Yadda ta’addancin ke karuwa a Sakkwato bayan zabe
An sake guntule hannuwan wani matashi Bayan kammala zaben bana a Jihar Sakkwato, ana ci gaba da samun kai hare-hare da ake zargi suna da alaka da bangar siyasa. An jikkata mutane da dama a wasu kananan hukumomin jihar sai ma’aikatan da aka yi wa bulala ko aka kora daga ofisoshinsu. Zuwa yanzu dai mutum […]
Sani Muhammad, wanda shi ma aka guntle wa hannu
- An sake guntule hannuwan wani matashi
Bayan kammala zaben bana a Jihar Sakkwato, ana ci gaba da samun kai hare-hare da ake zargi suna da alaka da bangar siyasa. An jikkata mutane da dama a wasu kananan hukumomin jihar sai ma’aikatan da aka yi wa bulala ko aka kora daga ofisoshinsu.
Zuwa yanzu dai mutum uku su samu nakasar da ba za ta taba gyaruwa ba, inda biyu daga cikinsu suka rasa hannunsu na dama, yayin da na uku ya rasa hannuwansa biyu.
Mutum biyu masu suna Abdullahi Shehu da Sani Muhammad kowanensu ya rasa hannunsa na dama, yayin da Habibu Abubakar Nakasari ya rasa hannuwansa biyu gaba daya a farkon wannan mako.
Habibu Abubakar Nakasari Sarkin Samarin Nakasari, dalibi ne a fannin koyon harsuna (Linguistic) da ke shekarar karatu ta biyu a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato. Dalibin mai shekara 22 an guntule hannayensa biyu a ranar Lahadin da ta gabata, inda wadansu matasa hudu suka auka masa suka yi masa ta’asar da kara tayar da hankalin Sakkwatawa da al’ummar Najeriya.
A zantawarsa da Aminiya dalibin ya ce, “Unguwarmu Nakasarin Ardo a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu amma a Unguwar Mana nake kwana gidan abokina Abu Lamfad. A ranar Lahadin da ta wuce na ajiye motata inda take kwana na dauki babur dina na je shagon dinkin Abu don jiransa mu tafi tare, muna shagonsa na dinki har zuwa karfe 1:30 na dare aka kira shi da waya ya fita bayan ya dawo ne yake fada min babansa ne ya kira ya ce yana son ya samo masa shayin Buzaye (Ataye). Na ce masa ya tafi da babur dina ya ce a’a zai tafi da nasa. Ya ba ni mabudin gida ya wuce ni kuma na tafi gida, ba kowa mu ke kwana gidan. Da na isa gidan na bude kofa na dauko katako na aje kasa don in dora babur in sa shi a cikin gida, kawai na ji wani ya buga min katako a kai, ya kuma sare ni da adda a kai.”
Ya kara da cewa: “Sai dayan kuma ya shigo cikin gidan wanda shi ne ya guntule min hannun guda biyu da adda, jini ya rika fita saman kaina da hancina da hannayena. Haka na fito gidan da gudu na doshi makwabtanmu, fitowar da na yi na hadu da wadansu mutum biyu a waje, su ne suka umarci biyun da ke cikin gida cewa su tafi suna saman babur ne daban kuma suka wuce da nawa har suke tambaya ta ina mabudin motata. Hakan ya nuna sun san ni, amma ni ban sansu ba sai dai na ga fuskar daya kuma duk inda na sake ganinsa ina iya gane shi.”
Ya ce: “Makwabta lokacin kowa ya rufe gidansa, na nemi dauki a wani gida ban samu ba ina cikin wannan hali ne abokina ya dawo bayan ya gaya min ba zai dawo ba sai karfe hudu, amma sai gashi ya ga halin da nake ciki. Ya ce in bari ya rufe ni cikin gida ya kirawo ’yan uwana a kai ni asibiti, na ce ban aminta ba, haka muka samu karin wadansu mutum biyu tare da shi aka kai ni Asibitin Kwararru na Jiha daga nan ne aka dawo da ni nan Asibitin Kashi na garin Wamakko.”
Habibu ya ce yanzu ya rasa hannayen da zai yi wa kansa komai don haka yana kira ga gwamnati ta taimaka masa a sanya masa hannayen roba don nasa ba za su dawo ba har abada har an turbude su.
“Ina hulda da babban dan Gwamna, wato Najib Tambuwal, ni dan Jam’iyar PDP ne, ban san na yi fada da kowa ba don ba na rigima, Wannan abin da aka yi min ina zargin abokina da nake kwana tare da shi tsawon lokaci, saboda wata rana an taba zuwa gidan aka yi ta bugun gida ana son in bude na zaci shi ne da na tambaya na gane ba shi ba ne, kuma na kira shi ya ki dauka. Wannan aikin hassada ce daga wanda da ake tare da su,” inji Habibu.
Ya ce ’yan sanda sun sanar da shi sun kama abokin nasa da wadansu mutum biyu suna bincike. Ya ce sun sanar da shi ne lokacin da suka ziyarce shi don daukar bayanin abin da ya faru daga farko har karshe.
DOkta Nuradden Altine Aliyu Shugaban Asibitin Kashi na Wamakko ya ce “Matashin mai shekara 22 an kawo mana shi an guntule hannunsa biyu dole muka yi kokarin dawo da shi hayyacinsa don yana zubar jini an cire hannunsa ba bisa ka’ida ba, muka tsayar da zubar jinin, don hannayen ba su komawa, jininsu ya daskare kwayoyin cuta sun shiga ciki awa shida zuwa bakwai da faruwar lamarin aka kawo shi wajenmu, ba abin da za mu yi sai gyaran mikin kawai.”
Ya ce gwamnatin jihar ta shiga lamarin sosai an yi masa tiyata ranar Litinin, kuma zai ci gaba da shan magani, kuma nan gaba kadan za a yi masa hannayen roba in ta kama a fita da shi za a yi. Ya ce tunda gwamnatin Sakkwato ta shiga lamarin zai samu taimako, hannayen roba suna da matukar tsada, amma ba za su gagari gwamnati ba.
Mahaifin dalibin Malam Abu Atto ya shaida wa Aminiya cewa wannan kaddara ce daga Allah suna fatan Allah ya saka wa dansa a kan wadanda suka yi masa haka. Ya ce yana ganin an yi masa haka ne don ana yi masa hassada.
Shugaban Jami’ar Usman Dan Fodiyo Farfesa Abdullahi Audu Zuru ya jajanta wa dalibin kuma ya ce jami’ar za ta duba yadda za ta yi game da karatunsa.
A Karamar Hukumar Sabon Birni a ranar Litinin da ta gabata matasan Jam’iyyar APC da PDP sun yi arangama dauke da makamai a tashar mota ta Sabon Birnin bayan da magoya bayan PDP suka ce sun sauke Sarkin Tasha daga mukaminsa bisa zarginsa da ya goya wa Jam’iyar APC baya a zaben Gwamna da ya gabata. Rigimar ta jawo jikkatar mutane da dama har aka sare hannun dama na wani matashi mai shekara 35 mai suna Sani Muhammad.
Matashin da ke jinya a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo ya shaida wa wakilinmu cewa: “Ni dan Jam’iyyar APC ne wani dan PDP, Shugaban Layin Tasha ne ya guntule min hannu da takobi, shi ne aka kawo ni asibiti.”
Kwamared Abubakar Sambo Bazza mai sharhi kan lamurran yau da kullum ya shawarci iyaye da gwamnati da shugabannin siyasa su dauki mataki kan wannan kazamin lamari da ya kunno kai bayan kammala zaben Gwamna a jihar. “Iyaye su dauki nauyin da Allah Ya dora musu na tarbiyyar yara, jami’an tsaro su tashi tsaye wurin kawar da batagari a jiha, shugabanni su fito da hanyoyin magance radadin talauci a cikin al’umma, shugabannin siyasa su rage kaifin bangar siyasa a tsakanin matasa, a tarwatsa duk wasu cibiyoyin miyagun kwayoyi, mutanen unguwa su rika sanya ido kan wadanda ke unguwa, da sauran abubuwan da suka kamata ‘yan boko su yi. Wannan ba karamar barazana ce ga al’umma ba an yi wannan ta’asar har sau uku bai kamata a tsaya ana kallo ba, rashin imanin ya yi yawa ka dauko makami ka raba mutum dan uwanka da wani sashe na jikinsa kan siyasa ko wata bukatar duniya,” inji Bazza.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Abubakar Sadik Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa, suna sane da lamarin, kuma sun kama wanda ake zargi suna bincike, bayan sun kammala za su sanar da jama’a.