Yadda sojoji suka kashe dan sanda da duka a Legas
Wasu fusatattun sojoji sun yi wa wani dan sanda dukan tsiya har sai da ya ce ga garinku nan, kan dakatar da su a danjar ba da hannu ta babban titin Badagry da ke Legas. Marigayin dai Insfekta ne a ofishin ’yan sanda da ke Ojo a jihar Legas. Ya kashe mahaifinsa saboda yi wa […]
Wasu fusatattun sojoji sun yi wa wani dan sanda dukan tsiya har sai da ya ce ga garinku nan, kan dakatar da su a danjar ba da hannu ta babban titin Badagry da ke Legas.
Marigayin dai Insfekta ne a ofishin ’yan sanda da ke Ojo a jihar Legas.
- Ya kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya
- NSCDC ta ba iyalan jami’inta da aka kashe a harin Kuje N2.8m
Rahotanni dai na nuna sojojin na dawowa ne daga wani horo, inda suka fusata lokacin da ’yan sandan suka dakatar da hannun da suke, domin ba wani hannaun damar wucewa.
Wani da abin ya faru a kan idonsa, Sule Abiodun ya ce sojojin sun sakko daga motar ta su, in da suka tura `yan Sandan a motarsu suka yi gaba da su.
“Mun samu labarin barikinsu suka kai su suka yi musu dukan tsiya,” inji shi.
Wani shaidar ya ce sojojin sun yi kokarin wullar da gawar a wata magudanar ruwa, kafin mahukuntan Barikin su shiga lamarin.
“Daya Dan Sandan kuma na asibiti, yayin da gawar wanda aka kashen ke ajiye a mutuware”, in ji John Okereke da abin ya faru kan idonsa.
A hannau guda daga masu ruwa da tsaki a Runudunar `yan Sandan har ta Sojojin Division 81 sun yi ALlah wadai da lamarin.
Kakain Rundunar `yan Sandan Legas Benjamin Hundeyin a shafinsa na Twitter ya ce Tawagar Sojoji karkashin jagorancin Birgediya janar KN Nawoko, sun kai ziyarar ta’aziyya da jaje ga Kwamishinan ’yan Sandan jihar Abiodun Alabi ranar Juma’a
.
Shi ma Mataimakin Daraktan yada labarai na ofishin Sojojin na runduna ta 81 ya ce jagororin rundunar na tattaunawa da na ’yan sandan domin daukar matakin da ya dace kan lamarin.