Yadda sojoji suka fatattaki ISWAP a Sakkwato

Ana takaddama kan harin da aka kashe sojoji a Sakkwato.

Yadda sojoji suka fatattaki ISWAP a Sakkwato

Tsohuwar ajiya (Daga: www.ontv-live.com)

Sojojin Najeriya sun fatattaki mayakan kungiyar ISWAP da suka kaddamar da wani hari a yankin Sabon Birni na Jihar Sakkwato.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ba wa sojojn bisa namijin kokarin, wanda ya ce zai taimaka matuka wajen samar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta tabbatar harin da mayakan kungiyar suka kai wa sansanijn jami’an tsaron hadin gwiwa.

“Hakan zai karfafa kokarinmu na ganin hukumomin tsaron da ke jihar suna aiki tare cikin hadin kai.

“Mun yi tir da hare-haren ISWAP a jiharmu kuma ba za mu bari hakan ya ci gaba ba”.

“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato, muna godiya da jinjina ga sojoji da suka tsaya kai da fata wajen dakile ayyukan masu tayar da kayar baya da suka jima suna addabar Najeriya.

“Muna goyon bayan daukacin hukumomin tsaron kasar nan saboda yadda suka nuna kishin kasa da kuma dagewa wajen fatattakar miyagu a fadin kasar nan.

“Muna rokon Allah Ya kara ba wa sojojinmu nasara, muna kuma da yakinin cewa nan ba da jimawa za su magance matsalar,” inji Tambuwal.

– Sojoji sun tabbatar da harin

Hedkwatar Tsaro ta tabbatar da harin ta’addancin a kan wani sansanin soji da ke karamar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato inda aka kashe jami’an soji da na soji.

Daraktan yada labarai na Rundunar Tsaro, Manjo-Janar Benjamin Sawyer, ya ce sojojin Najeriya da na Nijar suna gudanar da aikin hadin gwiwa don zakulo sauran mayakan na ISWAP.

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa sojojin Operation Hadarin Daji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun yi nasarar dakile harin.

“Harin da aka kai da misalin karfe 5:30 na safe, 26 ga Satumba 2021, a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar, bai yi nasara ba, inda sojojin suka dakile maharan cikin hanzari.

“Hare-haren da sojoji suka kai a watannin baya-bayan nan a shiyyar Arewa maso Yamma, sun ragargaza mayakan ISWAP da ’yan bindiga.”

– ’Yan bindiga ne suka kai harin

Wani malami a Sashen Tarihi na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, wanda ke nazarin ta’addnci a Arewa maso Yamma kuma kwanan nan ya wallafa wani littafi mai suna ‘Ni dan fashi ne,’ Dokta Murtala Rufa’i, ya shaida wa wakilinmu cewa kwamandan ’yan bindiga a Sabon Birni ya bayyana cewa wani sanannen shugaban ’yan fashin a yankin gabashin Sokoto, Turji, ya dauki alhakin harin.

“Ya shaida wa mazauna wasu al’ummomi a Sabon Birni cewa bai kamata a zargi kowa a kan harin ba, saboda shi ne ya kai harin,” inji malamin jami’ar.

Ya karyata ikirarin sojoji na cewa ISWAP ce ta kai harin, yana mai cewa: “Maganar gaskiya ita ce ba mu da wasu abubuwa na ISWAP a Sabon Birni.

“Tarihin ISWAP daya tilo da muke da shi a jihar shi ne tsakanin shekarar 2018 zuwa 2019 lokacin da wasu masu ikirarin jihadi masu alaka da ISWAP da Ansaru suka sauka a wasu wurare kusa da Tangaza, Gudu da Illela.

“Amma sojojin Najeriya da na Nijar sun share su a wani aikin hadin gwiwa kuma tun daga lokacin, ba a kar jin duriyarsu ba.

 -Shugabannin ’yan bindiga sun hada kai

“Turji ne ya tsara wannan harin saboda shi da Halilu da Dankarami sun binne bambance-bambancen da ke tsakaninsu kuma yanzu sun hada kai saboda aikin soji da ke gudana a Zamfara.

“Kafin wannan aikin, ba sa tare, Halilu shi kadai ne, Turji shi kadai ne Dankarami shi kadai. Kuma saboda wannan aikin soji, sun hade.

“Rahotannin da ke fitowa daga Zamfara na nuna cewa babu wani shugaban ’yan ta’adda da aka kashe, ko ya ji rauni ko ya bar sansaninsa. Sun bar sansaninsu na dan lokaci kuma za su koma.

“Wannan harin yana da nasaba da kwanton bauna, an yi wa jami’an tsaro kwanton bauna aka kashe su. Sun kashe sojoji, farar hula da ’yan sanda.”

– Ina mafita

Wani kwararre kan harkokin tsaro da leken asiri, Kabiru Adamu, a wata hira da Aminiya, ya ce hanya daya tilo da za a dakile ayyukan maharan ita ce a tabbatar an yi amfani da duk wuraren da ba su da gwamnati.

Ya ce: “Ba zan kammala wadannan maganganun ba tare da na ambaci bukatar bukatar kwace wuraren da suka mayar maboyarsu ba.

“Akwai wani dajin da ke hada Zamfara da Sabon Birni a Sakkwato, mai yiyuwa ne wadannan banda fashi, sun saba zuwa Sabon Birni, ba su bi ta hanyar da ta saba ba.

“Muna bukatar mamaye wadannan dazuzzukan da kuma sanya idanu da kunne a cikinsu domin tabbatar da babu wata barazai ko mai barazana da ke zaune a cikinsu.

“Sojoji gami da sauran hukumomin tsaro yakamata su sami bayanan sirri da za su gaya musu su wane ne a wadannan kungiyoyin, mene ne karfinsu, lokacin da suke shirin kai hare-hare, da kuma dalilan irin wadannan hare-hare,” inji masanin a kan harkar tsaro.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50