Yadda surukaina suka yi garkuwa da matata —Magidanci

Iyayen matar sun je gidansa sun kwashe kayan N2.5m sannan suka yi awon gaba da ita

Yadda surukaina suka yi garkuwa da matata —Magidanci

Kotu

Wani magidanci ya zargi surukansa da yin garkuwa da matarsa mai juna biyu da kuma sace masa dukiya.

Ya shaida wa kotun Majistare da ke zamanta a Madalla cewa iyayen matar sun je gidansa sun kwashe masa kayan Naira miliyan 2.5 sannan suka yi awon gaba da matar tasa.

Ya kara da cewa surukan nasa sun kuma yi awon gaba da ’yarsu mai juna biyu daga gidansa da ke Rafinsanyi a Suleja, ba tare da saninsa ba.

Wadanda ake zargin dai sun musanta tuhumar da ake musu, bayan dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Ateni ya karanta zargin da ake musu.

Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Majistare Ruth Ibrahim, ta bayar da belin wadanda ake zargin bisa sharadin za su gabatar da mutum biyu da za su tsaya musu.

Daga nan sai kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Satumba.