Yadda sojoji suka yi wa Halilu Sububu da mayaƙansa kwanton ɓauna

Kwanakin ɗan bindiga Bello Turji sun kusa ƙarewa.

Yadda sojoji suka yi wa Halilu Sububu da mayaƙansa kwanton ɓauna

An samu ƙarin bayanai kan kisan da aka yi wa kurgumin ɗan bindigar nan, Halilu Sububu wanda ake kira da Buzu, wanda ya addabi jama’ar Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da shi.

Aminiya ta ruwaito yadda aka bindige Buzu da mayaƙansa a wata arangama da suka yi da dakarun Operation Hadarin Daji a ranar Alhamis.

A cewar majiyoyi da dama, an kashe Buzu da mayaƙansa ne bayan wani kwanton ɓauna da aka yi musu a Kwaren-Kirya, wani ƙauye da ke kan hanyar Mayanchi zuwa Anka a jihar Zamfara.

Wata majiya a ƙauyen Mayanchi ta tabbatar da cewa sojojin sun kashe ‘yan bindiga da dama a arangamar da suka yi a kan hanyar Mayanchi zuwa Mafara.

“Mun samu labarin cewa ‘yan bindigar na shirin tsallakawa rafi ne, sai sojojin da suka yi musu kwanton ɓauna suka bude muu ut, lmrin d y ki g mutur Sububu da mayaƙansa.

Halilu Sububu

“Mun samu labarin cewa babura uku ne kawai na ‘yan bindigar suka tsere wa harin kwanton ɓaunar a yayin arangamar. Sojojin sun ƙwato makamai da babura na ‘yan bindigar.

“A yanzu da nake magana da ku, mutanenmu suna murna a Mayanchi da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su. Mun yi farin ciki a yau.

“Muna yaba wa sojojin Najeriya da gaske kuma muna fatan za su ci gaba da tafiya har sai sun kama ko kashe Turji da sauran ‘yan bindigar. Mun gaji da wannan ‘yan bindigar.”

Buzu wanda ya fito daga jamhuriyar Nijar, yana zaune ne a wani daji a Zamfara, kuma yakan tsere zuwa ƙasarsa bayan ya kai hari a Nijeriya.

Mun kashe fiye da mayakan Sububu 38 — Rundunr Soji

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta kashe ’yan bindiga fiye da 38, lokacin gumurzun da ya kai ga kisan Halilu Sububu.

Cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’ a na rundunar, Guruf Kaftin Kabiru Ali, ya fitar ya ce dakarun rundunar na musamman tare da haɗin gwiwar rundunar sojin ƙasa sun yi artabu da ’yan bindigar a lokacin da suke wucewa a yankin Mayanchi.

“A lokacin gumurzun, jami’anmu sun kashe jagoransu Halilu Sububu da kuma wasu ƙarin yaransa fiye da 38”, in ji sanarwar.

Sojojin sun kuma ce sun ƙwato makamai masu yawa daga hannun ’yan bindigar da suka haɗa da RPG biyu da RPG mai harba bam, ɗaya, bindiga ƙirar PKT uku, da AK-47 biyar da kwanson zuba alburusai 29 da kuma harsasai fiye da 1000.

Tuni dai babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa ya ce za a tura ƙarin sojoji yankin domin tabbatar da kakkaɓe sauran ’yan bindigar da suka addabi yankin, ciki har da Bello Turji.

Janar Christopher Musa ya ce kwanakin ɗan bindiga, Bello Turji da sauran manyan ’yan bindiga da suka addabi ƙasar sun kusa ƙarewa a daidai lokacin da sojoji suke cigaba da aiki a Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.

Ya ce kashe Kachalla Halilu Sububu, wanda ƙasurgumin ɗan bindiga ne yan cikin nasarorin da sojojin suke samu.

Janar Christopher ya ƙara da cewa wani aikin soji na musamman mai suna “Fansar Yamma a Arewa maso Yamma,” da za a ƙaddamar ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Ya ce za a ƙara tura wasu jiragen yaƙi zuwa jihar domin ci gaba da aikin sojin, kamar yadda babban hafsan ya bayyana a ziyararsa ga Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa