Yadda Sarki da tsohon shugaban yanki da iyalansu suka rasa rayukansu a turmutsitsin Muna
Tsohon shugaban riko na karamar Hukumar Illela a jihar Sakkwato Alhaji Bello Gidan Hamma da Sarkin Zing Alhaji Ibrahim Abbas Sambo da ke jihar Taraba, suna cikin wadanda suka rasa rayukansu a yayin turmutsitsin da ya faru a wurin jifar shedan a lokacin aikin hajjin bana, sai dai tasu rasuwar ta zama daban ne saboda […]

Tsohon shugaban riko na karamar Hukumar Illela a jihar Sakkwato Alhaji Bello Gidan Hamma da Sarkin Zing Alhaji Ibrahim Abbas Sambo da ke jihar Taraba, suna cikin wadanda suka rasa rayukansu a yayin turmutsitsin da ya faru a wurin jifar shedan a lokacin aikin hajjin bana, sai dai tasu rasuwar ta zama daban ne saboda har da matansu da iyayensu suka rasu a turmutsitsin.
Alhaji Muhammad Sarki, Magajin garin Gidan Hamma, da ke cikin karamar hukumar Illela a jihar Sakkwato, shi ne mahaifin tsohon shugaban riko na karamar hukumar Illela Alhaji Bello, ya bayyana wa Aminiya yadda ya samu labarin rasuwar dansa kamar haka, ‘ A ranar Alhamis da ta gabata, wato ranar Sallah layya, na samu labari a gari cewa wani abu ya faru Makka na cinkoso har ya yi sanadiyar rasa rayukka da dama, ban yi kasa a gwiwa ba na dauki waya na kira daya daga cikin iyalaina Muhammadu Nasiru, kani ga kantoma, bayan ya dauki waya nake tambayarsa labarin halin da suke ciki, kawai yake gaya min ba lafiya, don kantoma Allah Ya yi masa cikawa, shi ne ya shafe shi da hannunsa. Na ce sauran fa, ya ce min har yanzu ba a san ida suke ba, kuma an zagaya asibiti da sauran wurare ba a gansu ba, kuma wadansu ba a iya gane fuskarsu in aka ga gawarsu, da haka muke kyautata zaton sun mutu, don har yanzu da nake magana da kai ba wani labarinsu.’
Alhaji Muhammad ya kara da cewa ‘Su shida ne suka tafi a karkashin jagorancin kantoma, dukkansu zuriya daya ne, iyalan gidana biyar ne suka rasa ransu a Saudiya, da shi Bello Magaji da matata da abokiyar zamanta Hajiya Umulkhairi da kanwata, gwaggonsa ke nan Hajiya Hauwa’u da matansa biyu Umaima da Balkisu.’’
‘’Kantoma ya bar mu ni mahaifinsa da mahaifiyarsa, yana da shekaru 43, da ‘ya’yansa bakwai,, maza biyu mata biyar, dukkansu kanana. Mun ya rashin yaro mai ladabi da son jama’a da taimako, matansa ma ‘yan wannan gari ne Gidan Hamma, don haka ne bakin ciki ya mamaye garin, don kusan kowa an taba.’
Honarabul Haliru Garba, dan uwa ne ga marigayin, yanuna bakin cikinsa kan rasa gwarzo, jarumi, mai sadaukarwa da son jama’a da kyawawan dabi’a wanda ba ya son tashin hankali.
Malam Muhammad Mukhtar, wanda kani ne ga Margayin, shi ne suka yi waya ta karshe da shi, ya ce cikin dare kafin a wayi gari da labarin rasuwarsa, shi marigayin ne ya kira shi da kansa yake tambayarsa lafiyar gida da yi masa nasihohi, ashe maganar karshe ne suka yi.
Aminiya ta so jin ta bakin mahaifiyar marigayin da matarsa da ya da ya bari, amma Magaji ya ce ba za su iya magana da manema labarai ba.