Yadda taron bunkasa harsunan gida don tunawa da Farfesa Hambali Jinju ya wakana

A makon jiya ne masana, marubuta da al’umma masu kishin harsunan gida suka hallara a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka kwashe kwanaki hudu (18 zuwa 21 ga Fabrairu, 2014) suna gudanar da taron kara wa juna sani game da harsunan gida, musamman domin tunawa da marigayi Farfesa Hambali Jinji, kwararren malamin jami’a, wanda […]

Yadda taron bunkasa harsunan gida don tunawa da Farfesa Hambali Jinju ya wakana
Yadda taron bunkasa harsunan gida don tunawa da Farfesa Hambali Jinju ya wakana

A makon jiya ne masana, marubuta da al’umma masu kishin harsunan gida suka hallara a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda suka kwashe kwanaki hudu (18 zuwa 21 ga Fabrairu, 2014) suna gudanar da taron kara wa juna sani game da harsunan gida, musamman domin tunawa da marigayi Farfesa Hambali Jinji, kwararren malamin jami’a, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa harshen Hausa hidima.
Abin da ya wakana a ranar farko:
Tun da farko dai an bude taron ne kimanin karfe goma na safe, inda Gwamnan birnin Yamai ya gabatar da jawabin maraba. Daga bisani kuma Ministaan Ilimi na Nijar ya gabatar da nasa takaitaccen jawabin, inda ya nuna farin cikinsa da shirya wannan taro a kasarsu. Ya nuna shirin da kasarsa take yi na mutunta harsunan kasa na gado.
Haka shi ma Ministan Watsa Labarai na Nijar, ya gabatar da nasa jawabin, sannan ya mika abin magana ga Shugaban kungiyar Marubuta Harsunan Gida ta Najeriya (NILWA), wanda Nasiru Wada Khalil ya wakilta.
Shugaban ya bayyana dalilin da ya sanya kungiyar daga Najeriya ta hada kai da takwararta ta Nijar domin shirya gagarumin taron. Ya ce sun yi haka ne saboda tunawa da kwararren malamin Hausa, Farfesa Hambali Jinju, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma hidima. Ya ce mafi yawan lokacinsa da rayuwarsa, ya yi wa al’umma hidima ne a Najeriya, duk da cewa shi haifaffen kasar Nijar ne.
Shi ma takwaransa na Nijar, Shugaban kungiyar Marubuta Harsunan Gida (ASAUNIL), Malam Tarno Bala, irin wannan jaewabi ya gabatar. Ya nuna irin kokarin da marubuta harsunan gida suke yi a Jamhuriyar Nijar.
Shi kuwa Jakadan Najeriya a Nijar, Alhaji Abduljalil; a nasa jawabin, ya yi maraba ne da mahalarta taron, wadanda suka niko gari tun daga Najeriya zuwa Yamai, inda ya nuna goyon bayansa da na ofishinsa wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron cikin lumana.
Ministan Al’amuran kasashen Waje na Nijar, Baazum Muhammad, wanda a ma’aikatarsa aka gudanar da taron, ya samu halartar zauren taron, inda ya gana da mahalarta, ya gabatar da takaitaccen jawabin nuna goyon baya da taron.
Ranakun gabatar da takardun taro:
A ranaku biyu da aka ware don gabatar da takardu da nazarce-nazarcen masana, an samu nasarar haka, inda masana daga jami’o’i da kwalejojin ilimi na kasashen Najeriya da Nijar suka halarta kuma suka gabatar da takardun da suka haura guda hamnsin. Fitattun malaman Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Jami’ar Bayero Kano, Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato, Jami’ar Jihar Kaduna, Jami’ar Umaru Musa ’Yar-aduwa, Katsina duk daga Najeriya sun halarta kuma sun gabatar da takardu, wasu kuma sun fafata wajen yin tambayoyi da muhawarori da karin bayani. Haka ma daga Nijar, an samu masana daga Jami’ar Abdulmunini ta birnin Yamai da marubuta da masana harsunan gida, duk sun gabatar da takardu.
Wasu daga cikin masanan da suka gabatar da takardu sun hada da Farfesa Ibrahim Mukoshy da Farfesa Abdallah Uba Adamu da Muhammad dahiru Abdurrahman da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza da Bashir A. S. da Farfesa S. A. Yakasai da Farfesa Yusuf Adamu da sauransu da dama.
Haka kuma da dare, an gudanar da taruka a gidan Rediyon Altenatibe da ke birninYamai, inda marubuta daban-daban a Njieriya da Nijar suka karanta kirkirarrun labarai da wakoki da sauransu. Cikin wadanda suka gudanar da karatun, sun hada da Sulaiman Rejeto da Salmu Hassan da Halima Sarmai da Hajiya Umma, dukkansu marubuta daga Nijar. Haka kuma kwararren mawakin nan, Mamman Barka ya gudanar da wasa na musamman, inda ya gabatar da sabon kayan kidansa na gargajiya mai suna ‘Biram’ sannan ya amsa tambayoyin al’ummar da suka halarci taron. Daga Najeriya kuwa, marubutan da suka gabatar da ayyukansu na adabi sun hada da Ado Ahmad Gidan Dabino da Malam Kabir Sani, Shugaban kungiyar Marubuta ta Najeriya, Reshen Jihar Katsina, da Sarkin Fulani Dankama da Bashir Yahuza Malumfashi da Abu Hidaya da sauransu da dama.
An samar da sabuwar kungiyar manazarta Hausa:
A yayin gudanar da wannan muhimmin taro, masana, marubuta da manazarta Hausa da al’adun Hausawa sun nuna matukar bukatar kafa sabuwar kungiya, wacce za ta kunshi marubuta da manazarta harshen Hausa zalla. Wannan kuwa ya biyo bayan takardar da Farfesa Yusuf Adamu ya gabatar ne a wurin taron, wacce ta bijiro da bukatar yin haka. Nan take aka amince da haka, aka yi kwarya-kwayan taro, inda aka kafa kwamitin mutum bakwai, wadanda za su ci gaba da aikin tabbatar da kafa kungiyar. Wadannan mutane kuwa sun hada da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Taha Muhammad da Farfesa Yusuf Adamu da Farfesa Muntari Yusuf da Farfesa Salisu Yakasai da Farfesa Aliyu Bunza da Malam Lawal Aminu. An amince cewa za a yi taruka biyu, daya a Kano, daya kuma a Kaduna, tsakanin watannin Maris zuwa Mayu na bana.
Ranar Karrama marubuta, malamai da masu yi wa harsunan gida hidima:  
An karkare taron na birnin Yamai ne da bikin karrama muhimman masana da masu yi wa harsunan gida hidima, a ranar Juma’a (12-02-2014); ranar da Majalisar dinkin Duniya ta ware domin bikin harsunan gida. Bikin ya gudana ne a Jami’ar Abdulmumini. Wadanda aka karrama din sun hada da wadanda ke raye da kuma wasu da suka riga mu gidan gaskiya.
Wadanda suka rasu kuwa sun hada da marigayi Farfesa Muhammad Hambali Jinju, wanda aka sadaukar da taron kacokan domin tunawa da shi. Akwai kuma marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya.
Daga kasar Nijar, wadanda aka karrama sun hada da, Shugaban kasar Nijar Muhammadou Issofou da tsohon Shugaban kasar Nijar, Muhammadu Tandja da Ministan Sadarwa na Nijar da Ministan Ilimi na Nijar da Ministan Al’adun Gargajiya na Nijar da Babban Darakta na Hukumar Tarihi ta CELTO.
Sauran sun hada da Mista Thomas Battner da ’yar jarida Lidiya Ado da Maliki Alasan da kuma gidan rediyo mai zaman kansa, wato Radio Al’umma.
Daga Najeriya kuwa, wadanda aka karrama sun hada da Dokta Bukar Usman. An karrama shi ne a matsayinsa na marubucin da ya jajirce wajen farfado da tatsuniyoyi, hikaya da almara a kasar Hausa. Sai kuma mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Farouk Umar Farouk, a matsayinsa na mai kula da kare martabar Hausa da Hausawa. Akwai kuma tsohon Sufeto-Janar Alhaji Ibrahim Commassie, a matsayinsa na Garkuwan Hausa kuma mai yi wa Hausa hidima. Sai Sadiya Ado Bayaro, Giwar danmaje, wacce ta taimaka wajen tattarawa da wallafa ire-iren kirarin da ake samu a masarautun kasar Hausa.
Sauran daga Najeriya sun hada da Farfesa Abdallah Uba Adamu, saboda kokarinsa na samar da haruffan Hausa a kwamfuta. Akwai Farfesa Ibrahim Malumfashi, saboda kwarewarsa da hidimarsa a fannin tarihin Adabi da rubuce-rubucen Hausa. Sai kuma mawakin zamani na Hausa, Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA).
Taron ya sha yabo daga masana:
Masana da wasu daga cikin muhimman mutanen da suka halarci gagarumin taron sun yi tsokaci tare da yaba wa yadda taron ya gudana, kamar yadda kuma wasu suka yaba wa marigayi Farfesa Hambali Jinju, wanda aka shirya taron domin tunawa da shi.
Farfesa Ibrahim Mukoshy na Jami’ar usman danfodiyo Sakkwato, wanda ya yi aiki tare da marigayi Farfesa Jinju ya yaba masa kamar haka: “Farfesa Hambali Jinju mutum ne mai hakuri, mai kishin al’umma mai kishin Hausa. Mutum ne wanda bai da tsoro, mai fadin gaskiya a gaban kowane ne. Ya taba fada wa marigayi Sarkin Daura Muhammadu Bashar gaskiya game da tarihin Bayajida, ba tare da shayi ba, cewa abin da ake fada cewa Bayajida shi ne asalin Hausa, tatsuniya ce, wacce ake samun irinta a kowace al’umma. Yana da kokarin koya wa dalibansa iyaka iyawarsa domin ganin sun fahimta.”
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, wanda ya kasance daya daga cikin daliban marigayin, waka ya rubuta ta ta’aziyya mai baituka 19. Har kuka ya yi da hawaye a yayin da yake rera wakar gaban mahalarta taron. A baiti na uku, ga abin da Malam Bunza yake cewa:
“Rabuwa da Hambali Jinju manyan fama, Gogan da yas san hauni ya san dama, Masani iyayen tsangayar alfarma, Da baje karatu ba zaman tsince ba.”
Shi kuwa shahararren marubucin littattafan tatsuniyoyin Hausa kuma mai yi wa harshen hidima da dukiyarsa, Dokta Bukar Usman, yabawa ya yi da yadda aka shirya taron kuma da yadda ya gudana. Da wakilinmu ya tambaye shi ko me zai ce game da taron? Sai ya ce:
“Kamar yadda taro ya gudana, na yaba da yadda na ga masana masu kishi sun halarci taron da yadda suka gabatar da muhimman takardu. Mutane sun nuna kishi matuka, yadda muka taso tun daga Kano a mota zuwa Yamai, tafiyar awa goma sha bakwai, ba cin zango. Mun yi sa’a hanyar tana da kyau, sai dai nisa kawai. Taron ya kayatar kuma ya gamsar matuka. Furofesoshi sama da guda ashirin suka halarta daga Jami’o’in Bayero Kano, danfodiyo Sakkwato, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Jami’ar Umaru Musa ’Yar-adua Katsina da sauransu. Sun zo sun hadu da takwarorinsu na nan Nijar. Abin ya burge ni yadda aka gabatar da jawabai da kasidu cikin yarukan Hausa da Faransanci da Ingilishi. Taron ya taimaka wajen bukasa ilimi”
Shi kuwa shahararren mawakin gargajiya a Nijar, Mamman Barka ya yi bayani ne game da harshen Hausa da bunkasarsa. Ga abin da yake cewa:
“Ina fata in ga cewa harsunanmu na gargajiya an sanya su cikin makarantu, a rika amfani da su wajen koyarwa. Domin kuwa duk wani arzikinmu yana rataye ne bisa al’adunmu kuma dukan al’adunmu suna nan rataye bisa ginshikin harshenmu. Duk wanda ya batar da harshensa, to ya bace. Da harshe ne ake koyon tarbiyya, da shi ake tarbiyyantar da yara, da shi ake tattaunawa, ake gudanar da dukkan harkoki.
“Harshe wani abu ne da yake muhimmi a cikin al’adu. Ya kamata shugabanninmu na Afirika su maida hankali, a maido da harsunanmu, a ba su daraja, yaranmu matasa su taso da harsunanmu. Saboda yanzu in ka yi lissafi ka gani, mutum idan ya iya harshensa da kyau, Turancin ma da wuri yake koya. Ni kullum ina gaya wa yarana, cewa idan duk suna son su fahimci wani darasi da aka koya musu a makaranta, da farko idan sun karanta shi, su fassara shi da Hausa. Idan suka fassara shi da Hausa, za su fi fahimta, amma kar su ce da fari za su fahimce shi da Turancin, za su samu matsala. Harshe abu ne mai muhimmanci, wanda ya kamata ba ma Nijar da Najeriya kadai ba duk Afirika a ba su muhimmanci. Najeriya ta ba harsunan gida muhimmanci, domin akwai jaridu da yawa na harsunan gida da sauransu. Idan ba domin Najeriya ba, ni ina tsammanin in don Nijar ne, da yanzu Hausa ta jima da mutuwa.”
daya daga cikin ’ya’yan marigayi Farfesa Jinju, wato Abubakar Muhammadu Hambali, ya yi farin ciki ne da murna, ganin yadda aka karrama mahaifinsa. Yana cewa: “Ina matukar farin ciki yadda aka hada mutane suka halarci wannan taro domin tunawa da mahaifinmu. Wannan rana ta kasance ni kaina ina tunawa da shi baban namu. Shi ya fi damuwa da abin da ya shafi al’ummarsa da kuma al’adarsa da harshensa. Yana kula da Afirika da al’adun Afrika da ci gaban al’umma. Ya fi kula da wannan fiye da shi kansa. A yau na ga amfanin hidimar da ya dauki lokaci yana yi wa al’umma. Za mu ci gaba da yin duk abin da za mu yi domin ci gaba da raya ayyukansa.”
An kammala taron cikin lumana, inda mahalarta daga Najeriya suka sada zumunta da takwarorinsu na Nijar, kamar kuma yadda suka ziyarci Gidan Tarihi da ke Yamai. An tsaida cewa za a gudanar da taro na gaba irinsa a badi, a Najeriya idan Allah Ya kai mu.