Yadda Sarkin Kagoro ya sa mutanensa biyan diyyar shanun da aka sa masu guba

Sarkin Kagoro da ke Kudancin Jihar Kaduna, Mista Ufuwai Bonet ya dakile aukuwar rikicin da ka iya tasowa a tsakanin wani makiyayi da wadansu matasa da ke yankin bayan da suka kashe masa shanu ta hanyar sanya musu guba a wurin kiwonsu. Sarkin na Kagoro (Oegwom Oegworok) Mista Ufuwai Bonet ya dakile rikicin ne ta […]

Yadda Sarkin Kagoro ya sa mutanensa biyan diyyar shanun da aka sa masu guba

Sarkin Kagoro da ke Kudancin Jihar Kaduna, Mista Ufuwai Bonet ya dakile aukuwar rikicin da ka iya tasowa a tsakanin wani makiyayi da wadansu matasa da ke yankin bayan da suka kashe masa shanu ta hanyar sanya musu guba a wurin kiwonsu.

Sarkin na Kagoro (Oegwom Oegworok) Mista Ufuwai Bonet ya dakile rikicin ne ta hanyar tilsata musu biyan diyyar Naira miliyan daya da rabi a ranar Asabar din makon jiya. 

Sarkin Kagoro da Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta karamar Hukumar kaura da Bafulatanin da abin ya faru da shanunsa da Mai martaba Sarkin Jama’a wanda Sarkin Gandun Jama’a ya wakilta da wata kungiyar Dattawa ta Jihar Kaduna suka gana suka yanke wannan hukunci a zaman da suka gudanar a garin Kagoro da ke karamar Hukumar kaura da ke Jihar Kaduna.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi masarautar ta Kagoro domin jin ta bakin Sarkin, an shaida mata cewa Sarkin yana fama da wani uzuri, amma ya wakilta Wazirin Kagoro, Mista Dabid Peter don yin magana a madadin masarautar.

Wazirin Kagoro Dabid Peter, wanda da shi aka yi ta fadi-tashi a kan lamarin, ya ce da farko an yi ta kokarin boye wa masarautar abin da ya faru. Domin bayan faruwar lamarin Bafulatanin ya je wurin mai unguwar da abin ya faru ya shaida masa inda aka kira matasan da ake zargi da sanya gubar da ta yi sanadiyyar mutuwar shanun. Wazirin ya ce daga nan sai aka kai maganar wurin sojoji da Sarkin Kagoro ya ji ne ya ce lallai sai wadannan matasan sun biya Bafulatanin kudin shanunsa da suka jawo masa hasara.

Ya ce mai shanun ya bukaci a biya shi Naira miliyan daya da rabi a mutunce saboda ya ga kokarin da Sarkin yake yi a kai. “Da sarkin ya ga matasan ba su da karfin biyan kudin sai lamarin ya zama na kowa da kowa inda ya sa aka harhada kudin aka taru a wancan makon aka biya Bafulatanin wanda jin dadin abin da aka yi masa ne ya ce ya yafe Naira dubu 500, kuma nan take aka ba shi Naira miliyan daya da dubu 51,” inji Wazirin Kagoro.

Mista Dabid ya ce su a Masarautar Kagoro suna zaman lafiya da Fulani tuntuni in ban da abubuwan da suka faru a rikicin zaben shekarar 2011 da ya mamaye kusan ko’ina a kudancin Kaduna. “Ko a lokacin ma Mai martaba Sarki ya ce kada wani Bafulatani da ke masarautarsa ya ce zai gudu ya bar kasar Kagoro amma ya ce duk wanda ya ga hankalinsa ba kwanta ba, ba zai hana shi barin yankin ba. A lokacin duk wanda ya yi niyyar tafiya Sarki kan sa a yi masa rakiya har zuwa kan iyakan masarautar sannan a mika shi ga masarauta ta gaba.” inji shi.

A karshe Wazirin ya yi kira ga manoma da makiyaya su zauna lafiya da juna domin dukansu abokan hulda ne tuntuni.

Sarkin Hausawan Kagoro kuma Dagacin Unguwar Hausawan Kagoro, Malam Sunusi Babaji Muhammed, wanda shi ne ya fara kawo shawarar bai wa Fulanin wani abu don rage musu hasara a wani zama da suka gudanar da sojoji ya shaida wa Aminiya cewa dole ne a yi wa tufkar hanci tunda an riga an samu matsala. “Ganin irin hasarar da Fulanin suka yi kuma da alama babu niyyar ba su wani dan ihsani sai nan take na mike a wurin na bayar da gudunmawar Naira dubu 30, hakan sai ya burge shugaban sojojin sai aka umurci ’yan Gundumar Kpak, inda abin ya faru daga nan dai da aka ga ba su da hali

sai suka yanke cewa za su bayar da Naira dubu 30 su ma daga unguwar. Su ma matasan da suka taba yin ikirari aka nemo su aka yanke musu naira dubu ashirin-ashirin. Ganin irin yunkurin da aka yi ne sarkin Kagoro ya ji dadi ya ce lallai sai an san yadda aka yi aka biya wannan kudi, shi ne a karshe dai ya buga wa ’yan siyasar yankin waya kamar dan Majalisar Wakilai daga karamar Hukumar kaura Honorabul Gideon Goni da Shettiman Kagoro kuma Sanatan Kudancin Kaduna danjuma La’ah suka bayar da gudunmawarsu,” inji Dagacin.

Dagacin ya ce lallai suna zaman lafiya da Masarautar Kagoro sannan zamantakewarsu na dada kyutata a tsakani, inda ya yi kira ga manoma da makiyaya su rungumi juna su zauna lafiya domin ba za a taba raba manoma da makiyaya ba wadanda tun asali an san su tare, “Don haka duk wanda aka keta masa haddi ya yi kokari ya kai kara kada ya ce zai dauki doka a hanunsa,” inji shi.

Sarkin Gandun Jama’a, Alhaji Sulaiman Isa da ya wakilci Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammad II ya ce sun halarci taron biyan diyyar da Sarkin Kagoro ya jagoranta a masarautarsa ce bayan samun takarda daga wata kungiya ta Dattawan Jihar Kaduna don zama shaida a kan abin da ya faru da kuma irin kokarin da Sarkin ya yi na tilasta biyan diyyar. “Babu shakka irin wannan yunkuri daga shugabannin al’umma abin a yaba ne, idan ana samun haka daga wajen sarakuna da sauran shugabanni, dole mabiya su yi ladabi,” inji shi.

A karshe Sarkin Gandun ya yi kira ga manoma su daina toshe labin shanu kamar yadda ya yi kira ga makiyaya su daina cinye wa manoma amfanin gonarsu domin kowa ya zauna lafiya.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Shugaban kungiyar Miyetti Allah na karamar Hukumar kaura, Ardo Salisu Ibrahim wanda aka fi sani da Ardo Hari, ya jinjina wa Sarkin Kagoro, Mai martaba Ufuwai Bonet kan irin kokarin da ya yi game da wannan lamarin, “Ba mu taba zaton haka ba, duk da cewa mun san ba mu da matsala da sarakunan Kagoro da Moroa da Takad da ke karamar Hukumar kaura ba. Amma abin da Sarkin Kagoro ya yi abin a jinjina masa ne. Muna zaman lafiya da sarakunan in ban da ’yan matsalolin da muke samu a tsakanin da wadansu matasan yankin Kagoro,” inji shi.

Shugaban ya ce suna yawan samun matsalar sanya wa dabbobinsu guba a wuraren kiwo, wanda hakan ke janyo musu asarar shanu a yankin inda ya ja hankalin manoma da makiyaya da su kiyaye da hakkokin junansu. “Kamar yadda shanu suke da muhimmanci a wajen Bafulatani haka amfanin gona yake da muhimmanci ga manomi. Don haka ina kira ga ’yan uwana makiyaya su daina saka kananan yara da ba su wuce shekara 10 zuwa 15 suna kada dabbobi masu yawa kiwo ba, ta yadda za su rika shiga cikin gonakin mutane suna ci musu amfanin gona. Haka su ma manoma bai kamata su rika toshe wa makiyaya hanyoyinsu da aka sani ba, kowa ya kiyaye hakkin dan uwansa,” inji shi.

Daga ya yi kira ga ’yan uwansa makiyaya su dawo mahaifarsu su ci gaba da kiwo tunda an samu zaman lafiya a yankin.

Yadda lamarin ya faro – AhmaduMada

daya daga cikin masu shanun da aka hallaka mai suna Malam Ahmadu Made ya bayyana wa Aminiya cewa “Shanun da aka hallaka namu ne na gado mu zuriyar tsohon Sarkin Fulani Ma’adam, wanda shi ne Sarkin Fulanin Kagoro na farko. Muna zaune a nan kusan shekara 200 kuma ba mu taba samun matsala da kowa ba. Mun gaji shanun ne tare da filayenmu tun iyaye da kakanni.” 

Ahmadu Mada ya ce sai bayan rikicin shekarar 2011 suka fara samun tsangwamar da ta kai suka bar yankin zuwa Ladduga a Kachiya, kuma bayan sun dawo da wasu dabbobin sai ga shi har kashe su ake yi ta hanyar zuba musu guba a wuraren kiwonsu ba sau daya ba sau biyu ba.

“Wannan matsalar ta faro ne tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairu inda aka hallaka mana shanu sama da talatin ta hanyar sanya musu guba. Abin da ya ta da mana hankali shi ne akwai wani matashi da ya taba yi mana ikirari cewa da gubar Naira dari zai iya hallaka mana shanu, kuma ba a fi mako guda ba muka ga shanun sun fara mutuwa, shi ne muka sanar da hukuma da shugabannin al’umma,” inji shi.

Ya ce da farko in sun sanar da masarauta takan ce su koma wajen masu unguwanni da dagatai ne a sasanta amma abin yakan ci tura. “Yanzu mu ba biyan diyyar ce kawai damuwarmu ba, yadda za a magance ci gaba da faruwar hakan domin zaman lafiya ne babban abin da ya fi damunmu,” inji shi.

Ya jinjina wa Sarkin Kagoro bisa hobbasar da ya yi a wannan karon ganin abin ya yi yawa kada ya haifar da wata matsala.

Ahmadu Mada ya kuma nuna damuwa kan yadda tun kafin a gama biyan diyyar shanu 30 din aka sake kashe wasu guda 19 da guba, kuma ya koka kan yadda wadansu a yankin suka mamaye musu filayensu na gado.

A karshe yayi kira ga gwamnati ta shigo cikin lamarin sosai idan ba a daina sanya wa shanunsu guba suna kashewa ba, domin ta rika kama duk wanda ke aikata irin haka ana hukunta shi saboda zama darasi ga wadanda ba sa son zaman lafiya. “Tunda yanzu abin da ake amfani da shi ke nan a ko’ina maganar makiyaya da manoma,’ inji shi.