Yadda sauye-sauyen CBN suka ceto Naira

Kamfanin Dillacin Labarai na Rueters ya ce, karuwar kudin lamuni (bond) na Amurka da cirarwar Dalar Amurka suna tayar da kurar da ke barazana ga kasuwanni masu tasowa a bana. Kuma suna nuna tsuke halin da kudi ke ciki a kashin kansu kuma suna iya jawo karuwar asara ga kadarori da kasuwannin. Kuma su biyun […]

Yadda sauye-sauyen CBN suka ceto Naira

Kamfanin Dillacin Labarai na Rueters ya ce, karuwar kudin lamuni (bond) na Amurka da cirarwar Dalar Amurka suna tayar da kurar da ke barazana ga kasuwanni masu tasowa a bana. Kuma suna nuna tsuke halin da kudi ke ciki a kashin kansu kuma suna iya jawo karuwar asara ga kadarori da kasuwannin. Kuma su biyun suna iya jawo babbar illa ga guguwar saye da sayarwa. Cibiyar Kudi ta Duniyan (IIF) a baya-bayan nan ta ce karuwa a cikin shekara 10 kan lamunin na Amurka ya samu ribar kashi 3 cikin100, kuma harin mamaya da Dalar Amurka ta samu ya kawo nakasu ga bunkasar kasuwanni masu tasowa, lamarin da ya jawo “koma-baya.”

Koma-bayan  tana iya karuwa, kamar yadda Cibiyar IIF ta ce, tana faruwa ce sakamakon karuwar kudin ruwa kan lamunin ajiya na Amurka.

Rahoton ya kara da cewa a tsakanin watannin Janairu zuwa na Satumba, darajar takardun kudaden wasu kasuwanni masu tasowa a kasashe hudu sun zube da akalla kashi 20 cikin 100 idan aka kwantantasu da Dalar Amurka.

Darajar  kudin Peso na Ajantina ta zube da kashi 12 a  makonni biyu da suka wuce, inda aka rika sayar da Dalar Amurka 1 a kan Peso 41.  Hakan ya faru ne duk da yunkurin da Babban Bankin kasar ya rika yi na kara kudin ruwa da  kashi 60 cikin 100 don dakile faduwar darajar kudin da kuma hana muguwar hauhawar farashin kayayyaki.

Faduwar darajar takardun kudin ta faru kwana daya bayan kasar ta nemi Asusun  Lamuni na Duniya (IMF)  ya ranta mata Dala biliyan 50 a matsayin rance ceto da asusun ya riga ya amince da shi.

Kafin Asusun IMF ya amince da wannan bashi, kasar ta amince ta rage gibin kasafinta daga kashi 2.7 a bana daga kashi 3.9 da ta samu a 2017.  Sai dai duk da haka matakin bai yi wani tasiri ba, ganin yadda darajar Peso ta fadi da kashi 45 cikin 100 idan aka kwantanta da Dala daga bara zuwa yanzu.

Kasuwanni masu tasowa sun ci gaba da shiga tasku sakamakon faduwar darajar kudin Turkiyya wato Lira da na Indiya Rupee zuwa matakin mafi karanci a kan Dala, Rupee ya fadi da kashi 11 cikin 100 tun farkon bana.

Wannan matsala ta haifar da hauhawar farashin kayayyaki a wasu kasashe da kuma jawo gibi kan kasafin kudi a wasu kasashen da kuma karuwar bashi cikin Dala, a matsayin dakile ci gaban kudin shigar kasa (GDP) ga kuma  takaddamar kasuwanci a tsakanin Amurka da China, sai  tasirin harkokin kasuwanci, amma Najeriya a nata bangare ta aruirita ta kauce wa matsalolin da suka taso wa kasuwanni masu tasowa, sakamakon daidaituwar darajar Naira da kuma ba baki ’yan kasashen waje damar su higa su fita ta hanyar kasuwanci na I&E.

Wadannan nasarori Najeriya ta same su ne a dalilin matakan da Bankin CBN ya rika dauka a ’yan shekarun baya duk kuwa da irin matsalolin da wasu kasashe suka rika fuskanta na faduwar darajar kudinsu amma Naira ta ci gaba da samun tagomashi da hakan ya sa aka rika rububin masu son zuba jari a kasar nan.

Misali, abin da ke sanya Gwamnatin Tarayya ta bunkasa tattalin arzikinta yanzu a wannan lokacin, mafi karanci rahoton asusun ajiye kasar ya kai kashi 14.03 cikin 100 wanda a yanzu haka ya haura.

Adadin kudin shigar kasar da ake samu wata hanya ce da kasashe suka bi kamar su: Ajentina da Turkiyya da Afirka ta Kudu da Brazil da Meziko da Masar da Koriya ta Kudu da Philippines da kuma China, a fannin adadin kudin shigar da gwamnati take samu.

Kudaden da aka lissafo na bayyana saurin samun hauhawar tattalin arzikin kasa a makonnin da suka gabata duk da daidaituwar darajar Naira.

A cewar wani mai nazari na FdTM, Lukman Otunuga, a lokacin da ake samun turjiya a fannin kasuwanci tsakanin kasashe biyu masu karfin tattalin arziki zai sanya kasashe da dama cikin zullumi wajen bai wa kamfanoni kwarin gwiwa.

Otunga ya bayyana shakkunsa a kan yadda ake gasar bunkasa harkokin kasuwanci a duniya da kuma samun nakasu a fannin ci gaban tattalin arziki lura da yadda kasuwar take cikin yanayi

“A rubu’in shekarar 2018, Najeriya ta kasance da ci gaba rike da kambun rashin bashi da karuwar kudin shiga da kashi 1.5 cikin 100 na rubu’in shekara hauhauwar farashin ya kai kashi 11.14 cikin 100. Duk da kudin ajiyar kasashen ketare ya yi kasa a watan Maris da Dala biliyan 45 amma ana iya amfana a hakan.

“Farashin mai ya samu karfin gwiwa sakamakon fannin siyasa yayin da darajar Naira take dada tasowa idan aka kwatanta da darajar Dala wanda hakan na kara wa kasar kwarin gwiwa. Akwai shakkun yadda darajar Naira take idan aka kwatanta ta da Dala, da karuwar samun kudin ruwa da fargabar da ake yi na farfadowar tattalin arzikin da aka samu,” kamar yadda Otunuga ya bayyana.

Shugaba Buhari wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya wakilta a wurin taron a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka, ya ce akwai babban nauyin da ke kan Najeriya game da samar da kungiyar gamayya ta sanya ido. Buhari ya ce, “Ina tabbatar muku cewa Najeriya za ta ci gaba da jajircewa ga ajandar nagarta da kuma ci gaba mai dorewa a yankinmu da dukan nasarorin inganta rayuwar dukan al’ummar ECOWAS baki daya.

“A yayin iyar da wannan buri cikin kyakkawan tsari, Najeriya za ta ci gaba da tabbatar da cewa an gina tattalin arzikinmu bisa nagarta da kuma dabarun cimma nasara mai dorewa, sannan za ta yi la’akari da sake fasalin WAMI a cikin hukumar.  Wannan kuma abu mai wahalar gaske, saboda tsarin hade cibiyar Sanya Ido ta Afirka ta Yamma, (WAMI) da kuma (WAMZ) ga Hukumar ECOWAS za ta bar WAMZ ne ba tare da zauren da zai rika musayar ra’ayoyi da tattauna batutuwan da suka shafi alfanun kasashe masu magana da Ingilishi a ECOWAS.”

Shugaban kasar ya ce, babu batun kin yarda da yawan kudin da ake bukata wajen aiwatar da hakan, an yi amfani da lokaci da kokari wajen ci gaba da bibiyar ajandojin nagartar yankin. Ya ce wannan zai tabbata ne ta hanyar cimma manufofi da tsare-tsaren kungiyar gamayya ta sanya ido nan da 2020. “Saboda haka haduwarku a nan ya yi ma’ana a daidai lokacin da ya rage saura watanni 18 a samar da takardun kudi na bai-daya na ECOWAS. “Mambobin wannan majalisa kamar yadda tattaunawarku ke ci gaba da gudana ta fuskar kaddamar da kungiyar gamayya ta sanya ido na yankin, to kuna bukatar aza mahangarku ga yanayin da duniya ke kai da kuma kalubalen dake fuskantar yankunan da abun ya shafa.”

A daidai lokacin da ake samun komawa baya a kasuwanci, masana harkokin zuba jari a Meristem Securities Inbestment Limited suna ba masu zuba jari shawara su yi amfani da fadin farashi a matsayin hanyar fadada kasuwancinsu.

A cewar Meristem, ana samun ci gaban kasuwanci a ‘yan watannin da suka wuce, kuma matsalolin da ake fuskanta sun kusa wucewa, “Yadda farashin ke dagawa a kasuwar zuba jari, da alama akwai nasara nan gaba. Yadda farashin ya je kasa zai taimakawa ‘yan kasuwa wajen fadada harkokinsu, amma sai sun dage,” inji su.

Masanan sun ce zaben 2019 yana kawo matsala ga masu zuba jari, domin ya sa wadansu suna janye kudadensu, wanda hakan ke nufin akwai damar samun riba. “Mun yi imanin cewa bayan zaben 2019, za a samu daidato a kasuwa. Amma ya kamata a kasance cikin shiri kafin lokacin. Don haka me zai hana ka saya kayyayaki tun yanzu.?”

A karshen taron Kwamitin Bankuna a Legas, Daraktan Kula da Bankuna Malam Abdullahi Ahmed ya ce, “Duk da ana janye kudade a kasuwar zuba jari kuma ana samun koma baya, duk da haka janyewar ba ta kai yadda muke gani ba a kasuwanni masu tasowa, wanda hakan na nuna yadda aka amince da tattalin arzikin Najeriya. Har yanzu farashin gangar mai yana sama da Dala 70, kuma wasu abubuwa da ke faruwa a tattalin arzikin duniya za su taimaka wa farashin man.”

A jawabin, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na bankin Guaranty Trust Bank a wajen taron cewa ya yi kanana da matsakaita kasuwanci suna tafiya yadda ya kamata, tambayar kawai ita ce ta yaya za a ci gaba da fadada daga inda ake?