai suke hawa idan ana gudanar da biki a masarautar?
Ai duk wata kwalliya da ka ga ina yi, ina yi ne saboda in burge Sarki, don haka da bikin Sallah ko wani sha’ani ina daukar kwalliya kamar yadda kowa ke yi kuma ni ma ina hawa kamar yadda duk wani hakimi yake hawa. Domin ka ga gorar nan tawa, ita ce dokina da ita nake ado kuma ita nake hawa kuma ita nake dukan duk wani mai neman ya yi ganganci a gaban Sarki. Ba ka ji wakar da marigayi Shata ya yi mini ba inda yake cewa, ba a habaici a fadar Shehu duk wanda ya ce zai yi habaici wawa tashi buga mai gorar taka.Don haka ba na wasa da wannan gorar da ka gani, kuma idan na yi hawa za ka ga Sarki yana mini jinjina kamar yadda yake wa kowa.
To da gaske ne wai kana iya fadin duk wata magana a gaban Sarki ba tare da wani shayi ba?
Kwarai da gaske domin idan na ga Sarki baya walwala sai in kirkiri wani abin da na san zai sa Sarki ya yi dariya. Sai in ce Sarki ka yi wawan zama to fadin haka na iya sa Sarki ya yi dariya kuma makarraban da suke kewaye a fada sai ka ga suna dukar da kai kasa wai sun ji kunya an fada wa sarki maganar da ba ta dace ba.
To matakan nawa kuma ’ya’yanka nawa, kuma kana da mai gado?
Matana biyu sai dai Allah ya yi wa daya matar tawa rasuwa saura daya, ’ya’yana biyu namiji da mace kuma shi namijin yana can a Jihar Nasarawa a Keffin Yamusa kuma ina ganin ba ni da mai gadona ko da yau Allah Ya yi min rasuwa.
To mece ce fatarka ga al’ummar Masarautar Zazzau?
Fatata ita ce Allah Ya ba mu zaman lafiya da kuma kaunar juna kuma al’ummar kasar Zazzau su ci gaba da bai wa Mai martaba Sarki hadin kai da kuma yi masa addu’a.