Yadda shugabancin Mugabe ya kawo karshe bayan shekara 37 yana mulki
Babban Birnin Harare na kasar Zimbabwe ya cika makil da mutane, inda suke ta raye-raye domin nuna jin dadinsu bayan sanarwar cewa tsohon shugabansu Robert Mugabe ya yi murabus daga shugabancin kasar. Shi dai Mugabe ya kwashe shakara 37 yana mulkin kasar, kuma yanzu haka yana da kimanin shekara 93 a duniya. Tun samun ‘yancin […]

Babban Birnin Harare na kasar Zimbabwe ya cika makil da mutane, inda suke ta raye-raye domin nuna jin dadinsu bayan sanarwar cewa tsohon shugabansu Robert Mugabe ya yi murabus daga shugabancin kasar.
Shi dai Mugabe ya kwashe shakara 37 yana mulkin kasar, kuma yanzu haka yana da kimanin shekara 93 a duniya.
Tun samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka, Mugabe ne kadai ya ja ragamar shugabancin kasar har zuwa yanzu da ya yi murabus.
Ya fara ne a matsayin Firaminista, sannan daga baya ya zama Shugaban kasa, inda ya kwashe shekara 37.
Shi dai Mugabe ya kasance daya daga cikin na kan gaba wajen fafutukar kwato ‘yancin kai daga turawa, inda har