Yadda taron Afirka da China ya wakana a Beijing

A ranar Talata ce, aka rufe taron kasashen Afirka da kasar China da aka sanya wa suna FOCAC na bana a birnin Beijing. Shugaban China  di Jinping ya bayyana cewa taron zai taimaka wajen bude wani sabon babi na difolomasiyyar da ke tsakanin kasarsa da Afirka. Shi dai taron na wuni biyu (Litinin da Talata […]

Yadda taron Afirka da China ya wakana a Beijing
Yadda taron Afirka da China ya wakana a Beijing

A ranar Talata ce, aka rufe taron kasashen Afirka da kasar China da aka sanya wa suna FOCAC na bana a birnin Beijing.

Shugaban China  di Jinping ya bayyana cewa taron zai taimaka wajen bude wani sabon babi na difolomasiyyar da ke tsakanin kasarsa da Afirka.

Shi dai taron na wuni biyu (Litinin da Talata da suka gabata) an gudanar da shi ne a Cibiyar taro ta kasat China, kuma shugabannin kasashen Afirka ko wakilansu 53 da mai masaukinsu na China sun gana da juna tare da wakilan Majalisar dinkin Duniya da Tarayyar Afirka da sauransu.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban China, di Jinping ya yi alkawarin ba kasashen Afirka tallafin Dala biliyan 60 domin bunkasa yankin. Wanda hakan zai kara dankon zumunci a tsakanin kasarsa da yankin Afirka.

Manufar wannan shirin shi ne inganta huldar kasuwanci a tsakanin China da kasashen ketare, kuma tuni kasar ta bai wa wasu kasashe a yankin Asiya da Afirka rancen biliyoyin Dala don gina hanyoyin motoci da jiragen kasa da tashoshin jiragen ruwa da sauran manyan kayayyakin more rayuwa kamar yadda Rediyon Faransa ya ruwaito daga Shugaban China a lokacin taron.

Bayan kammala taron, Shugaba di Jinping da Shugaba Ramaphosa na Afirka ta Kudu da kuma sabon shugaban taron tattaunawar wato Shugaban Senegal Macky Sall sun gana da ’yan jarida tare. di Jinping ya bayyana cewa, taken taron na bana shi ne “Hada kai da samun moriyar juna, da yin kokari tare wajen neman raya makoma ta bai-daya a tsakanin  China da Afirka,” kamar yadda gidan rediyon China (CRI) ya ruwaito daga Shugaba di.

A nasu jawabin, Shugaba Ramaphosa da Shugaba Sall sun bayyana cewa, tun da aka fara taron FOCAC shekara 18 da suka gabata, taron ya zama muhimmin dandali na kara kaimi ga samun ci gaba a tsakanin China da Afirka, musamman ga kasashen Afirka. Kuma sun ce an samu sakamako mai kyau a yayin taron wanda ya nuna zumunci mai karfi da ke tsakanin Afirka da China, tare da tsara shirin raya dangantakar da ke tsakaninsu. “kasashen Afirka suna fatan hada kai da kasar China wajen zurfafa abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Afirka da China da raya shawarar ziri daya da hanya daya, da bullo da sababbin matakan hadin gwiwa a tsakanin Afirka da China da kuma neman raya makoma ta bai-daya a tsakanin kasashen.Muna godiya ga Shugaba di Jinping da gwamnatin China saboda jarin da ta zuba a manyan fannoni a Afirka, ciki har da gina ayyukan more rayuwa da raya masana’antu da inganta tattalin arziki a teku,da kimiyya da fasaha da kiwon lafiya, da ba da ilimi da horar da kwararru da sauransu,,” kamar yadda CRI ya kalato daga jawabin Ramaphosa. 

Yadda Najeriya za ta ci moriyar tallafin

Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, na daga cikin ayarin Shugaba Muhammadu Buhari kuma ya ce Najeriya na cikin manyan kasashen Afirka da za su bukaci kudi mai yawa daga cikin kudin da kasar ta China ta ware domin tallafa wa Afirka.

Da yake yi wa Sashen Hausa na Muryar Amurka karin haske kan yadda Najeriya za ta ci moriyar kudaden, Gwamna Badaru, ya ce aikin gina tashar wutar lantarki a tsaunin Mambila da ayyukan gina layin dogo da ake shirin yi a fadin kasar nan da kuma aikin sake farfado da titunan da suka lalace, duk suna daga cikin manyan ayyukan da Najeriya za ta nemi tallafin aiwatar da su.

Cikin kudaden da kasar China da ’yan kasuwarta suka ware don tallafa wa kasashen Afirka, akwai Dala miliyan dubu 15 da za su kasance tallafi na musamman da kuma basussukan da ba su da kudin ruwa, akwai kuma Dala miliyan dubu 20 da za a ba da bashi domin tsara manyan ayyuka a kasashen Afirka.

Da yake gabatar da nasa jawabin a wajen taron, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu tallafi da gudunmawa da basussuka daban-dabam da sula haura Dala miliyan dubu biyar, wanda gwamnatin ta yi amfani da su wajen yin manyan ayyuka a kasar, kamar layin dogo da gina manyan hanyoyi da kuma sha’anin noma.