Yadda sojojin Ukraine da na Wagner suke dagargaza Sudan

Rasha na da dakaru masu yawa a Sudan, waɗanda suka je can a ƙarƙashin Kamfanin Wagner.

Yadda sojojin Ukraine da na Wagner suke dagargaza Sudan

An yi wata ganawar ba-zata a watan Satumban 2023, a wani wuri da ba a saba ba.

A yayin da Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yada zango a filin jirgin sama na Shannon da ke Ireland a kan hanyarsa ta komawa gida daga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar a New York, ya gana da Shugaban Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batun matsalar tsaro ta duniya da kuma “ƙalubalen da haramtattun ƙungiyoyin da Rasha ke ɗaukar nauyinsu ke yi.’’

Ofishin Zelensky ya ce ganawar shugabannin biyu da suka haɗu a tashar jirgin, sakamakon yada zango da jiragensu suka yi, ba tsarata aka yi ba.

To amma wani rahoto ya nuna cewa wasu dakarun musamman na Ukraine sun taka rawar gani wajen ƙulla ganawar.

A lokacin Sudan ta fuskanci gagarumin koma-baya sakamakon yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun tsaro na RSF.

Rikicin ya samo asali ne sakamakon rikicin shugabanci a tsakanin manyan jagororin sojin ƙasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan, Shugaban Rundunar Sojin Sudan da ke matsayin Shugaban Kasar da kuma tsohon Mataimakinsa, wanda shi ke jagorantar rundunar tsaron ta RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemedti.

Yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da raba wasu miliyoyi da gidanjensu, inda wasu suka fice daga ƙasar.

Haka tattalin arzikin ƙasar ya samu gagarumin komabaya sakamakon yaƙin.

Yadda Ukraine ke goyon bayan sojojin gwamnatin Sudan

Mujallar Wall Street Journal ta ce sojojin Ukraine sun taimaka wa al-Burhan ficewa daga birnin Khartum a watan Agustan 2023 a lokacin da dakarun RSF suka yi wa hadikwatar sojojinsa ƙawanya.

Daruruwan dakarun Ukraine na musamman a ƙarƙashin jagorancin jami’in leƙen asirin ƙasar da ka fi sani da Timur sun isa Sudan bayan musayar jawabai ta waya da aka yi a tsakanin Janar al-Burhan da Zelensky, kamar yadda mujallar ta ruwaito.

Mujallar ta Wall Street Journal ta ce dakarun Ukraine ba taimakawa wajen tseratar da al-Burhan kaɗai suka yi ba, har da sauya salon yaƙin Sudan, ta hanyar kai jirage masara matuƙa tare da kai wa dakarun RSF samame cikin dare.

Sai dai a amsar da ta ba BBC, Hukumar Leƙen Asiri ta Ukraine ba ta tabbatar ko musanta rahotonnin hannu a yaƙin na Sudan ba, sai dai ta ce “jami’anta na gudanar da ayyukansu a wasu yankuna daban-daban don kare muradun ’yan ƙasarta da ke zaune a wasu ƙasashe’’.

Me sojojin Wagner ke yi a Sudan?

A watan Fabrairun 2024, wani bidiyo ya ɓulla inda a ciki ake zargin cewa dakarun Ukraine a Sudan sun kewaye wata motar sojoji da ta sha ruwan harsasai tare da gawar wani sojan Rasha a ciki.

Motar na ɗauke da alamar tambarin kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner.

A wani ɓangare na bidiyon, an ga sojojin Ukraine na yi wa wasu sojojin Rasha da suka kama tambayoyi. “Mece ce manufarku a nan?” kamar yadda wani sojan Ukraine ya tambaya.

“Mu kawar da gwamnatin yankin,” sojan ya amsa. Ba a dai san yaushe ko wurin da aka ɗauki bidiyon a Sudan ba, kuma BBC ba za ta iya tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Kamfanin sojojin hayar Rasha na Wagner ya daɗe a Sudan, tun kafin ɓarkewar yaƙi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.

An fara ganin bidiyon farko na sojojin Wagner a Sudan a shekarar 2017.

A lokacin rahotonni sun ce dakarun na Wagner na bayar da horo ne ga sojojin Sudan, tare da zargin cewa suna taimaka wa dakarun tsaron ƙasar wajen murƙushe masu zanga-zanga.

Bayan mutuwar shugaban Wagner, Mista Yebgeny Prigozhin a watan Agustan 2023, sashen kamfanin da ke aiki a ƙasashen Afirka ciki har da Sudan ya koma ƙarƙashin ikon dakarun sojin Rasha na musamman.

A yanzu mayaƙan Wagner da ke goyon bayan dakarun RSF, su ne waɗanda sojojin Ukraine ke son kai wa hari, kamar yadda Misis Beberley Ochieng, mai sharhi ta BBC Monitoring ta bayyana.

“Rahotonnin da ke fitowa game da aikin da sojojin Ukraine ke yi a Sudan, na nuna cewa a yanzu sun fi mayar da hankali wajen kai wa dakarun Rasha hari, fiye da taimaka wa sojojin Sudan wajen yaƙar dakarun RSF,’’ in ji ta.

Hukumomin Ukraine sun sha zargin dakarun Kungiyar Wagner da aikata laifuffukan yaƙi.

Shugaban Sashen Tattara Bayanan Sirri na Rundunar Sojin Ukraine, Mista Kyrylo Budanob ya yi zargin cewa wasu daga cikin dakarun na Wagner da ke a Sudan yanzu, sun taɓa yin yaƙi a Ukraine.

“Duk dakarun Rasha da suka aikata laifuffukan yaƙi, walau a baya ko a nan gaba za su fuskanci ladabtarwa a ko’ina suke a duniya’’, in ji shi.

Kasar Ukraine na ƙoƙarin kakkaɓe dakarun sojin hayar Rasha, ta hanyar tallafa wa gwamnatin Sudan da kuɗi, kamar yadda Mista Murad Batal Shishani ya bayyana a wani jawabi kan rikicin siyasar duniya da aka gudanar a Landan.

“Janar Hemedti ya kasance babban abokin Rasha a Afirka musamman Kungiyar Wagner.

“Shi ke iko da yankin da ke da arzikin zinare a ƙasar, wani babban abin da ake biyan Wagner da shi,’’ in ji shi.

A 2022, wani rahoto na kafar yaɗa labaran CNN ya zargi Rasha da hannu a haƙa tare da cinikin zinare a Sudan, inda aka zargi Rashar da aikewa da jirage 16 maƙare da zinaren daga Sudan zuwa Siriya.

Wata majiya daga Rundunar Sojin Ukraine ta tabbatar wa mujallar Wall Street Journal (WSJ) cewa tana wani shiri don kawo tarnaƙi ga kasuwancin zinare da Rasha ke yi a Sudan.

Samun galaba a kan Janar Hemedti tare da ƙarfafa ƙawance tsakanin Ukraine da Sudan, ka iya kawo naƙasu ga shirin Rasha na samar da sansanin sojinta a Jihar Port Sudan da ke bakin Tekun Maliya.

‘Maƙiyin maƙiyina abokina ne’

Wasu masu sharhi na kiran abin da ke faruwa a Sudan yanzu a matsayin ‘“Cikakken yaƙin bayan fage tsakanin Rasha da Ukraine’’, wani yaƙi da ake amfani da wani, inda kowane ke ƙoƙarin kare muradunsa.

“Janar Hemedti na samun goyon bayan ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Rasha, yayin da al-Burhan ke samaun nasara a yaƙin saboda samun tallafin kuɗi daga Saudiyya da sojoji daga Ukraine,’’ kamar yadda Mista Glen Howard, tsohon Shugaban Gidauniyar Jamestown, wata ƙungiyar bincike a Amurka ya fadi.

Ukraine na ƙoƙarin gina kanta ta yadda za ta riƙa yi wa Rasha barazana a ko’ina a duniya, kamar yadda Nicholas A. Heras na cibiyar New Lines ta Amurka ya bayyana.

“Shirin da ke tsakanin Shugaba Zelensky da Al-Burhan shi ne abin nan da ’yan magana ke cewa “maƙiyin maƙiyina, abokina ne,’’ in ji shi.

“Haka kuma Ukraine tana jin daɗin hakan, saboda yana nuna wa duniya cewa Zelensky zai iya fuskantar Putin a kowane lokaci, kuma a ko’ina, ba Turai kawai ba,’’ in ji shi.

To sai dai ƙarfin Sojojin Ukraine a Sudan, ba ya da yawa, sakamakon yaƙin da take yi da Rasha a ƙasar, don haka ne takan aika sojoji ’yan ƙalilan ga abokanta na Afirka.

“Amma saɓanin Ukraine, ita Rasha dakarunta na da yawa a Sudan.

“Rasha na da dakaru masu yawa a Sudan, waɗanda suka je can a ƙarƙashin Kamfanin Wagner, inda ɗimbin mayaƙan ƙungiyar da ke da tarin makaman atilare da sauran manyan makamai masu linzami, ke horas da dakarun RSF dabarun yaƙi,’’ in ji Heras.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta