Yadda Shekau ya zama mai rai da yawa
An samu rudani a batun kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, inda sojojon Najeriya ke cewa sune suka kashe shi , su kuma sojojin kasar Kamaru suka ce sune suka kashe shi, sai kuma wani dan jarida da ke yawan tuntubarsu ya fito ya nuna cewa Shekau na nan da ransa.Sojojin kasar Kamaru sun ce […]

An samu rudani a batun kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, inda sojojon Najeriya ke cewa sune suka kashe shi , su kuma sojojin kasar Kamaru suka ce sune suka kashe shi, sai kuma wani dan jarida da ke yawan tuntubarsu ya fito ya nuna cewa Shekau na nan da ransa.
Sojojin kasar Kamaru sun ce sun kashe Shekau ne a wata maboyarsa yayin wani artabu da suka yi da ‘yan Boko Haram a Ngala da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru lokacin da ‘yan Boko Haram din suke kokarin tsallakawa cikin kksar Kamaru. Har ma suka nuna hoton wani mai gemu suka ce shi ne Shekau din.
Ita kuma hedkwatar tsaro ta Najeriya da farko ta nuna cewa sojojin Najeriya sun kashe Shekau, sai kuma aka sake bayyana cewa wani mutum ne aka kashe a Konduga da suka gano shi ne yake fitowa a matsayin Shekau din saboda ya yi kama da shi.
Shi kuma Ahmed Salkida, wani dan jarida dan Najeriya da ke zaune a Dubai da aka sanshi da kokarin ganawa da shugabannin kungiyar Boko Haram, ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne labarin da ake yadawa cewa sojoji sun kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau, inda ya nuna cewa yana nan da ransa lafiya lau, kamar yadda bincikensa ya tabbatar.
Salkida, wanda ya yi wannan bayanin a shafinsa na tiwita, ya kuma karyta labarin da ke nuna cewa gwamnatin Najeriya na tattaunawa da ‘yan Boko Haram domin a sako mata ‘yan makaranta fiye da 200 da suka yi garkuwa da su kwanaki 165 da suka gabata a cikin watan Afirilu, a Chibok ta jihar Borno.
Haka kuma dan jaridan ya ce ba gaskiya ba ne labarin da ke nuna cewa kungiyar agaji ta Red Cross tana kokarin shawo kan ‘yan Boko Haram din domin su sako ‘yan matan, su kuma a saki wadansu mutanensu da jami’an tsaron Najeriya suke tsare da su.
Tun da farko dai jami’an tsaron Najeriya sun nuna cewa an kashe Shekau, sai kuma suka ce sun kashe wani wanda ya yi kama da Shekau yake fitowa da suna shi ne Shekau din, da suka ce sun gano ainihin sunan wanda aka kashen shi ne Muhammad Bashir.