Yadda taron Gizagawa karo na 5 ya gudana a Katsina
A ranar Asabar da ta gabata ce Gizagawa daga sassan Najeriya suka hallara a zauren taro da ke Filin Samji Katsina, inda suka gudanar da babban taronsu na kasa karo na biyar. A wannan karo, taron ya gudana ne a karkashin shugabancin Alhaji Ibrahim Aminu, Mai Ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara ta Fuskar Al’amuran Matasa, […]
A ranar Asabar da ta gabata ce Gizagawa daga sassan Najeriya suka hallara a zauren taro da ke Filin Samji Katsina, inda suka gudanar da babban taronsu na kasa karo na biyar.
A wannan karo, taron ya gudana ne a karkashin shugabancin Alhaji Ibrahim Aminu, Mai Ba Gwamnan Jihar Katsina Shawara ta Fuskar Al’amuran Matasa, wanda ya gabatar da jawabi tare da jawo hankalin matasa dangane da illolin da ke tattare da tu’ammali da kwaya da sauran kayan maye.
Babban Bako Mai Jawabi, ya kasance kwararre kuma masani kan harkokin tsaro, wanda kuma shugaba ne na Gidauniyar Tabbatar da Zaman Lafiya a Tsakanin Al’umma (Peace Builders Foundation), Abuja, Alhaji Ibrahim Ahmad Katsina. A taron ya gabatar da takarda mai taken “Annobar Shaye-Shayen Miyagun kwayoyi a Tsakanin Matasa: Ina Mafita?” Ya jawo hankalin matasa su natsu, su dauki darasi daga rayuwar manyansu da ke cikin al’umma. Ya ce a duk lokacin da ka ga wani hamshakin attajiri ko malami ko mai sarauta, to ya kintsa rayuwarsa ce tun lokacin da yake da kuruciya, domin da ya biye wa tu’ammali da kwaya, ba zai samu nasara ba. Ya doka misali da cewa, duk matashin da ke son samun daukaka da nasara a rayuwa, to ya guji shan kwaya.
Da yake ta’aliki ga wannan muhimmiyar takarda da bako mai jawabi ya gabatar, Shugaban Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Dokta Aliyu Idris Funtuwa, ya nanata muhimmancin da ke tattare da tarbiyya da bin hudubobin manya da kuma dabbaka al’adun gargajiyar Bahaushe a rayuwa.Ya yi gargadi musamman ga dalibai su guji shan kwaya da kayan maye.
A yayin taron, an karrama Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa danladi Abubakar tare da wadansu manyan mutane da suka dade suna tallafa wa al’umma ta hanyoyi daban-daban.