Yadda tabarbarewar tsaro ta lalata al’amura a Jihar Borno

Duk mutumin da ya san Jihar Borno a shekara 10 da suka gabata, zai san cewa yanzu ta canja ta fuskar kasuwanci da zamantakewa da kuma harkar ilimin addini da na zamani. Jihar ta yi iyaka da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, inda ake samun fatake da ke fataucin kayayyaki a tsakanin kasashen.Baya ga […]

Yadda tabarbarewar tsaro ta lalata al’amura a Jihar Borno

 Alhaji Kashim Shettima Gwamnan Jihar BornoDuk mutumin da ya san Jihar Borno a shekara 10 da suka gabata, zai san cewa yanzu ta canja ta fuskar kasuwanci da zamantakewa da kuma harkar ilimin addini da na zamani. Jihar ta yi iyaka da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi, inda ake samun fatake da ke fataucin kayayyaki a tsakanin kasashen.
Baya ga haka an san jihar da karbar baki, baya ga dimbin kabilun da jihar ke da su sama da 20 da suke zaune lafiya shekaru aru-aru tare da bakin. Wannan ya sa ake wa jihar kirari da “GIDAN ZAMAN LAFIYA.”
Al’ummar jihar suna gudanar da harkokinsu babu tsangwama; kuma wani abin sha’awa shi ne yadda kabilun jihar musamman wadanda suka fito daga Kudancin jihar suke bin addinai daban-daban alhali sun fito daga gida ko daki daya.
To amma a yanzu abin ya sauya, domin babu batun harkar kasuwanci a fadin jihar, saboda baya ga rufe kan iyakokin jihar da kasashen makwabta; hatta kanana da manyan kasuwanni duk sun durkushe sakamakon rufe wasu da kone mafi yawansu a wasu kananan hukumomi,  cikin har da babbar kasuwar Maiduguri (Monday Market).
Lalata makarantun firamare kuwa hususan a Maiduguri fadar jihar abin ba a cewa komai, inda yanzu haka wasu malamai da dalibai ke zaune a gida saboda rashin ajujuwa.
Idan kuma aka yi maganar sana’o’in hannu ne domin neman na ci-maka, akasarin matasan jihar a yanzu ba su da sana’ar da za su dogara da kansu sun koma zaman kashe wando. Bugu da kari kananan masana’antu da aikin gona sun tsaya cik, haka maganar take a bangaren kiwon lafiya da sauran bangarorin da ya kamata a ce an ci gaba, duk saboda tabarbarewar tsaro.To amma duk da matsalar tabarbarewar tsaron da ta addabi  jama’a, al’ummar jihar ba su yanke kauna da samun zaman lafiya ba.
 A nata bangare gwamnatin jihar a karkashin Alhaji Kashim Shettima ta tashi tsaye don inganta rayuwar al’umma duk da matsanancin halin da jihar ta tsinci kanta a ciki.
A daya daga cikin jawabansa, bayan nuna alhini da bakin cikin abin da ke faruwa a jihar Gwamna Shettima ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen inganta rayuwar al’ummar jihar; inda yake cewa “Ina bakin cikin abin da ke faruwa a wannan jiha tamu, to kuma har yanzu ina kira ga ’ya’yan wannan kungiya su yi wa Allah su ajiye makamansu don a samo hanyoyin tserar da rayukan al’umma,  kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da ayyuka don inganta rayuwar al’ummar jihar nan.”
Masu lura da al’amura na ganin cewa jihar ta samu ci gaba matuka a lokacin mulkin Gwamna Shettima duk da kalubalen tsaron, inda gwamnatinsa ke taka rawa a fannin gina hanyoyi da inganta kiwon lafiya da samar da ruwan sha a kananan hukumomin jihar 27.
Malam Babagana wani majiyaci a asibitin Guzamala ya ce “A yanzu malaman asibiti na kulawa da mu baya ga magungunan da ake ba mu a kan lokaci, ba kamar da ba.”
Su kuwa Bukar Muhammad da Falmata Ali da Mustapha Baba Goni dukkansu dalibai a makarantu daban-daban daga kananan hukumomin Guzamala da Jere da Maiduguri sun ce: “A yanzu muna samun karatu da yake akwai kayan aiki, kuma ana ba mu abinci mai inganci, kuma an gyara mana ajujuwa da dakunan kwana.”

…Hare-haren Boko Haram: Akwai lauje a cikin nadi
– Rundunar Adalci

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa a kan al’ummomin jihohin Yobe da Borno da Adamawa da ake zargin’yan kungiyar Boko Haram da aiwatarwa ga alamu akwai lauje a cikin nadi.
Shugaban Rundunar Adalci ta kasa reshen Jihar Yobe Malam Zakari Adamu ya bayyana haka lokacin da yake tattauna da Aminiya a Potiskum Jihar Yobe musamman ganin lamarin ya ki ci ya ki cinyewa duk da dokar ta-bacin da aka sa wa jihohin.
Ya ce, wadannan hare-hare da ake kaiwa a kai-a kai da ake zargin ’yan Boko Haram da kaiwa kodai Gwamnatin Tarayya ce ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’ummomin ko kuma kai tsaye tana da hanu dumu-dumu a hare-haren kare-dangi da ake yi da nufin kawar da al’ummomin yankin daga taswirar kasar nan ko ta duniya dungurungum.
 Malam Zakari Adamu ya ce yadda aka dauki lokaci mai tsawo wai ana yaki da ’yan Boko Haram amma duk da makudan kudin da Gwamnatin Tarayyar ta ware da dimbin jami’an tsaron da aka kai yankunan amma wai a ce har yanzu an kasa shawo kan lamarin kashe- kahe da kone-konen da ake yi.
“Kamar yadda na san karfin jami’an tsaron Najeriya koda da wata kasa ake irin wannan abu da tuni an murkushe su, ballantana tsirarun ’yan kasa da aka san inda suke ai ka ga dole ne mu ce akwai lauje cikin nadi,” inji shi.
Shugaban ya ce babu abin da ya sa ya karkata ga tunanin akwai hannun Gwamnatin Tarayya cikin wannan lamari na kashe –kashen rayuka da gurgunta tattalin arzikin jama’ar yankunan shi ne yadda wani sojan Najeriya ya fito a wata kafar labarai ya ce akwai hannun sojojin Najeriya a kashe-kashen da ake yi.
 Ya yi kira ga gwamnnati ta san cewa a yanzu al’ummomin yankunan da ake tarzoma da na jihohin Arewa sun san su masu yakarsu don wata manufa ta siyasa da cin amana, kuma ta gaggauta kawo karshe wannan mummunan abu kafin al’umma su botsare.
Kuma ya shawarci Gwamnatin Tarayyar kan kada ta kara sa dokar ta-baci a jihohin uku tunda babu wani amfani da sa dokar ta samar in ban da kara ruruta wutar kai hare-haren.