Yadda shugaban majalisar dokokin Legas ya wawashe kudin majalisar -Shaidun EFCC
daya daga cikin shaidun hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annuti (EFFC) mai suna Adeniyi Adebayo ya bayyana wa babbar kotun tarraya da ke Legas yadda shugaban majalisar dokokin jihar, Mista Adeyemi Ikuforiji ya karbi makudan kudi daga majalisar ta hanyoyin da ba su dace ba.Hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban majalisar, Adeyemi Ikuforiji […]

daya daga cikin shaidun hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annuti (EFFC) mai suna Adeniyi Adebayo ya bayyana wa babbar kotun tarraya da ke Legas yadda shugaban majalisar dokokin jihar, Mista Adeyemi Ikuforiji ya karbi makudan kudi daga majalisar ta hanyoyin da ba su dace ba.
Hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban majalisar, Adeyemi Ikuforiji da mai taimaka masa na musamman, Oyebode Atoyebi a gaban kotu kan zargin karbar Naira miliyan dari shida ta hanyoyin da ba su dace ba, tsakanin watan Afrilun shekarar 2010 da watan Yulin shekarar 2011.
Adebayo ya shaida wa kotun cewa Atoyebi ya fada da bakinsa cewa ya karbi miliyoyin Naira daga asusun majalisar a madadin shugaban majalisar.
Ya ci gaba da cewa Atoyebi ya karbi kudi a madadin shugaban majalisar na azumin Ramadan da na odilan matarsa da na ofishin shugaban majalisar da na ayyukan yau da gobe da kuma kudin alawus na tafiye-tafiyen ’yan majalisar jihar.
Ya kara da cewa Atoyebi ya karbi kudin alawus na gidan shugaban majalisar da na gidan shakatawar shugaban majalisar da sauransu ta hanyar da ta saba wa doka.
Shi ma a tasa shaidar, Mista Godwin Obla ya ce kwamitin masu bincike sun sami bayani ne daga rajistar kudi ta majalisar dokokin jihar.
Hukumar EFCC ta ce yin hakan ya saba wa shashe na 18, karamin sashen na (a) na dokokin da suka hana almundahanar kudi ta shekarar 2011.
Lauyan da ke kare wadanda ake zargi, Mista Tayo Oyetibo ya bukaci kotun ta umarci EFCC ta bambance takardun shaidar don kada a bata lokaci.
Daga bisani sai alkalin kotun, Mai shari’a Buba ya bukaci masu gabatar da kara su tantance takardun shaidar don a gaggauta sauraron shari’ar.
Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 7 da 8 da kuma 10 na watan Janairun shekarar 2014.