Yadda Shirin Labarina Ke Jan Miliyoyin ’Yan Kallo

Miliyoyin mutane kan kalli shirin ta talabijin a gidajensu ko gidajen kallo ko shagunan ’yan kasuwa da ke kamo shirin domin nishiadi.

Yadda Shirin Labarina Ke Jan Miliyoyin ’Yan Kallo

Labarina shirin Kannywood ne mai dogon zango, kuma daya daga cikin fina-finan Hausa mafiya tashe a wannan lokaci.

Yadda aka tsara labarin da zubin jarumansa da kuma yadda suke taka rawar da aka ba su da naga cikin abubuwan da ke kayatar da masu kallo.

Ana iya cewa shirin Labarina ya zama ruwan dare gama duniya, saboda yadda masu kallo suka karbe shi musamman a gidajensu a Arewacin Najeriya da ma kasashen waje.

Miliyoyin mutane kan kalli shirin ta talabijin a gidajensu ko gidajen kallo ko shagunan ’yan kasuwa da ke kamo shirin domin nishiadi. Baya ga haka akwai miliyoyin jama’a da ke kallon shirin a YouTube.

Darakta a Kannywood, Aminu Saira, wanda ya lashe lambobin yabo akalla guda uku, shi ne ya tsara kayataccen shirin.

Labarina, wanda Sumayya (Nafisa Abdullahi) ke be ba da labarin rayuwarta, na  dauke da labarin soyayya da zamantakewar iyali da al’adun bahaushe, ya hada da jarumai matasa da masu tasowa, wadanda masu kallo suke kauna.

Uwa uba! akwai kuma taurari irinsu Sadiq Sani Sadiq, Nafeesat Abdullahi, Alhasan Kwalle, Naziru M. Ahmad Sarkin Waka, da sauransu.

Daga bisani an maye gurbin Nafeesat Abdullahi da wata jaruma, Fati Washa, a matsavin Sumayya a shirin.

Sauya Summayyar ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masu kallo, inda wasu ke nuna rashin jin dadinsu, wasu nuna na nuna farin cikinsu game da hakan.

Amma duk da haka, sauyin ’yar wasar da ke jan shirin Labarina, hakan bai hana shi ci gaba ba jan zarensa ba tare da wata tangarda ba.

A zango na tara (9) da aka shiga yanzu, an shiga ba da kayatacen labarin Maryam (Fatima Hussein)

A tashar Arewa24 ake haska shirin da karfe 9 zuwa 10 kowace ranar Laraba, kuma yana cikin fina-finan Kannywood da aka fi kallo a halin yanzu.

Hakalazika shirin ya abin abin tattaunawa a kafofin sada zumunta.