Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (3)
Diyata Ummulhairi ta yi mani bayanin nasarar da ka samu.
A shekarar 2012, shekara goma ke nan cur da ta gabata, wani al’amari mai ban mamaki ya faru da ni GIZAGO (08065576011), inda na gana da wata ‘aljana’ mai suna Ummulhairi da kuma mahaifinta.
Na zabi in ba ku labarin dukkan yadda ganawar tamu ta gudana, domin akwai gargadi da darussa masu yawa da za mu iya amfani da su a zamanance.
- Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (2)
- Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (1)
A yau za mu dora daga inda muka tsaya, ku biyo ni!
Ina fadin haka sai na ji ta kyalkyale da dariya. Ta ce mani cikin wata murya mai albishir. “A’a, ba ni da aure!”
“Yauwa, Allah Ya cika mani burina a game da ke Ya Umma!”
Na yi addu’a. Ita kuwa ta ce, “Amin.”
“Tun yanzu, kafin a jima mu sake magana, bari in gaya maki abin da nake ciki, domin ki taya ni addu’a.”
Na sake bujiro mata da wani batu na karya.
“Kamar yadda na ce, wani aiki ne Ministan Abuja zai ba mu kuma ina sa ran muddin dai aikin ya tabbata, akwai alheri, domin ni kaina ina sa ran zan samu Naira Miliyan biyar daga cikin ladan aikin.
Don haka ki taya ni addu’a.”
Kafin ma in rufe baki, sai na ji Ummulhairi ta fara jawo dogayen addu’o’i.
Haka ta yi ta yi, sai da ta dauki minti uku da rabi tana zuba addu’o’i, sannan ta ce “Amin.”
Muka shafa tare. “Na gode, na gode Umma. Don Allah ki taimaka ki gaishe mani da Baba, da zarar ya gama hidimar da kika ce.
Kuma ina son idan na gana da Minista zuwa jibi zan je kasuwa in yo maku siyayya.
Ina son saya wa Baba turare. Ki taimaka ki gaya mani sunan turaren da yake amfani da shi.”
Tana jin haka sai na ji ta fadi mani sunan wani turare, ni kuma na ma mance sunan da ta gaya mani.
Na ce a cikin raina, “Wannan tantiriyar ’yar wankiyar, lallai ta gamu da gamonta.
“Idan ka je za ka shiga wajen Minista, ka karanta Ayatul Kursiyyu, ka hada da Lahaula kafa uku, sannan ka yi wa Manzon Allah salati.
Da ikon Allah, duk abin da ka je nema za ka samu a wurinsa. Amma kada ka mance, komai dare ka dawo, ka kira ni zan hada ka da Baba. Wassalamu alaikum.”
Abin da ta gaya mani ke nan, sai ta kashe waya. Ni kuwa na kishingida a gadona da nufin yin barci. Na kashe wayata.
Ba ni na sake jin maganarta ba sai washegari da misalin karfe hudu na yamma, lokacin da ta kira ni.
Ni kuwa sai na dauki waya, bayan ta fara da gaisuwa, ni kuwa sai na gyara murya na amsa mata.
Kafin ma ta ce wani abu, sai na ce mata: “Malama Umma, albishirinki!”
Kawai sai na ji ta kyalkyale da dariya. Ta ce mani: “Goro!”
Tana fadin haka sai na yi tunani cikin sauri, na ce bari in kara shirya mata gadar zare.
Na ce mata: “Ki taya ni godiya ga Allah, domin kuwa addu’ar nan taki ta jiya, Allah Ya amsa.
Kin san yadda muka yi da Minista kuwa?” Kafin in kai ga rufe maganata, sai kawai na ji ta fara cewa: “Masha Allah, alhamdu lillahi, shukurallah kasiran. La haula wala kuwwata illa billah. Ka ce mani an dace ke nan.”
“Kwarai kuwa, an dace. Kin san na gaya maki wani aiki ne mai kima zai ba mu, wanda zan samu Naira miliyan biyar. Ai kuwa abin ma sai ya zama tamkar abin da Hausawa ke kira gyadar dogo, kasa ’ya’ya, sama ’ya’ya.
Maimakon Naira miliyan biyar da na sa ran samu, sai ga shi na samu Naira miliyan goma sha biyar.
Bayan haka, ya kuma kara yi mani alkawarin wani aikin nan da wata daya mai zuwa.
Kin ga kuwa ina bukatar taimakon karin addu’a. Ina Baba yake ne ko yana kusa?”
“Kai, amma na ji dadi da wannan bayani,” inji Ummulhairi.
Ta ci gaba da cewa: “Baba yana Saudiyya, yana gudanar da wata addu’a ta musamman, amma zai dawo nan Hubbare da magariba.
Zan shaida masa wannan abin alheri.”
Ta dan dakata da magana, sannan ta ce mani: “Da ma jiya na gaya maka cewa akwai alherai masu yawa da za su same ka, to wannan somin tabi ne.”
Ni kuwa sai na yi dariya, na ce a zuciyata, ka ji shashasha!
Sai na ce mata: “Game da alkawarin da na yi maku jiya ke da Baba, dazu na je kasuwa na sayo turaren nan, ke kuma na zabo maki wasu abubuwa na musamman.
Ta yaya zan same ku domin in ba ku?” Jin haka sai Ummulhairi ta ce: “Me ya sanya ka cika sauri haka? Bari in sanar da kai wani abu da ka mance.
Ka tuna fa mu rauhanai ne, ba mu bukatar wani kayan abinci da sutura da sauran danginsu.
Amma turaren nan da ka yi wa Baba alkawari, shi kadai muke bukata. Shi ma zai yi amfani da shi ne domin yi maka addu’a, zai ba sauran malaman rauhanai sadakarsa.
Yanzu abin da za ka yi shi ne, idan mun gama magana, ka samu dabino guda goma sha biyu, ka yi sadaka da guda goma sha daya, ka ajiye guda daya a wurinka.
Da misalin karfe tara na dare, sai ka yi alwala, ka yi Sallah raka’a biyu. Da zarar ka sallame, sai ka yi salati goma sha daya ga Annabi Muhammad (SAW).
Sai ka sanya dabinon nan guda daya a baki, ka cinye. Kana gama cinyewa, sai ka kira ni, zan hada ka da Baba, domin karin bayani.”
Daga nan sai ta kashe waya. Ni kuwa na sha alwashin a yau zan kure wadannan aljanun bogi, aljanun karya, ’yan wankiya, ’yan 419 na gaban sahu.
A nan ne na ci gaba da nazarin wannan al’amari. Na farko dai na gane cewa lallai su ’yan damfara ne, domin kuwa ga shi na shirga masu karya amma ba su gane ba.
Da farko na ce ba zan yi amfani da kudina in kira wayarsu ba amma dai domin in kara kai su bango, sai na canza ra’ayi.
Na sayi katin MTN na Naira dari hudu na sanya wa wayata.
Kamar yadda ta ce, da dare sai na kira ta. Kiran farko, har ta gama kara ba ta dauki wayar ba.
A kira na biyu, sai ta dauka. Ta ba ni hakuri, ta ce mani wai tana ganawa da Baba ne, shi ya sa ba ta dauki wayar ba.
Ta ce ta yi masa dukkan bayani, don haka bari ta ba shi wayar. Da ta ba shi sai na ji muryarsa ya yi mani sallama.
“Assalamu alaikum dana Gizago!”
Ni kuwa na amsa, na saurara ya ci gaba da magana. “Diyata Ummulhairi ta yi mani bayanin nasarar da ka samu.
“Shi ne nake son gaya maka cewa, madamar kana tare da mu, ba za ka taba ganin ci baya ba, sai daukaka.
“Kuma ka ga yau din nan, akwai wata gamayyar addu’a da za mu yi da manyan malaman aljannu a Harami anjima.
“Don haka, zan sa sunanka a cikin daya daga cikin wadanda za su amfana da wannan addu’a. Kafin in yi nisa, ina son ka kara natsuwa, ka fahinci sharuddan da zan nanata maka.
“Na farko dai, ka sani, aminci ne ya hada mu da kai, kauna ce ta musamman ta hada mu da kai.
“Don haka, ka rike amana, kada ka sake ka gaya wa kowa labarin alakar da ke tsakaninmu.
“Duk kuma abin da muka ummurce ka, ka aikata ba tare da ka yi mana gardama ba.”
Za mu ci gaba