Tahir Baga: Yadda Aka Kashe Babban Abokin Shekau
Tahir Baga na sahun farko da suka kafa kungiyar Boko Haram a Maiduguri kafin su shige Dajin Sambisa tare da irin su Abubakar Shekaru, Mamman Nur, Khalid Albarnawi, da sauransu
Dakarun Operation Hadin Kai sun yi nasarar kashe wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram, Tahir Baga, a Dajin Sambisa.
Tahir Baga wanda babban abokin tsohon shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ne, ya hadu da ajalinsa ne a ranar 13 ga Mayu, 2024 lokacin da sojojin da suka kaddamar da wani babban farmaki, inda suka lalata yankunan Shababul Umma, Garin Panel Beater da Lagara Anguwan Gwaigwai a tsakiyar dajin na Sambisa.
Tahir Baga, ya kasance na kusa da Abubakar Shekau kuma na sahun farko da suka kafa kungiyar Boko Haram a Maiduguri kafin su shige Dajin Sambisa tare da irin su Mamman Nur, Khalid Albarnawi, Abubakar Shekau, Kaka Ali, Mustapha Chad, Abu Maryam da Abu Krimima.
Tahir Baga babban jagora da ake girmamawa a Boko Haram. A lokuta da dama dama ya dakile yunkurin mayaka da yawa da iyalansu na mika wuya sannan kuma ya tursasa yara mata da dama da su kai harin kunar bakin wake.
- Hafsan Sojan Amurka Ya Yi Ritaya Don Goyon Bayan Falasdinawa
- Babu Dalilin Ci Gaba Da Rabon Tallafin Abinci —Gwamnan Gombe
Kisan Tahir Baga, babban koma baya ne ga kungiyoyin ta’addancin Boko Haram.
Majiyoyin leken asiri sun shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi cewa, a ci gaba da kai farmakin sojoji suka hallaka ‘yan ta’adda guda biyar, wasu da dama kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Majiyar ta bayyana cewa, kashe ’yan ta’addan tare da korar su, ya kuma kai ga ceto mutane 14 da suka hada da mata 4 da yara 10 daga hannun ’yan ta’addan.
Dimbin ’yan ta’addan da suka kasa tinkarar sojojin kuma sun tsere suka yi watsi da makamansu da sauran kayan aikinsu.