Yadda sojoji suka hallaka ’yan ta’adda 8 a Kaduna
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda takwas a wata arangama a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda takwas a wata arangama a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Sojojin sun aika su lahira ne a yankin Kampanin Doka, lokacin da dakarun suke gudanar da sintiri, inda suka iske bata-garin sun kai hari.
Ma’aikatar tsaron jihar Kaduna ta ce, nan take sojoji suka kashe bakwai daga cikin maharan, suka kwato makamai a hannunsu.
Kwamishinan ma’aikatar, Samuel Aruwan, ya ranar Alhamis cewa sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da harsasai sama da 120 da na’urorin sadarwa da wasu makamai da ababen hawa daga hannun ’yan bindigar.
Aruwan a ce sojoji sun kuma hallaka wani dan bindiga a yayin wani sintirin da suka gudanar a yankin Gayam, sauran ’yan ta’addan kuma suka tsere da raunukan harbi.
- Kwamishinan ’yan sandan Akwa Ibom ya rasu a Legas
- Mai aikin shara ya mayar da Dala 10,000 da ya tsinta a Kano
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ambaliya Ke Raba Dubban ‘Yan Najeriya Da Muhallansu