Yadda saurayi ya kashe buduwarsa da danta saboda gardamar talabijin
Jami’an tsaro sun tsare Tyrone Terell Johnson dan shekara 42 a jihar Tedas da ke Amurka saboda laifin kashe buduwarsa da danta dan shekara 10 wanda ya ce matar ta wulakanta shi saboda canza tashar talabijin. Wani jami’in sojan ruwa ne ya kira hukumar ‘yan sanda bayan kisan mutum biyun da aka yi. Rahotan dai […]
Jami’an tsaro sun tsare Tyrone Terell Johnson dan shekara 42 a jihar Tedas da ke Amurka saboda laifin kashe buduwarsa da danta dan shekara 10 wanda ya ce matar ta wulakanta shi saboda canza tashar talabijin.
Wani jami’in sojan ruwa ne ya kira hukumar ‘yan sanda bayan kisan mutum biyun da aka yi.
Rahotan dai na bayyana cewa, ana zargin Johnson da kisan gilla ta hanyar harbin mutum biyu a cikin gidansu. ‘Yan sandan sun shiga gidan da aka yi kisan ne, inda suka samu gawar Stephanie Ann Willis da danta Ricky Willis, rahotan na bayyana cewa, an kashe su ne saboda rashin amincewar Johnson na canza tashar wasan kwallon kafa da suke kallo a talabijin.
Johnson da ake zargi da kisan mutanen biyu, kafin ya aikata laifin budurwar tasa ta fara yi masa gardama har sai da ya fusata ya yi yunkurin kwashe kayansa don yin kaura daga gidan da suke zaune. Duk da haka Johnson ya ce Stephanie, tai ta binsa tana furta masa kalamai da zasu bata masa rai sanadiyyar gardamar.
Rahotan ya kara da cewa, Johnson ya harbe Stephanie lokacin da take rike da na’urar canza tashoshin talabijin a hannunta.
‘Yan sandan dai sun shiga dakin da Johnson ya yi kisan, inda suka same su cikin jini. A yanzu haka dai Johnson na tsare a hannun hukumar ba a bayar da belinsa ba.