Yadda taron hukumomim kasuwancin teku na Afirka ya gudana a Abuja
A makon jiya ne Kungiyar Bunkasa Lamuran Kasuwanci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro kan bunkasa tashoshin teku don inganta kasuwanci a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a Abuja. Babbar Jami’ar Yankin na Majalisar Dinkin Duniya, Lousiania Rodrizue ta bayyana cewa akwai bukatar shirya manufofin da za su sanya wannan sashe […]
A makon jiya ne Kungiyar Bunkasa Lamuran Kasuwanci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro kan bunkasa tashoshin teku don inganta kasuwanci a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya a Abuja.
Babbar Jami’ar Yankin na Majalisar Dinkin Duniya, Lousiania Rodrizue ta bayyana cewa akwai bukatar shirya manufofin da za su sanya wannan sashe na bunkasa hada-hadar kasuwanci zuwa tasashoshin teku.
Ta kara da cewa, “Kuma ina ganin hadakar hukumar kasuwancin ta yankin Afirka na da gagarumar rawar da za ta taka wajen samun wannan nasara cikin kankanen lokaci.”
Rodrizue ta ce gudanar da wannan jagoranci shi zai kawo tururuwar ’yan kasuwa ga tashoshin tekun na Afirka da za su sanya sashen ya rika samar da makudan kudin shiga.
Taron ya zanta kan inganta tasoshin bakin tekun ta hanyar saukin gudanar da kasuwanci da hana tsoma bakin wadanda doka ba ta ba wa izini ba da kan wahalar da hada-hadar. Taron ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka da kwararru daga sauran sassan duniya kan lamuran kasuwancin teku.