Shugabanni ke taimakon ’yan bindiga a Katsina — Radda
Gwamnan ya ce dole ne jama’ar gari su tashi tsaye don kare kansu daga ‘yan bindiga.
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana cewar hare-haren ’yan bindiga ba za su yi nasara ba, face sai da taimakon wasu mutane a cikin al’umma.
Da yake magana a taron majalisar jama’a da aka gudanar a Daura a ƙarshen mako, Gwamna Radda, ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ta taimaka wa jama’a don kare yankunansu daga hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata laifuka.
- Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin kawo ƙarshen tsattsauran ra’ayi — Gwamnatin Kano
- Matatar Dangote za ta iya sayar wa ’yan kasuwa fetur — NNPCL
Taron yana ƙarƙashin shirin da aka yi wa laƙabi da “Tattaunawa da Jama’a: Tsarin Kasafin Kuɗaɗen ’Yan Ƙasa na 2025.”
“Muna da tsari wanda za mu tallafawa kowace al’umma da ke son kare kanta, ta hanyar ba su horo da goyon baya domin su fuskanci masu laifuka kafin zuwan jami’an tsaro,” in ji shi.
Gwamnan ya bayar da labarin yadda ya ziyarci wani ƙauye da ake kira Tsamiyar-jino, inda ya shafe tsawon sa’o’i biyu a cikin mota kafin ya isa daga babban titin.
Ya ce idan ‘yan bindiga suka kai hari a irin wannan yankin mai nisa, jami’an tsaro za su ɗauki lokaci mai tsawo kafin su isa ƙauyen domin kai musu ɗauki.
“Kafin su isa, abin da zai faru tuni ya faru – an kashe mutane kuma an yi garkuwa da wasu,” in ji shi.
Ya jaddada cewa jami’an tsaro kaɗai ba za su iya magance matsalar tsaro ba, saboda ya ce ba su da yawa.
Ya bayyana mamakinsa kan yadda mahara ke kashe mutane ba tare da wani yunƙuri daga jama’ar gari na kare kansu ba.
Ya bayyana cewa ƙananan ’yan bindiga za su iya turjiya idan mutanen gari sun haɗa kansu waje ɗaya da nufin kare kansu.
Gwamna Radda, ya kuma gargaɗi cewa biyan kuɗin fansa ba ya tabbatar da tsira ga wanda aka yi garkuwa da shi.
“Wasu lokutan su kan karbi kuɗi amma su kashe mutum,” in ji shi.
Ya kuma zargi wasu shugabannin al’umma da haɗa baki da ’yan bindiga saboda samun kuɗi.
“Wani shugaban al’umma a wani ƙauye ya karɓi Naira 700,000 daga hannun ‘yan bindiga kuma ya bar su suka shiga garinsa, inda suka kashe mutum 30,” in ji shi.
Gwamnan, ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta kama wasu mata da malamai da suke bai wa ’yan bindiga bayanai.
“Duk ɓangarorin jama’a kusan suna da hannu a waɗannan laifukan,” in ji shi.
Domin magance wannan matsala, ya ce gwamnatinsa ta samar da rundunar tsaron sa-kai ta al’umma.
Ya ce an ba su horo tare da samar musu da bindigogi, rigunan kariya, da kayan salke sannan suna aiki tare da ’yan sanda da sojoji.
Kazalika, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da babura 700, motoci ƙirar Hilux guda 65, da motoci masu sulke 10 don ayyukan tsaro.
Haka kuma ya ce suna kashe miliyoyin Naira wajen sayan man fetur da ke kula da motocin a ƙananan hukumomin da ke fama da mahara.
“Mun sayi kayan leƙen asiri masu inganci, wanda har da na’urar 5G, domin taimakawa wajen yaƙi da ‘yan bindiga,” a cewarsa.
Jihar Katsina daj na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ’yan bindiga suka jefa al’umma dama cikin halin ha’ula’i da ƙunci mai tsanani.