Yadda ta kaya a kananan hukumomin Abuja

A makon jiya ne aka gudanar da zaben kananan hukumomin yankin Birnin Tarayya, Abuja, inda Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin biyar Jam’iyyar APGA ta samu daya, yayin da PDP ta tashi a tutar babu. Ga jerin zababbun shugabannin da Hukumar INEC ta bayyana kamar haka:APC 5 1.    Abdullahi Adamu (APC), Yankin Birnin Abuja (AMAC) […]

Yadda ta kaya a kananan hukumomin Abuja
Yadda ta kaya a kananan hukumomin Abuja

A makon jiya ne aka gudanar da zaben kananan hukumomin yankin Birnin Tarayya, Abuja, inda Jam’iyyar APC ta lashe kujerun shugabannin biyar Jam’iyyar APGA ta samu daya, yayin da PDP ta tashi a tutar babu. Ga jerin zababbun shugabannin da Hukumar INEC ta bayyana kamar haka:
APC 5
1.    Abdullahi Adamu (APC), Yankin Birnin Abuja (AMAC) ya samu kuri’a dubu 27 da 482. Bitrus Tanko (PDP), kuri’a dubu 21 da 965.
2.    Abaji, Abdulrahman Ajayi (APC) yalashe da kuri’a dubu 13 da 515, ya kada Yahaya Garba (PDP) wanda ya samu kuri’a dubu 10 da 632.
3.    Bwari, Mista Musa Dikko (APC), ya samu nasara da kuri’a dubu 18 da 66, sai Andrew S. Gwani Igu (PDP), kuri’a dubu 13 da 279.
4.    Abdullahi D. Galadima (APC) ya lashe ta Kuje da kuri’a dubu 15 da 175 ya kada Ishaku Tete Shaban (PDP) mai kuri’a dubu 13 da 650.
5.    Joseph K. Shazin (APC) ya kawo Kwali da kuri’a dubu 15 da 309, yayin da Daniel Ibrahim (PDP) ke bin sad a kuri’a dubu 13 da 673.
APGA
dan takarar Jam’iyyar APGA, Danze Mustapha Adams ya lashe Gwagwalada da kuri’a dubu 15 da 590, ya kada na APC, Abubakar Jibrin Giri, wanda ya samu kuri’a dubu 14 da 569.