Yadda Sarkin Jere Sa’ad Usman ya rasu
Alamu na nuna cewa jinyar da ta yi ajalin Sarkin Jere Dokta Sa’ad Usman ta samo asali ne daga wani hari da aka kai mashi shekara shida da ta wuce. Bayanan da jaridar Daily Trust ta tattara sun nuna cewa marigayin ya sha fama da jijjiga sakamakon raunin da ya yi bayan da wasu jama’a […]
Alamu na nuna cewa jinyar da ta yi ajalin Sarkin Jere Dokta Sa’ad Usman ta samo asali ne daga wani hari da aka kai mashi shekara shida da ta wuce.
Bayanan da jaridar Daily Trust ta tattara sun nuna cewa marigayin ya sha fama da jijjiga sakamakon raunin da ya yi bayan da wasu jama’a a yankin suka dira a kanshi a shekarar 2014.
Wata majiya a cikin iyalinsa ta bayyana cewa har Birtaniya sai da jinya ta kai Sarkin, kuma shekara shida da wata uku ke nan cif da dawowarsa gida Najeriya.
Ranar Laraba ne dai wani kanin Dokta Usman din, Aminu Jere, ya sanar da rasuwar marigayin.
“Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun. Yanzun nan na yi rashin dan uwana Sarkin Jere, Dokta Sa’ad Usman”.
Wani da ga marigayin, Adamu Ibrahim Jere, ya tabbatar wa wakiliyar Daily Trust a Kaduna cewa Dokta Usman ya rasu ne da misalin karfe 2.00 na tsakar daren Talata.
“Ranar Talata ciwon ya tashi, amma tsakanin karfe 5.00 zuwa 6.00 na yamma ya samu sauki, har ma ya warware kusan karfe 7 na dare. Amma kusan karfe 2.00 rai ya yi halinsa”, inji Adamu.
Dokta Usman, wanda ya rasu yana da shekara 70 a duniya, miji ne ga tsohuwar Ministar Kudi a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, kuma tsohuwar ’yar Majalisar Dattawa, Esther Nenadi Usman.
Ya kuma taba rike manyan mukamai a gwamnatin Jihar Kaduna, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jiha.