Yadda ta kaya a wasannin farko na kakar bana a Ingila da Sifaniya

Chelsea ce ta fara da ƙafar hagu bayan da Manchester City ta je har gida ta doke da ci 2-0.

Yadda ta kaya a wasannin farko na kakar bana a Ingila da Sifaniya

Kakar ƙwallon ƙafa ta bana 2024/2025 da ta kankama a ranar Juma’ar da ta gabata ta fara da ɗaukar zafi inda wasu ƙungiyoyi suka fara gasar da ƙafar hagu sannan wasu ƙungiyoyin da ake ganin ƙanana ne suka riƙe wuyan manyan ƙungiyoyi.

A gasar Firimiyar Ingila, Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Chelsea ce ta fara wasan da ƙafar hagu bayan da takwararta ta Manchester City ta je har gida ta doke da ci 2-0 a wasan makon farko da suka kara a ranar Lahadi a filin wasa na Stamford Bridge.

Shi ne karon farko da sabon Kocin Chelsea Enzo Maresca wanda ta ɗauko daga Leicester City ya ja ragamarta.

Chelsea, wadda ta yi ta shida a bara ta raba gari da kocinta Mauricio Pochettino, sannan ta maye gurbinsa da Marresca.

Minti na 18 da fara gara ƙwallo sai City ta jefa ƙwallo ta hannun Erling Halaand – wanda ya buga wasa 100 a ƙungiyar ta Etihad, inda ya ci 91, sannan ya taimaka aka zura 15 a raga.

A kakar wasa ta 2022/2023, Erling Haaland ya jefa ƙwallaye da yawa a gasar Premier inda cikin watan Agusta ya jefa ƙwallo 13 fiye da yawan ƙwallon da ’yan wasan Chelsea gaba ɗaya suka ci guda 11 da na Manchester United guda tara kamar yadda BBC ta ruwaito.

City ta ƙara ƙwallo ta biyu ta hannun Mateo Koɓacic, saura minti shida a tashi daga fafatawar ta hamayya.

Ƙungiyar Chelsea ta kashe zunzuruntun kuɗi Fam miliyan 185 (kimanin Naira biliyan 388 da miliyan 500) wajen sayen ’yan wasa 11 a bana.

Don haka Maresca yana da manyan ’yan ƙwallo sama da 40 a ƙungiyar.

Da wannan sakamakon City ta yi wasa 24 a jere a gasar Premier ba tare da rashin nasara ba, tun lokacin da Aston Villa ta doke ta da ci 1-0 a watan Disamban bara.

Wannan ne karo na takwas a jere da City ta fara wasan farko a Premier a waje.

Ƙungiyar ta lashe wasa 13 daga 14 a farkon fara Premier, idan ka cire wanda Tottenham ta doke ta 1-0 a kakar 2021/2022.

Ita kuma Chelsea ba ta yi nasara ba a karo na 10 da ta fuskanci City, tun bayan ci 1-0 da ta ci mata a gasar Zakarun Turai a shekarar 2021, inda ta yi canjaras biyu aka doke ta takwas daga ciki.

Manchester City ta ci wasa na huɗu da canjaras a fafatawa biyar bayan da ta je ta fafata a Stamford Bridge.

A fafatawa a tsakanin Leicester City da Tottenham kuwa a ranar Litinin da ta gabata sun tashi ne kunnen doki, inda suka raba maki a gasar ta Premier.

Pedro Porro ne ya fara ci wa Tottenham ƙwallo a minti na 31 a karawar ta hamayya, kuma haka suka je hutun rabin lokaci ana cin Leicester City 1-0.

Bayan da aka dawo zagaye na biyu ne Leicester ta riƙe wuyan Tottenham inda Jamie Ɓardy ya jefa ƙwallo a ragar Tottenham.

An yi mamaki da Leicester City ta fara wasa da Jamie Ɓardy, wanda kwana ɗaya tsakani koci Steve Cooper ya ce ɗan ƙwallon yana jinya.

Leicester ta fara amfani da Bobby Decordoɓa-Reid, wanda ta ɗauka a bana da wanda ta ɗauka aro daga Brighton, Facundo Buonanotte.

Sauran wasannin da aka buga:

Arsenal 2 — Wolves 0

Newcastle 1 — Southampton 0

Nottm. Forest 1 — Bournemouth 1

Man United 1 — Fulham 0

Brentford 2 — Crystal Palace 1

Ipswich Town 0 — Liverpool 2

Everton 0 — Brighton 3

A gasar La Liga ta Spain kuwa Mallorca ce ta riƙe wuyan Real Madrid mai riƙe da kofin inda suka tashi wasan ranar Lahadi da ci 1-1

Real Madrid ce ta fara jefa ƙwallo a ragar Mallorca ta hannun Rodrygo a minti14 da fara taka leda, haka suka tafi hutun rabin lokaci, Real na da ƙwallo ɗaya a raga.

Sai dai bayan da aka dawo zagaye na biyu ne mai masaukin baƙi ta farke ƙwallon ta hannun Vedat Muriƙi.

Real ta ƙare wasan da ’yan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ferland Mendy katin kora daf da za a tashi, sakamakon ƙetar da ya yi wa Vedat Muriƙi.

A kakar bara a gasar ta La Liga, Real ta doke Mallorca 1-0 a gida da waje.

A ranar Asabar kuma Barcelona ta je gida ta lallasa Valencia da ci 2-1 a wasan makon farko a La Liga.

In za a iya tunawa a ranar Larabar makon jiya ne Real Madrid mai riƙe da Kofin La Liga ta ɗauki Kofin UEFA Super Cup na bana, bayan da ta lallasa Atalanta da ci 2-0 a birnin Warsaw na ƙasar Poland.

Real ce ta lashe Kofin La Liga a kakar bara da Kofin Zakarun Turai (Champions League).

Sauran wasannin da aka fafata sun haɗa:

Osasuna 1 — Leganes 1

Real Sociedad 1 — Rayo Vallecano 2

Valencia 0 — Barcelona 2

Valladolid 1 — Espanyol 0

Villareal 2 — Atletico Madrid 2

Wasannin mako na biyu yau Juma’a 23 ga Agusta za a fafata kamar haka:

Celta Vigo da Valencia

Sevilla da Villarreal

Gobe Asabar 24 ga Agustan 2024

Osasuna da Mallorca

Barcelona da Athletico Bilbao

Getafe da R. Vallecano

Espanyol da Sociedad

Jibi Lahadi 25 ga Agustan 2024

Real Madrid da Valladolid

Leganes da Las Palmas

Alaɓes da Real Betis

Atletico Madrid da Girona

Yadda kasuwar ’yan wasa ke gudana

Wakilan ɗan wasa mai kai hari na Brentford da Ingila Iɓan Toney na tattaunawa da Ƙungiyar Al-Ahli ta Saudiyya domin sayen ɗan wasan mai shekara 28. (Teamtalk).

A makon jiya ne Brentford ta yi watsi da tayin da Al-Ahli

ta yi wa Toney. (Telegraph). Manchester United ba ta da sha’awar ɗaukar Toney. (Sky, Jamus).

Manchester City na son kocinta Pep Guardiola, mai shekara 53, ya yanke shawara kan ko zai rattaba hannu a kan sabon kwantiragi da ƙungiyar kafin Kirsimeti.

A shekarar 2025 ce kwantiragin ɗan ƙasar Spain ɗin zai zo ƙarshe. (Sky Sports).

Nottingham Forest da Villarreal da Sevilla da Valencia na zawarcin mai tsaron baya na Aston Ɓilla da Spain, Alex Moreno, mai shekara 31. (Football Insider).

Gundogan zai bar Barca, Chelsea za ta bayar da Sterling ta karɓi Chiesa

Tottenham ta sallama tayin da Leicester ta yi wa Skipp

Panathinaikos na tattaunawa da Manchester United kan cinikin ɗan wasan tsakiyar Uruguay, Facundo Pellistri mai shekara 22. (Athletic).

Atletico Madrid ba ta yanke shawara a kan ko za ta sayi ɗan wasan tsakiya na Valencia da Spain Javi Guerra mai shekara 21 yayin da yarjejeniyar da suke son su ƙulla da ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila, Conor Gallagher mai shekara 24 ta gamu da cikas. (Athletic).

Liverpool za ta jira har zuwa kasuwar sayar da ’yan wasa ta watan Janairu don sayen zaƙaƙurin ɗan wasan nan bayan ƙoƙarin da take yi don sayen ɗan wasan tsakiyar Spain Martin Zubimendi mai shekara 25, daga Real Sociedad ya ci-tura. (Football Insider).

Fulham ta sake tattaunawa da Manchester United domin sayen ɗan wasan tsakiyar Scotland Scott McTominay mai shekara 27. (Sky Sports).

Daraktan wasanni na Napoli Giovanni Manna ya ƙi ya bayanna makomar McTominay. (Manchester Eɓening News).

Las Palmas ta yi wa Fulham tayin sayan ɗan wasanta ɗan ƙasar Brazil Carlos Vunicius, mai shekara 29 wanda Corinthians ke zawarcinsa. (Sky Sports).

Crystal Palace ta samu nasara a cinikin da take yi kan mai tsaron bayan Faransa da Wolfsburg Maxence Lacroix mai shekara 24. (Sky ta Jamus).

Sun kashe yaron da suka sace bayan neman fansar N25m

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Suka Sa Farashin Citta Ta Yi Tashin Gwauron Zabo

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT