Yadda Shugaba Buhari ya rage wa gwamnoni karfi

Gazawar gwamnoni wurin ceto takwaransu na jihar Edo, Godwin Obaseki daga guguwar da ta hana shi shiga takarar zaben dan takara a jam’iyyar APC, da sauyin shekarsa zuwa jam’iyyar PDP alama ce ta cewar Shugaba Buhari ya rage karfin ikon gwamnoni a Najeriya. Ya kuma kara tabbatar da dakushewar karfin kungiyoyin da gwamnoni ke amfani […]

Yadda Shugaba Buhari ya rage wa gwamnoni karfi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Gazawar gwamnoni wurin ceto takwaransu na jihar Edo, Godwin Obaseki daga guguwar da ta hana shi shiga takarar zaben dan takara a jam’iyyar APC, da sauyin shekarsa zuwa jam’iyyar PDP alama ce ta cewar Shugaba Buhari ya rage karfin ikon gwamnoni a Najeriya.

Ya kuma kara tabbatar da dakushewar karfin kungiyoyin da gwamnoni ke amfani da su wajen magana da murya daya.

Idan aka waiwaya baya, gwamnoni sun ci karensu babu babbaka musamman ta yadda suke zabar mutanen da suke so domin wakiltar jihohinsu a mukamai da dama na siyasa ko a jam’iyyance ko a tarayyar kasar nan, kamar yadda tafiyar ta kasance a gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan da ta shude.

A wannan lokacin, Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi, babu hanyar da ba su bi ba ta ganin sun tseratar da Obaseki amma abun ya ki yiwuwa.

Akalla gwamnoni bakwai ne suka je wajen Uban Jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu domin ceto Obaseki, suka kuma tafi wajen Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole, kafin su je Fadar Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari amma abun ya ci tura. Aka kuma haramta wa Obaseki shiga zaben saboda matsalolin takardun shaidar karatunsa.

Ba kan Obaseki farau ba

Hakan shi ya tilasta wa Obaseki sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, lamarin da ya bar mutane cikin tunanin ko gwamnonin za su iya taimakon sa wajen lashe zabensa karo na biyu a karkashin jam’iyyar PDP.

Sai dai kuma Obaseki ba shi ne mutum na farko da aka taba yi wa haka ba. Tsohon Gwamnan Jihar Legas Akinwumi Ambode ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayin sakamakon sabanin da ya shiga tsakaninsa da Tinubu. Hakan ya sa ya rasa takararsa da zaben gwamna a karo na biyu, inda yaron mai gidansa Bola Tinubu ya kayar da shi a zaben fitar da gwanin jam’iyyar ta APC.

A shekarar 1999 gwamnonin suka kirkiri kungiyar ta (Nigeria Governors Forum) wadda tsohon gwamnan Nasarawa, Abdullahi Adamu ya fara jagoranta, kuma sun yi amfani da ita wajen cimma kudurorinsu da dama. A tsawon shekaru 16 da PDP ta yi tana jan ragamar mulkin kasar nan, gwamnoni ke zabar ministocinsu da duk sauran manya-manyan mukaman Gwamnatin Tarayya. Hakan ya samu cikas a lokacin da aka rantsar da Shugaba Buhari.

Buhari ya dama wa gwamnoni lissafi

Bayan an rantsar da Buhari, ance gwamnonin sun same shi da sunayen wadanda suke so ya ba su ministoci, amma Buhari ya ce musu hakan ba hurumisu ba ne tun da shi ma ba shi ya zaba musu kwamishinonin da za su yi aiki da su a jihohinsu ba.

Masu fashin bakin siyasa sun ce wannan tamkar dan ba ne da Buhari ya dasa na rage wa gwamnonin karfin iko. Haka nan kasa cire shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomole da gwamnonin suka yi sakamakon mara masa baya da Tinubu ya yi ita ma wata manuniya ce.

Ra’ayoyin masana

A ra’ayin masu fashin baki kan hakan, Farfesa Sylvester Odion, na Shahen Koyar da Kimiyar Siyasa a Jami’ar Legas ya ce, a can baya gwamnonin sun yi amfani ne da saukin kai da sanyin hali na Shugaba Goodluck Jonathan suka yi abin da suke so.

Ya ce, shugaba Buhari ya yi amfani da karfin mulkinsa na shugaban kasa ya danne su, kuma ba za su iya tankwara shi ba saboda yawancinsu suna da irin nasu matsalolin.

Farfesa Yahaya Tanko Baba na Sashen Kimiyar Siyasa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto, ya ce karfin mulkin gwamnoni ya rage ne tsakanin 2015 zuwa yanzu.

Ya ce, hakan ya faru ne bayan Jam’iyyar APC ta kwace mulki hannun PDP sakamakon bangarewa da wasu gwamnoni biyar suka yi daga cikin jam’iyyar PDP.

Ya ce, tun daga wannan lokaci ne karfinsu ya ci gaba da dakushewa saboda tun da APC ta hau karagar mulkin kasa, hukuncin jam’iyya a ke ba muhimmaci ba gwamnoni ba.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara