Yadda tagwayen Zamfara suka kubuta daga masu garkuwa
A yayin da aka baro Sumayya mai ciki a daji Bayan shafe kwanaki 27 a hannun masu garkuwa da mutane, ’yan tagwayen Zamfara, Hassana da Hussaina Bala sun dawo gida cikin danginsu a ranar Asabar da ta gabata, bayan da danginsu suka mika kudin fansa Naira miliyan 15 ga masu garkuwar. A tattaunawa da Aminiya, […]
Yadda tagwayen Zamfara suka kubuta daga masu garkuwa
A yayin da aka baro Sumayya mai ciki a daji
Bayan shafe kwanaki 27 a hannun masu garkuwa da mutane, ’yan tagwayen Zamfara, Hassana da Hussaina Bala sun dawo gida cikin danginsu a ranar Asabar da ta gabata, bayan da danginsu suka mika kudin fansa Naira miliyan 15 ga masu garkuwar.
A tattaunawa da Aminiya, babban yayan tagwayen, Malam Abdurrashid Bala ya bayyana yadda kannen nasa suka kukuta.
“Mun kai kudi Naira miliyan 15 a wani daji cikin Jihar Zamfara kusa da Jihar Katsina. Mutanen sun zo sun karbi kudin, sun sakar mana yaranmu. Mun kai su asibiti domin tantance lafiyarsu. Ya zuwa yanzu dai babu wata matsala a tare da su. Haka kuma masu garkuwa ba su keta haddinsu ba, ba su ci zarafinsu ba, domin ba mu ga wani rauni a jikinsu ba. Wannan shi ne abin da kawai zan fada maka ke nan,” a cewar Abdurrashid.
Ya kara da cewa lokacin da suke can hannun masu garkuwar suna ba su abinci kowane iri sai dai sun fi ba su shinkafa da wake. Ana zuba masu a roba, maza kuma ana zuba masu saman leda-bage, a haka suke ci. Ya ce kuma idan za a kai su wanka, ana kai su wurin gulbi ne kamar shanu, su yi wanka a dawo da su.
“Ba su bugunsu, sai in wani dan uwansu ya kira waya ne, to a lokacin za a rika hantararsu, da ba su kashi domin wanda ya kira ya ji suna matse don kawo daukin gaggawa,” inji shi.
Wani na kusa da dangin ’yan tagwayen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce mutanen masu garkuwa da mutane sun fi 200 a cikin dajin. Ya ce suna da babban ubangida da ba ya zuwa dajin, waya kawai ake yi da shi.
“Mutanen suna gabas da Birnin Magaji, a wuraren kauyen Magari da Tsanu. Akwai Hausawa da Fulani da Kanuri a cikinsu. A karkashin itace suke zaune kuma mashinansu suna rufe su da ganye. Haki ne a wurin da suke zaune,” inji majiyar.
Ya nuna takaicinsa game da jami’an tsaro, cewa “akwai mamaki, jami’an tsaro su kasa daukar kowane mataki ganin an san za a kai kudi don karbo wasu. Naira miliyan 15 aka bayar. Mutum biyu suka kai kudin, Ibrahim da Munzil, domin maharani da suka zo sun fi su 20 domin karbar kudin da aka ba su kudin cikin jakar Ghana biyu. Suka duba kudin ya cika, jagoran tawagar tasu ya yi wani kulumboto, suka dauki kudin suka ba su yaran, aka sa su mota aka kawo su babban titi,” a cewarsa.
Daya daga cikin angunan da ke shirin auren tagwayen mai suna Munzil, ya yi wa Aminiya karin haske kan lamarin. “Ni kam me zan ce? Kawai dai mun gode Allah da kuma wadanda suka taimaka mana har yaran suka kubuta, mun gode. Amma dai a yanzu ba za ka samu damar magana da su ba, in dai na samu dama ina tare da su, zan yi maka Magana,” a cewarsa.
Alhaji Abubakar Yusuf Dauran, shi ne mahaifin daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Sumayya, wacce har yanzu take hannun masu garkuwar. Ya bayyana wa Aminiya cewa: “Na samu labarin dawowar ’yan tagwaye, na gode Allah, an mayar da su gida sun wuce Abuja saboda wani dalili. A matsayina na baban Sumayya, wacce gidanta aka je aka sace ’yan tagwaye tare da ita, lokaci daya, rana daya; to shi ne nake da damuwa da tunanin rashin adalci da nake tunanin an yi mini. A ce an tafi an dauko ’yan tagwaye a baro Sumayya ita kadai ta kara shiga damuwa ga ta karama ce ’yar shekara 20, dauke da juna biyu.
“Duk neman agajin da muka yi kan sakin yaranmu gaba daya muke yinsa, ni da Alhaji Sani Salisu da Nura Mas’ud da babban yayan tagwayen Abdurrashid. Har yarjejeniya muka yi cewa tare za a hada kudi a karbo yaran, kowa ya tsaya kan abin da muka yarda da shi. Ni Naira miliyan uku na diyata, kar in wuce haka, su kuma kar su wuce Naira miliyan biyar na yaransu,” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa, “mun yi kokarin haduwa da yaran Sanata Kabiru Marafa kan maganar yaran, sun fada mana cewa Sanata ya yi alkawarin daga Naira miliyan daya har 10 zai bayar, mu dai je mu kare magana da mutanen. Kwatsam mun tafi gidan Sarkin Gusau don sanar da shi neman taimakon yaran, ya kira P.A na Marafa yake gaya masa cewa Ibrahim mijin yayarsu ya kawo masu wata muryar daya daga cikin yaran tana kuka, an ce za a kashe guda cikinsu in ba a kawo kudin ba. Da na ji wannan sai na fada wa mai gida, ya ce a tambayi yaron nawa ake bukata, ya ce Naira miliyan 10 ne, suna da Naira miliyan hudu a kasa. Ya ba da umarnin a bai wa Ibrahim kudin ta asusun ajiyarsa.
“Mai martaba ya ce kun jiya? Muka yi godiya, muka wuce muna korafin cewa wannan Ibrahim din ya yi mana shisshigi. Ba mu taba zama da shi ba amma ya yi mana haka. Bayan nan muka tafi wurinsa a Kaura tare da yayan mahaifin tagwaye da kawunsu kan maganar kudin, don karbo yaran gaba daya. A karshe ya ce su manufarsu da kudin, in an karbo tagwaye, sauran kudin su yi masu kayan daki. Nan dai aka aminta da barin kudin, a samu wasu a karbo kowa. Bayan mun koma aka fada mana cewa sun canja, ’yan biyu kawai za su karbo, kowa ya karbo nasa; har Sumayya ba ruwansu da ita. Muka ga ana yawo da lambar asusun ajiyar banki guda uku, ana neman taimakon karbo yaran. Wasu su ce miliyan 30, wasu 10, sai muka fahimci cewa akwai rashin gaskiya ciki.”
Baban Sumayya ya ci gaba da korafin cewa, “ga shi kuma mu ba mu san irin gudunmowar da aka samu ba. Da farko an tafi kan Naira miliyan 15, daga baya aka cin ma cewa a biya Naira miliyan 6, kuma abin da aka kai aka karbo yaran ke nan. Ibrahim Abubakar da Abdurrashid Bala da Munzil, su suka sanya lamarin ya canja har suka tafi da su Abuja wajen A’isha Buhari da wata mata da ta ce za ta dauki nauyin kayan dakin yaran. Sumayya ba ta da uwa, ita ma marainiya ce. Sun ce sun baro ta lafiya, ka san dai cikin karti, cikin bakin ciki da damuwa ne na fadi. Idan har diyata ta mutu zan tafi kotu da su.”
Da yake martani ga bayanin Baban Sumayya, Abdurrashid Bala ya ce bacin rai ne ya sanya yake wannan magana. “Bai kamata ya yi tunanin cewa sun raba Sumayya da ’yan uwanta ba, domin ko ba komai a gidansu ta tashi tun tana karama, har lokacin aurenta. Kuma mu ba mu tafi Abuja wajen matar Shugaban Kasa ba. Kawai mun tafi ne don yaran su samu nutsuwa, hankalinsu ya kwanta kafin su dawo cikin jama’a da su. Idan ya ce an samu kudi fiye da Naira miliyan 15 don karbo yaran, to ya bayyana hujjarsa. Za mu dawo bayan mun gama abin da ya kai mu Abuja.”