Yadda siyasa ta mayar da Gwamna Suntai ’yar bebi

A halin yanzu dai gwamna danbaba Suntai na jihar Taraba  ya zama tamkar ‘yar bebi saboda yadda wadansu da suka ganin sun fi kowa kusa da shi suke amfani da rashin lafiyarsa  suke ta yawo da shi daga wannan wurin zuwa wance don cimma burinsu na siyasa. Aminiya ta gano cewa, wadannan ‘yan bani-na-iyan ana zirgin […]

Yadda siyasa ta mayar da Gwamna Suntai ’yar bebi
Yadda siyasa ta mayar da Gwamna Suntai ’yar bebi

A halin yanzu dai gwamna danbaba Suntai na jihar Taraba  ya zama tamkar ‘yar bebi saboda yadda wadansu da suka ganin sun fi kowa kusa da shi suke amfani da rashin lafiyarsa  suke ta yawo da shi daga wannan wurin zuwa wance don cimma burinsu na siyasa.
 Aminiya ta gano cewa, wadannan ‘yan bani-na-iyan ana zirgin suna samun daurin gindi daga Abuja ne, tare da kuma goyon bayan wani tsohon babban Janar na soja dan asalin Jihar  Taraba, wajen yin babakere dangane da matsalar rashin lafiyar danbaba Suntai.
A karshen mako nan ne aka dawo da danbaba Suntai daga wani asibiti da ke Ingila, amma da suka sauka a filin jirgin saman Abuja, ba a bari mukaddashin gwamna Umar Garba, wanda ya je tarbarsa ya ganshi ba, sai aka tafi da shi gidan Janar danjuma mai ritaya.Su kansu manema labarai ba a yarda sun tattauna da shi ba.
Tun faruwar hadarin jirgin saman da shi Gwanna Suntai ke tukawa watani 23 da suka wuce a kusa da garin Yola da ke jihar Adamaw,a wadannan ‘yan ba-ni-n- iyan, da Sanata Emmanuel Bwacha ke jagoranta suka hana mukaddashin gwanna jihar Alhaji Garba Umar sakat, duk da kasancewa mukaddashin gwamnan ne ke bayar da kudin jinyar danbaba Suntai .
 A lokacin da aka dawo da gwamna danbaba daga wani asibiti da ke kasar Jamus ‘yan ba-ni-na-iyan sun so su haddasa rigimar addini a garin Jalingo, amma Allah Ya kare.
A  ranar lahadi 25 ga watan Agusta na shekarar 2013 ma an dauko danbaba Suntai daga wani asibiti da ke kasar Jamus ba tare da tuntubar mukaddashin gwamnan Garba Umar ba. Amma duk da haka Garba Umar ya tafi filin jirgin sama na Jalingo domin ya tarbi gwamna Suntai, amma  aka hana shi zuwa kusa da inda jirgin da ya kawo gwamnan ya tsaya.
Kwanaki kadan bayan an dawo gwamna Suntai, duk cewa babu wanda ya ga Suntai a fili ko ya ji muryarsa a gidan rediyo ko talabijin, sai kawai ‘yan ba-ni-na-iya suka kai wata wasika  zuwa majalisar dokokin jihar, wanda suka ce wai Suntai ne ya rubuta ta .
A cikin wasikar  Suntai ya  sanar wa majalisar jihar cewa ya dawo cikin koshin lafiya  kuma yana son ya koma aikinsa. Amma mafi yawan  ‘yan majalisar jihar suka nuna shakkun cewa danbaba Suntai ne ya rubuta  takardar da hannunsa. Wannan  ya sa ‘yan majalisar ziyartar danbaba Suntai a cikin gidan sa don tantance gaskiyar cewa ya samu saukin da zai  ba shi damar rubuta wasika da hannunsa. A lokacin wanan ziyara, ‘yan majalisa sun fahimci cewa danbaba Suntai bai da cikakkiyar lafiyar da zai iya komawa bakin aiki, kuma wasikar da aka ce shi gwamna Suntai ne ya rubuta da hannunsa, ba gaskiya ba ne. Bayan an tabka mahawara sai majalisar ta amince Alhaji Garba Umar ya zama mukaddashi Gwamna. Shawarar da ita kanta uwar jam’’iyyar PDP ta kasa ta amince da ita.
 Ana cikin haka, sai jikin gwamna Suntai ya sake tashi,  wanda ya sanya wani kwararan likita mai suna Farfesa Zakari Aliyu, wanda  shi ne shugaban asibitin kwararu na Jalingo, ya bayar da  shawarar   a sake maida Suntai wani asibiti da ke kasar Amurka don a cigaba da jinyarsa. Daga wanan asibitin ne kuma aka  sake kai Suntai  wani asibiti da ke Landan.
Labarin dawo da gwamna Suntai daga Landan ya soma bazuwa a garin Jalingo tun makonni biyu da suka wuce, bayan majalisar zartaswa ta jihar ta yi wani zama inda ta amince da majalisar dokoki ta jihar ta nada  kwamitin masana   domin sun binciki lafiyarsa .
Wannan yunkuri na majalisar zartarwa ta jihar, inji majiyarmu ta tayar da hankalin ‘yan ba-ni-na-iya, inda maza-maza suka shirya dawo da gwamna Suntai zuwa Nijeriya don hana duk wani mataki na doka da majalisar zartarwa da majalisar dokokin jihar ke son dauka dangane da lamarin.
Aminiya ta jiwo cewa, wani jirgin sama mallakar  Janar T.Y. danjuma ne ya dauko gwamna Suntai tare da matarsa Hauwa da likitarsa Dokta Ahmed Kara zuwa Abuja daga Landan.
Majiyarmu ta fadi cewa, jirgi ya sauka cikin dare ne don kauce wa jama’a ganin halin da gwamna Suntai yake ciki, wanda  shi kansa  mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umar da kwamishinonin sa ba su samu damar ganin gwamnan ba.
Majiyarmu ta kara da cewa, da saukar gwamnan sai aka wuce da shi kai tsaye zuwa gidan  Janar danjum  da ke Unguwar Asokoso a cikin Abuja. ‘Yan jarida uku ne kawai suka samu damar yin hira da Gwamna Suntai, inda ya fadi a cikin harshen  turanci cewa, “I thank you for welcoming me from Abuja.” Watau, ’’ na gode muku saboda tarbata da kuka yi daga  Abuja.’’ Fadar haka ta sanya matar sa Hauwa ta fahimci cewa za a ji kunya, sai ta yi maza ta dakatar da hirar.
Wata majiya ta shaida mana cewa, har yazu danbaba bai da cikakkiyar lafiya, saboda haka akwai bukata a rantsar da mukaddashin gwamna Alhji Garba Umar a matsayin gwamnan jihar Taraba.
Wani dan siyasa a jihar  Taraba, Mista James Bulus, ya fadi cewa, dole a kawar da bambancin addini da kabilanci a wannan lamari a rantsar da mukaddashin gwamna, kamar yadda tsarin mulki Najeriya ya tanadar.
Minista James Bulus ya ce, ga dukkan alamu Gwamna dambaba Suntai bai da cikakiyar lafiyar da zai dawo bakin aiki, kuma rashin tsayayyun dangi ne ya sa aka maida shi kamar  ‘yar bebi ake ta  ba shi wahala da rashin lafiyarsa don cim ma wani buri.
Wani dan siyasa kuma a garin Jalingo, Malam Ibrahim Yunusa, ya ce abun takaici ne ganin har zuwa yanzu an ki rantsar da mukaddashin gwamna a matsayin gwamna, duk da kasancewar  Suntai bai san halin da yake ciki a halin yanzu ba.
 Ya ce bai kamata mai matsayi kamar na Janar T.Y. danjuma ya goyi bayan  rashin gaskiya tare da numa kiyayya kan wani addini da nuna kabilalci ba. Ya ce, Janar  danjuma  ya kamata ya yi ya kasance  mai gyara alamumura idan za su baci a Jihar,  ba mai bin bayan karya ba.
Wata majiya kuma ta bayyana cewa, duk abun da ke faruwa ana yinsa ne domin a hana mukaddashin gwamna Garba Umar samun tikitin jam’iyyar PDP lokacin zaben fidda gwani .
Majiyar ta kara da cewa, ministan yankin Neja delta Mista Dariyus Ishaku, wanda dan lailan Janar danjuma ake son ya samu tikitin takarar Gwamnan jihar  a karkashin tutar jam’iyyar PDP a shekara mai zuwa.