Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Sojojin Nijeriya sun halaka ’yan ta’adda 481, sun kama 741 tare da ceto mutane 492 da aka yi garkuwa da su a cikin wata guda

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar halaka ’yan ta’adda 481 a cikin wata guda a fadin ƙasar.

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce sojojin sun yi nasarar kama ’yan ta’adda 741 tare da kuɓutar da mutane 492 da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a a cikin wata gudan.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ne ya sanar da haka a yayin rahoton da ya gabatar a ranar Alhamis.

Ya ce ayyukan da dakarun suka gudanar sun tarwatsa ’yan ta’adda da maɓoyansu a wurare daban-daban, yana mai cewa sojoji ba za su raga wa ɓata-garin ba.

Manjo-Janar Edward Buba ya kara da cewa sojojin sun ƙwato makamai 480 da harsasai 2,063 daga hannun ’yan ta’addan.

Ya ƙara da cewa a yankin Arewa maso Yamma sojojin Rundunar Operation Hadarin Daji sun aika ’yan ta’adda 163, sun damƙe 80 sannan sun kuɓutar da mutane 80 da aka yi garkuwa da su.

“Sun ƙwato bindigogi ƙirar AK47 guda 121 da bindigogi ƙirar gida guda 32 da sauran makamai 53 da kuma harsasai 2,134, nau’ika daban-daban a yankin” in ji Manjo-Janar Edward Buba.

Ya ci gaba da cewa a yankin Arewa maso Gabas sojojin Rundunar Operation Haɗin Kai sun halaka ’yan ta’adda 198, sun kama 166 tare da kwato fararen hula 156 daga hannunsu.

Hakazalika mayaƙan Boko Haram da iyalansu 257 sun miƙa wuya a sakamakon tsananta ragargazar ’yan ta’adda da sojoji ke yi a yankin.

Ya ce a rewa ta Tsakiya kuma dakarun Rundunar Operation Whirl Stroke da kuma Operation Safe Haven sun kashe ’yan ta’adda 50, an kama 205 tare da ceto mutum 165 da suka sace.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara