Yadda Sarki Sanusi ya yi koyi da kakansa a dambatta
A kokarinsa na koyi da kakansa Sarki Sanusi, Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II a ranar Asabar 17 ga watan Oktoba ya yi hawan daushe inda ya yi amfani da taguwa a matsayin abar hawansa ba kamar yadda aka saba yin amfani da doki ba. Tarihi ya nuna cewa kakansa Sarki Sanusi a zamaninsa shi ma […]

A kokarinsa na koyi da kakansa Sarki Sanusi, Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II a ranar Asabar 17 ga watan Oktoba ya yi hawan daushe inda ya yi amfani da taguwa a matsayin abar hawansa ba kamar yadda aka saba yin amfani da doki ba.
Tarihi ya nuna cewa kakansa Sarki Sanusi a zamaninsa shi ma ya yi amfani da taguwa ce a matsayin abar hawansa, wanda kuma tun daga wancan lokacin ba a sake samun sarkin da ya yi irin hakan ba, sai fa a wannan lokaci .
A ranar Juma’a zuwa ranar Lahadin da ta gabata Sarkin Kano Muhamadu Sanusi ya fara gudanar da rangadi ta hanyar kai ziyara garuruwan danbatta da Makoda da Ungogo.
Rahotanni sun bayyana cewa yana daga tsarin masarauta idan aka nada sabon sarki ya kai irin wanann ziyara ga gundumomin masarautarsa don ya gana da hakimansa da sauran talakawa don sanin matsalolinsu. Hakan ya sa a duk lokacin da talakawa suka samu labarin sarki zai zo wurinsu suke murna tare da yin fitar dango don su ga sarkinsu.
Aminiya ta gano cewa lokacin da Sarkin ya isa garin danbatta a ranar Juma’a mutane sun yi cincinrido a garin don tarar sarki tare da yi masa maraba, musamman a wannan lokaci da yake shi ne karo na farko da Sarkin ya kai wanann ziyara a garin.
A wanann lokaci Sarkin ya jagorancin sallar Juma’a a babban Masallacin Juma’a na garin, inda a hudubarsu ya hore su da tsoron Allah da kuma bin iyaye.
Tarihi ya nuna cewa jagorantar sallar Juma’ar da sarkin ya yi, koyi ya yi da kakansa, domin an samu Sarki Sanusi ya jagoranci jama’ar garin danbatta sallar Juma’a.
Sannan daga bisani Sarkin Kano Sanusi II ya gabatar da jawabi a kofar gidan Hakimin garin, wato Sarkin Bai Alhaji Muktari Adnan. A wannan lokaci ma Sarkin ya yi wani abu na koyi da kakansa inda ya sanya wa Hakimin na danbatta alkyabbar da ya ba shi kyauta. Wannan ma daya ne daga cikin abubuwan da kakansa Sarki Muhamamdu Sanusi ya yi a zamanin mulkinsa, wanda kuma ba a taba samun sarkin da ya aiwatar da wanann kyauta ga Hakimin danbatta ba.
A wannan lokaci Sarkin Kanon ya raba lambar yabo ga wasu ‘yan asalin yankin guda 10 wadanda suke bayar da gudunmawa wajen ci gaban yankin. Mutanen sun hada da Alhaji Aminu Dabo da Dokta Mansur Muktar da Alhaji Ibrahim Amasaye da Dokta Amina Muktari Adnan da sauransu.
Har ila yau a wannan lokaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga jama’ar yankin da su zama cikin shirin ko-ta-kwana ta fuskar tsaro, da zarar sun ga bakuwar fuskar da ba su gane ba to su yi gaggawar sanya idanu akanta tare da sanar da jami’an tsaro.
Bayan an gama taron an gabatar da wata yar kwarya-kwaryar daba wacce Hakimin danbatta Alhaji Muktari Adnan ya shirya don girmamawa ga sarkin.
A lokacin wanann rangadi, sarkin ya kwana a garin danbatta, sannan da gari ya waye ranar Asabar ya nufi garin Makoda inda ya sauka a fadar Hakimin yankin Alhaji Wada Waziri (Sa’in Kano).
A garin Makoda ma Sarkin Kano Muhamadu Sanusi tare da Hakimin yankin sun gabatar da jawabai ga al’ummar yankin, inda sarkin ya yi kira ga jama’ar yankin garin Makoda da su da su bai wa harkar neman ilimi muhimmanci, musamman ilimin ’ya’ya mata. A wannan rana Sarkin Kanon Muhamamdu Sanusi ya koma garin danbatta inda ya sake kwana a can.
A ranar Lahadi kuma sai Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi ya nufi garin Ungogo, inda ya sauka a kofar gidan Hakimin Ungogo Alhaji Abdulkadir Ahmad Chedi. Kamar a sauran kananan hukumomin, a garin Makoda ma an gabatar da jawabai inda Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi ya yi kira ga jama’a da su kafa zaurikan sulhu, inda za a rika sulhunta tsakanin ma’aurata, a cewar sarkin ta haka ne za a samu raguwar yawan mace-macen aure da ake fama da shi a jihar.
Bayan an tashi daga wanann taron ne sai sarkin da tawagarsa suka nufi gidansa na Fanisau da ke wannan yanki na karamar Hukumar Ungogo. Bayan Sarki ya huta ne da yammaci ya koma cikin birnin Kano.
Aminiya ta rawaito cewa a dukkanin kananan hukumomin da Sarki Sanusi II ya ziyarta ya raba littafin da yake dauke da dokokin aiki ga masu rike da sarautun gargajiya. Littafin wani jagora ne da zai koyar da dukkanin masu rike da sarautun gargajiya yadda za su tafiyar da ayyukansu.
Lokacin da yake karin haske ga manema labarai game da rangadin da Sarkin ya yi a kananan hukumomi guda ukun, dan Majen Kano Alhaji Munir Sanusi ya bayyana cewa, a lokutan baya sarakai suna fita irin wanann rangadi ne don su karbi haraji.
“A lokutan baya sarakuna suna fita ranagdi ne don su karbi haraji. Sai dai yanzu abin ya canza, domin sukan yi irin wanann fita ne don a samu sanin juna tsakanin Sarki da talakawansa, musamman ganin cewa a wannan shi ne lokaci na farko tun hawan sarkin kan karagar mulki, haka kuma irin wanann fita takan bai wa sarakuna damar sanin halin da yankunan masarautarsu take ciki. Wannann yakan sa talakawa farin ciki, ganin cewa sun hadu da sarki ido da ido,” inji shi.