Yadda tankar mai ta kife ta kama da wuta

Wata tankar mai dauke da lita 40,000 na man dizal (AGO) a safiyar Alhamis ta fashe a kan babbar hanyar Oshodi-Apapa da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:15 na safe kamar yadda Babban Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a Jihar Legas, Ibrahim Farinloye ya bayyana. An gano cewa tankar […]

Yadda tankar mai ta kife ta kama da wuta

Wata tankar mai dauke da lita 40,000 na man dizal (AGO) a safiyar Alhamis ta fashe a kan babbar hanyar Oshodi-Apapa da ke Jihar Legas.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:15 na safe kamar yadda Babban Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a Jihar Legas, Ibrahim Farinloye ya bayyana.

An gano cewa tankar man ta tuntsure ne a daura da ofishin Hukumar Kashe Gobara inda kan motar ya rabu da jikinta.

Ibrahim Farinloye ya tabbatar da cewa jami’an kwana-kwana sun yi kokari wurin kashe wutar. Babu tabbacin asarar rayuka, inji shi.

‘Yan kallo a lokacin da matar ta fadi sannan ta kama da wuta
Yadda wuta ke ci a kan titi tare a bakin hayaki bayan motar ta kama da wuta
Daga nesa, bakin hayaki ya turke sama a inda wutar ta shi a ka hanya.
Wani jami’in kwana-kwana yana fesa ruwa domin kashe wutar
Jama’ar gari sun yi dafifi suna kallon yadda ake kokarin kashe gobarar
Jami’an kwana-kwana na ta kai-komo a lokacin aikin kashe gobarar