Yadda Shilpa Shukla ta samu daukaka a fina-finan Indiya
Shilpa Shukla ta kasance daya daga cikin mata ’yan fim masu tashe a Indiya. Ta samu daukaka a duniyar fina-finai a sakamakon yadda take maida hankali da jajircewa wajen aikin da aka ba ta a fim.An haife ta ne a gidan iyalan Bihari Bhumihar Brahmin da ke garin baishali. Ta taso ne a biranen New […]

Shilpa Shukla ta kasance daya daga cikin mata ’yan fim masu tashe a Indiya. Ta samu daukaka a duniyar fina-finai a sakamakon yadda take maida hankali da jajircewa wajen aikin da aka ba ta a fim.
An haife ta ne a gidan iyalan Bihari Bhumihar Brahmin da ke garin baishali. Ta taso ne a biranen New Delhi da Kolkata da kuma Gujarat. Ta yi karatunta na farko a Delhi Public School da Kwalejin P.K. Puram da ke birnin New Delhi, daga bisani kuma ta halarci Jami’ar Miranda House duk a birnin na New Delhi.
Shilpa ta fara fim ne a kamfanin M. K. Raina, daga bisani kuma ta koma aiki tare da darakta Arbind Gaur na kamfanin shirya fim na ‘Asmita Theatre.’ Wasu daga cikin fina-finanta a kamfanin sun hada da ‘Final Solutions’ na Mahesh Dattani da ‘Tara.’ Akwai kuma fim din da Gobind Deshpande ya shirya da ta fito a ciki, wato ‘Antim Diwas.’ Akwai fim din ‘Ek Mamooli Aadmi’ wanda Ashok Lal ya shirya. Ga fim din ‘Rakt Kalyan’ wanda Girish Kamad ya shirya. Daga nan kuma sai fim din da Neil Simon ya shirya, mai suna ‘Log-Baag.’
A 2003, ’yar fim din ta turza sosai, a lokacin da ta fito cikin fim din ‘Khamosh Pani.’ Ta kuma fito a cikin fim din Sudhir Mishra mai suna ‘Hazaaron Khwaishein Aisi’ wanda shi ma ya fito a 2003. Fim din da ya kara daga mata likkafa, shi ne ‘Chak De India’ inda ta fito a matsayin tsagera. Fim din, Shahrukh Khan ne ya shirya shi kuma ya fito a 2007. Ta samu kulawa sosai da fim din, inda ta shiga sahun wadanda aka tace domin cin gasar Filmfare, sannan kuma ta shiga sahun mutanen da aka tantance domin ba su lambar gimamawa ta kasa. Haka ma fim dinta da ke kan fitowa, ‘B. A. Pass’ wanda darakta Ajay Bahl ya bayar da umurni ya samu kyauta a bikin nuna fina-finai na SAAFF da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa. Haka kuma a 2012, an zabi wannan fim a gasar fina-finan Indiya ta ‘Cinefan Film Festibal.’