Yadda sojoji suka gano gawar Janar Alkali a cikin rijiya

Rundunar Sojin Najeriya ta gano gawar tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na Hedikwatarta, Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya) a cikin wata tsohuwar rijiya. An gano gawar ce a wata rijiya da ke kauyen Guchwet a Gundumar Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato. Rundunar Sojin ta bayyana cewa a cikin […]

Yadda sojoji suka gano gawar Janar Alkali a cikin rijiya

Rundunar Sojin Najeriya ta gano gawar tsohon Babban Jami’in Gudanarwa na Hedikwatarta, Manjo Janar Mohammed Idris Alkali (mai ritaya) a cikin wata tsohuwar rijiya.

An gano gawar ce a wata rijiya da ke kauyen Guchwet a Gundumar Shen a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato.

Rundunar Sojin ta bayyana cewa a cikin wadanda aka kama bisa zarginsu da hannu wajen bacewar marigayi Janar Alkali ne ya sanar da jami’anta cewa an jefa gawarsa a rijiyar da ta gano marigayin.

Rundunar sojin ta bayyana cewa samun bayanin ne ya sanya ta fara aikin janye ruwan rijiyar a safiyar shekaranjiya Laraba, kuma ba tare da bata lokaci ba ta gano gawar marigayin. Bayan an ciro gawar daga cikin rijiyar ne aka lullube ta a cikin wata jakar leda mai launin tutar Najeriya, kore da fari.

A lokacin da Babban Kwamandan Yaki na Rundunar Sojin Najeriya ta Uku da ke Rukuba a Jihar Filato, Birgediya Janar Umar Mohammed yake jawabi ga ’yan jarida, wanda shi aka damka wa alhakin nemo Janar Alkali ko a mace ko raye, ya bayyana cewa sun samu bayanin jefa gawar marigayin a rijiyar ne daga daya daga cikin mutane takwas da  Rundunar ’Yan sandan Jihar Filato take nema ruwa a jallo, inda daga baya ya mika kansa, sannan ya fallasa cewa an jefa gawar Janar Alkali a rijiyar.

Janar Mohammed ya ce mutum shida daga cikin takwas da ake zargi da hannu wajen bacewar Janar Alkali suna tsare a hannun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Filato.

Idan ba a manta ba dai Janar Alkali ya bace ne a ranar 3 ga Satumba, 2018 a kan hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi, inda bayanin sirri ya tabbatar da bacewarsa a yankin Dura Du da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu, kusa da kauyen tsohon Gwamnan Jihar Filato, Sanata, Dabid Jonah Jang.

Rundanar Sojin ta yi amfani da na’urar bincike mai suna tracker inda ta gano har kududdufin da aka jefa motar Manjo Alkali a ranar 29 ga Satumba, 2018. A ranar Juma’ar makon jiya ma Rundunar Soji ta gano wani karamin kabari da aka yi zargin an binne Janar Alkali bayan an kashe shi, inda kuma aka sake tone gawar tasa, a yanzu kuma aka gano gawarsa a rijiya shekaranjiya Laraba.

Daga nan aka yi wa gawar faretin girmamawa a gaban rijiyar, daga bisani aka sanya ta a cikin mota sannan aka wuce da ita zuwa asibitin barikin rundunar soji da ke Rukuba a Jos.

Janar Mohammed ya ce rundunarsu ba za ta huta ba har sai ta tabbatar da an hukunta duk wadanda suke da hannu a bacewar Janar Alkali.

Zanga-zanga ba za ta hana mu rusau a Abuja ba — Wike 

Lakurawa: Muna buƙatar taimakon Sakkwatawa — Hafsan Sojin Ƙasa

Mayakan Lukurawa sun kashe mutum 17 a Kebbi

Tsadar kayan abinci da rashin tsaro a Arewa abun damuwa ne —Sanata Babangida