Yadda shirin gwamnati na kafa Ruga ke shan suka da yabo

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana bullo da shirin Ruga da niyyar kakkafa rugage a sassan kasar nan a kokarinta na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya. Wannan mataki yana samun suka da yabo, inda gwamnonin wasu jihohi suka amince wadansu kuma suka ce atafau ba za a yi wannan tsari a jihohinsu […]

Yadda shirin gwamnati na kafa Ruga ke shan suka da yabo

Wadansu matasan Benuwai suna zanga-zangar adawa da samar da Rugar kiwo a jiharsu.

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana bullo da shirin Ruga da niyyar kakkafa rugage a sassan kasar nan a kokarinta na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya. Wannan mataki yana samun suka da yabo, inda gwamnonin wasu jihohi suka amince wadansu kuma suka ce atafau ba za a yi wannan tsari a jihohinsu ba.

Wannan dais hi ne shiri na uku da wannan gwamnati ta yi yunkurin gabatarwa don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya amma wadansu suna sa kafa suna shurewa.  A karon farko gwamnatin ta bayyana shirin kakkafa manyan wuraren kiwon shanu na zamani (Ranches) inda ta gamu da turjiya daga wasu sassan kasar nan. Daga nan ta bayyana bullo da tsarin manyan makiyaya (Colonies) nan ma wadancan rukunin mutane suka ja daga, kafin ta canja zuwa shirin Ruga wanda shi ma ya hadu da irin waccan turjiyar.

Akasarin jihohin da suke adawa da wadannan tsare-tsare suna nuna cewa babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta kwace filayen mutanen jihohinsu domin bai wa Fulani su zauna koda kuwa akwai Fulanin zaune a jihohin a halin yanzu. Sai kuma wadansu masu da’awar kare kabilu ko yankunansu da suka fi babatu da nuna turjiya da duk wani shiri da ya shafi harkar kiwo.

Jihohi 12 da suka amince za su bayar da filayen yin Rugar sun fito ne daga Arewa wato Adamawa da Sakkwato da

Kaduna da Kogi da Nasarawa da Kebbi da Taraba da Kastina da Zamfara da Neja da Filato da Bauchi.

Jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da wasu a Arewa ta Tsakiya ne ke adawa da shirin Ruga. Kuma an ruwaito Gwamnan Jihar Ebonyi kuma Shugaban Majalisar Gwamnonin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu yana cewa, babu filin da za su bayar don yin Ruga, kuma abin da kawai zai shiga tsakaninsu da Fulani makiyaya shi ne cinikin ba-ni-gishiri-in- ba- ka- manda, inda Fulanin za su rika kai musu shanu ko nama su kuma suna sayo ciyawar da Gwamnatin Tarayya za ta inganta samarwa a yankinsu

Kungiyar Shugabannin Kudu da na Midil Belt ce kungiyar da ke kan gaba a adawa da shirin inda ta bakin wakilanta da suka hada da Yinka Odumakin (Kudu maso Yamma) da Chigozie Ogbu (Kudu maso Gabas) da Bassey Henshaw (Kudu maso Kudu) da kuma Isuwa Dogo (na Midil Belt) suka ce shirin Rugar wani yunkuri ne “na yin mulkin mallaka ga sauran sassan Najeriya.”

Sun ce kiwo harka ce ta “kashin kai” da bai kamata gwamnati ta shiga ciki ba, inda suka yi barazanar cewa al’ummarsu za su kare kasarsu daga yi musu mulkin mallaka a karkashin shirin gwamnati na mamaya.

Sai dai a bangaren makiyaya da masana harkar kiwo sun nuna damuwa ne kan yadda Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin da suka amince da tsare-tsaren suka kasa fara gudanar da su a aikace. Sun ce in da gaske gwamnati take yi ya kamata ta fara aiwatar da shirin a jihohin da suka amince da shirin, maimakon barin shirye-shiryen a takarda.

 

A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.