Yadda shari’ar Masarautar Kano ke gudana

An fara sauraron shari’ar cikin tsauraran matakan tsaro

Yadda shari’ar Masarautar Kano ke gudana

Babbar Kotun Jihar Kano ta fara sauraron shari’ar neman hana rushe sabbin masarautun Jihar Kano.

Kotun ta fara sauraron shari’ar ne cikin tsauraran matakan tsaro, makonni biyu bayan soke msarauun da kuma nasa Muhammadu Sanusi II a kan sarauyar Kano.

Jami’an hukumar tsaro ta DSS da ’yan sanda sun girke motocinsu a muhimman wurare gaban nin zaman kotun, domin tabbatar da tsaro da hana zirga-zirga mara dalili.

Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, ne ya shigar da karar neman hana gwamnatin Kano soke sabbin masarautun jihar guda biyar.

A ranar Litinin ya kamata yi zaman, amma yajin aikin kungiyar kwadago ya hana.

Mai kara na neman kotu ta soke nadin Sarki Muhammadu Sanusi II da aka yi bayan gwamna Abba ya sanya hannu  kan sabuwar dokar marautu da majalisar dokokin jihar ta yi wa gyaran fuska.

Bayan sauraron karar ne Mai Shari’a Muhammad Liman ya ba da umarnin hana sauke Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da kuma nada Sarki Sanusi II.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta