Yadda tallafin karatu ke habaka fasaha da hadin kai a Sterling Bank
Yadda rungumar masu basira daga Sterling Bank ke bunkasa rayuwar matasa.
Shin kerawa ko kirkirar manyan kayayyaki na da alaka ne da bambancin jinsi, shekaru, al’ada da tsarin rayuwa kamar ajiye gemu irin na Viking, ko ‘dreadlock’?
Amsar ba mai wuya ba ce, kodayake za a yi mamakin wanda zai ba ita, tunda matashi ne mai son wasan ‘Video Game’ da motsa jiki, kuma masoyin yanayi, mai basira a fasahar zamani – wanda za mu kira Dauda!
- Sterling Bank ya bullo da tsarin tallafin karatu da aiki
- Sterling Bank ya cancanci yabo saboda bullo da PaywithSpecta
Duk da cewa Dauda yana aiki da Bankin Sterling, yana son ajiye gemu irin na Viking, daidai da harkokinsa na kashin kai, sabanin irin shigar da aikin nasa ke bukata.
Gaskiyar lamari game da Dauda shi ne, ba zai iya zama koyaushe sanye sutura aiki ba kamar ko na aikin banki.
Abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne cimma manufar da ya sa a gaba, ba bin wasu kirkirarrun ka’idoji na al’ada ba.
Ya kasance ana yawan guje masa saboda yadda fahimtarsa game da aiki, addini, da al’ada suka bambanta da akasarin mutane.
Kodayake yawanci an san yadda mutum ke ji idan aka nuna masa wariya, amma wadda David ke fuskanta ta fi tsanani da yawan maimaituwa.
Galibi ba a sauraron bakin ra’ayoyin nasa, ballantana ya ga sakin fuska, ko a mutunta shi, a saurare shi, har sai da ya yi kicibus da bankin Sterling Bank.
Ya samu kwarin gwiwa ne daga wani mai kitson ‘dreadlock’, mai daukar bidiyo kuma ma’aikacin bankin da suka hadu a wurin taron cibiyar Decagon Institute.
Kayan aikin mai daukar bidiyon – ba ‘dreadlock’ dinsa ba – ne suka ja hankalin Dauda, saboda kaiwarsu makura. Daga karshe, irinsu aka ba shi ya bunkasa harkarsa.
Daga baya ya hadu da Shugabar Zartarwa mai kula da Dabaru da Kirkira a wurin taron. Wata matashiya!
Bugu da kari, aka gabatar da bangaren ga taron a matsayin masu Tattara Basira daga Sterling.
Tawagar na aiki ne tare da Decagon wurin daukar nauyin horar da masu basira a bangaren fasaha don samar musu da ayyuka da kuma daukaka ta fuskar tattalin arziki.
Hakan ya burge Dauda, ganin abin da ya dade yana neman samu ke nan. Sauran kuma ya zama tarihi, domin yanzu, shi ma’aikaci ne a Sterling, bankin da ya taro mutane iri-iri domin gudanar da ayyuka masu ma’ana.
Duk da cewa ya yi watanni da fara aiki a Sterling, har yanzu irin yadda ake damawa da kowa a bankin na matukar ba shi sha’awa.
Karon farko kuma ke nan da yake aiki a cikin kwararru a fannin fasa da yawancinsu mata ne.
Aikinsa tare da su na kara masa kwarin gwiwa matuka; daya daga cikinsu ta lashe kyautar Microsoft a matsayin Kwararriya Mafi Daraja, saboda ayyukanta a Sterling.
Abin da ya fi faranta masa rai a Sterling shi ne tsarin hada aiki da karatu na ‘Grow With Sterling’ domin daliban da suka kammala karatun sakandare.
Shirin na ba tallafin neman karo ilimi a matakin digiri na farko a fannonin Basirar Na’ura (AI), Nazarin Bayanai da kuma Sauye-sauyen Fasahar Zamani a Jami’ar Nexford da ka kasar Amurka.
Bankin Sterling ke biyan kashi 85% na kudin makarantarsu, wanda hakan ke sa kudin karatunsu na digirin farko a Jami’ar ba ya wuce Dala 500.
Wani dalilin farin cikin Dauda kuma shi ne, kafin fara aikinsa a Sterling Bank, yana wani amini, ma’aikacin wani kamfani.
Duk cewa yana kawo shawarwari masu muhimmanci da ke iya yin tasiri sosai wajen kawo sauyi ma’an, ba a sauraron sa, saboda ba shi da shaidar karatu na digiri ko difloma.
Haka kuma, saboda karancin shekarunsa da matakin iliminsa, abokan aikinsa ba sa sauraron sa ko daukar sa da daraja, wanda hakan asara ce dukkanninsu.
Amma da yake Dauda ya yi amannar cewa wajibinsa ya ga cewa hakan canza, sai ya yada wa abokan mu’amalarsa labarin irin kauna da kulawar da yake samu a Sterling Bank.
Ta hakan ya fahimtar da su cewa bankin Sterling Bank shi ne makyankyasar kirkire-kirkire da kuma yada sabbin abubuwa na zamani.