Yadda ta kwashe a taron mawakan Hausa na duniya a Bauchi
A ranar Larabar makon jiya ce kungiyar Mawakan Najeriya ta gudanar da babban taronta, wanda ta saba gudanarwa duk shekara. A yayin gudanar da taron, wanda ya wakana a babban dakin taron da ke daura da kasuwar Wunti a cikin garin Bauchi, Shugaban kungiyar Mawakan Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Aliyu Ningi ya ce: “Babu abin […]
A ranar Larabar makon jiya ce kungiyar Mawakan Najeriya ta gudanar da babban taronta, wanda ta saba gudanarwa duk shekara.
A yayin gudanar da taron, wanda ya wakana a babban dakin taron da ke daura da kasuwar Wunti a cikin garin Bauchi, Shugaban kungiyar Mawakan Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Aliyu Ningi ya ce: “Babu abin da za mu fada wa Gwamnatin Jihar Bauchi sai godiya, domin ta ba da dukkan gudunmawar da ya kamata; duk da cewa kowa ya san cewa ana fama da karancin kudade a wannan lokaci amma abubuwa sun tafi yadda ya kamata a wajen taron.”
Cikin wadanda suka rera wakoki a wajen taron sun hada da Fati Nijar sai Adam A zango Aminu Alan waka daga Jihar Kano. Akwai mawaka kamar Khalifa Alhaji Sunusi Dokta Mamman Shata Katsina da A’isha Bauchi da Fati Jos da sauran dimbin mawaka, wadanda suka fito daga jihohi daban-daban na Arewacin Najeriya.
Akwai mawaka mata daga Jamhuriyar Kamaru da Nijar da Benin da Ghana da makamantansu.
Da yake zantawa da Aminiya a wajen taron, Shugaban kungiyar Mawakan ta kasa reshen Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Aliyu Ningi ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Bauchi Barista Muhammad Abubakar ya ba da gudunmawa sosai domin a lokacin gudanar da taron kuma gwamnatin jiha ta bada masauki da abinci ga mawaka, wadanda suka fito daga jihohi daban-daban. Sannan Shugaban Majalisar Tarayya, Barista Yakubu Dogara shi ma ya ba da gudunmawa sosai. Sauran wadanda suka ba da gudunmawa sun hada da dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya, Salisu Zakari Ningi, sai Malam Ali Wakili, Fagacin Bauchi, Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta kudu.
Da ya ke zantawa da wakilin Aminiya a wajen taron, wakilin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Isma’ila Na’abba (Afakalla) ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta dauki nauyin gudanar da makamancin wannan taro a shekara mai zuwa. Sannan kuma Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano za ta ci gaba da ba da dukkan gudunmawar da ya kamata ga kungiyoyin mawaka da sauran masu shirya fina-finan Hausa; domin ta haka ne za a tsaftace harkar waka da masu satar fasaha.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Wamban Kano, Alhaji Aminu Ado Bayaro ya bayyana farin cikinsa game da yadda aka gudanar da taron, sannan kuma ya shawarci mawakan kasar Hausa su ci gaba da hada kansu waje daya domin babu al’ummar da za ta samu ci gaba sai da hadin kai.
Daga bisani Alhaji Aminu Alan waka ya yi kyautar sabuwar mota kirar Toyota ga Alhaji Sunusi Dokta Mamman Shata a wajen taron.
Alhaji Maigari Muhammad Khanna, Shugaban Gidan Rediyon Bauchi (BRC), shi ne babban bako mai jawabi a wajen taron sannan kuma ya bayyana cewa tun lokacin da aka bude taron, Gidan Rediyon Bauchi yake watsa abubuwan da ke gudana kai tsaye a tashoshin rediyon Bauchi 12.
“kungiyar Mawakan Najeriya tana da alaka mai kyau tsakaninta da Gidan Rediyon Bauchi (BRC).” Inji Maigari Khanna.
Da yake jawabin rufe taron, Alhaji Haruna Aliyu Ningi ya nuna godiyarsa ga daukacin mutanen da suka halarci taron, sannan kuma ya mika godiyarsa ga Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Bauchi bisa yadda jami’ansa suka ba da tsaro a lokacin gudanar da taron. “Muna fatar kowa ya koma gidansa lafiya.’ Inji shi.
Sama da mawaka hamsin ne aka ba su lambar yabo a wajen taron. Sannan kuma akwai mawaka wadanda suka fito daga jihohin Gombe, Yobe, Adamawa, Kano, Jigawa, Katsina, Kaduna, Neja, Jos, Taraba, Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Nasarawa, Borno da Bauchi.