Yadda sunan ‘Corona’ ya janyo wa wata Mata tsangwama

Wata mata mai suna Corona Newton wadda a yanzu uwa ce ta bayyana yadda ake yawan tsangwamarta saboda sunanta ya zo daidai da cutar da ta addabi duniya a yanzu wato Coronavirus (COVID-19). Corona Newton mai shekara 49 kuma ma’aikaciyar gwamnati, ta ce tana kokari don jure cin mutuncin da jama’a ke yi mata sanadiyyar […]

Yadda sunan ‘Corona’ ya janyo wa wata Mata tsangwama

Corona Newton
Hoto Daga Metro.co.uk

Wata mata mai suna Corona Newton wadda a yanzu uwa ce ta bayyana yadda ake yawan tsangwamarta saboda sunanta ya zo daidai da cutar da ta addabi duniya a yanzu wato Coronavirus (COVID-19).

Corona Newton mai shekara 49 kuma ma’aikaciyar gwamnati, ta ce tana kokari don jure cin mutuncin da jama’a ke yi mata sanadiyyar sunanta.

“Mutane da yawa suna kirana da sunan Guinness da Budweiser,” inji Corona.

“Ina yawan yi musu dariya, amma abin yanzu ya fara wuce gona da iri, musamman yadda ya kai ga cin mutunci ta hanyar faxin sunan cikin vacin rai,” inji ta.

Corona ta ce, ma’aikatan gidajen sayar da abinci suna tunanin ina yin wasan barkwanci ne da sunanta da zarar ta gabatar da kanta wajen sayan abinci.

Ta ce: “Mutane da dama suna ce min kamar da ma ina jiran sunan wata cuta ce kafin a rada min sunan.”

Corona mahaifiyar ’ya’ya biyar ta ce ta dade tana fama da amsa kiran waya, inda ake tambayarta cewa: “Me sunan cuta ce ke magana?”

Jaridar The Mirror ta wallafa cewa, a lokacin da Corona take tukin mota tare da ’yarta don zuwa ganin likitan hakori a asibiti, sai ta amsa kiran waya daga wani mutum, inda ya fara tsine mata da cin mutuncinta.

Corona ’yar asalin birnin Oldham da ke garin Manchester a Kasar Ingila ta ce: “Ya yi min ihu a wayar sadarwa, (ya ji a ransa kamar zai iya aikata wani mugun abu game da ni) duniya ta zo karshe?”

Bayan ’yar Corona ta isa makaranta sai wani malami ya ce da ita me ya yi zafi ake kiran mahaifiyarta da sunan Corona?

Asalin sunan Corona Newton iyayenta ne suka rada mata, sun yi muhawara kan su sanya mata sunan Sarah ko Caroline wanda bayan sun gaza cimma matsaya, kawai suka rada mata suna Corona Kamar yadda jaridar Daily Star ta ruwaito.

Asalin sunan Corona an samo shi ne daga kalmar Latin wato Crown, wanda su ma suka aro kalmar daga Girka.

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba