Yadda soja ya aika dan sanda lahira
Wani Sufentan dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan da wani soji ya yi masa dukan kawo wuka a yankin Eleme da ke garin Fatakwal a Jihar Ribas. Dan sandan mai suna Hosea Yakubu ya gamu da fushin sojan ne bayan da ya yi aron hanya domin kauce wa cunkoson ababan hawa, a kan hanyarsu […]
Wani Sufentan dan sanda ya gamu da ajalinsa bayan da wani soji ya yi masa dukan kawo wuka a yankin Eleme da ke garin Fatakwal a Jihar Ribas.
Dan sandan mai suna Hosea Yakubu ya gamu da fushin sojan ne bayan da ya yi aron hanya domin kauce wa cunkoson ababan hawa, a kan hanyarsu ta dawowa daga aiki a ranar 16 ga watan Agusta, 2020.
Dan uwan marigayin ya shaida cewa dan uwan nasa tare da abokan aikinsa su biyu sun taso daga wajen aiki sai suka ari hanya domin gudun shiga cunkoso ababan hawa na hanyar Eleme.
A kan hanyar su ne wani soja sanye da kayan gida ya tare su ya bukaci sanin dalilin da ya sa suka yi aron hanyar.
“Gardama ta barke tsakaninsu ‘yan sandan da sojojin lamarin da ya sa daya daga cikin sojojin ya mari dan sandan da ke tuka motar.
“Hakan ta sa marigayin ya fito daga motarsu ta sintiri ya tunkari sojan da ya mari dan sandan; nan take ragowar sojojin suka rufe shi da kokawa.
“A lokacin da suka rufe shi da duka ne daya daga cikin sojojin ya dauki icce mai kauri ya buga wa dan uwan nawa a kai; Nan take kuma ya fadi kasa aka kuma garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal.
“Ya rasu ne bayan sa’a 24 da kwantar da shi a asibitin kuma kawo yanzu babu sanarwa ko daukar mataki daga bangaren ‘yan sandan da yake wa aiki ko bangaren rundunar soji”, inji dan uwan mamcin.
Wakilinmu bai samu jin ta bakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas ko Rundunar Sojan da ke jihar ba.